Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Offerings

433 ayoyi · 61 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Da a ce ina jin yunwa ai, ba sai na faɗa muku ba, gama duniyar nawa ne, da kome da yake cikinta.

  2. Ina cin naman bijimai ne ko ina shan jinin awaki ne?

  3. “Ku miƙa hadayar godiya ga Allah, ku cika alkawuranku ga Mafi Ɗaukaka,

  4. Ba ka farin ciki a hadaya, ai da na kawo; ba ka jin daɗin hadayun ƙonawa.

  5. Hadayun Allah su ne karyayyen ruhu; karyayyiya da kuma zuciya mai tuba, Ya Allah, ba za ka ƙi ba.

  6. Zan miƙa kitsen dabbobi gare ka da kuma baye-baye na raguna; zan miƙa bijimai da awaki. Sela

  7. Yin abin da yake daidai da kuma nagari Ubangiji ya fi yarda da shi fiye da hadaya.

  8. Hadayar mugaye abin ƙyama ne, balle ma in aka kawo da mugun nufi!

  9. Ubangiji ya ce, “Yawan hadayunku, mene ne suke a gare ni?” Ina da isashen hadayun ƙonawa, na raguna da na kitsen dabbobi masu ƙiba; ba na jin daɗin jinin bijimai da na tumaki da kuma na awaki.

  10. Sa’ad da kuka zo don ku bayyana a gabana, wa ya nemi wannan daga gare ku, da kuke kai da kawowa a filayen gidana?

  11. Ku daina kawo hadayu marasa amfani! Turarenku abin ƙyama ne gare ni. Ina ƙin bukukkuwanku na Sabon Wata, da na ranakun Asabbaci, da taronku na addini, ba zan iya jure wa mugun taronku ba.

  12. Bukukkuwanku na Sabon Wata da na tsarkakan ranaku na ƙi su. Sun zama mini kaya; na gaji da ɗaukansu.

  13. Itatuwan Lebanon ba su isa a yi wutar bagade da su ba, balle dabbobinsa su isa yin hadayun ƙonawa.

  14. Bayan wahalar ransa, zai ga hasken rai, ya kuma gamsu; ta wurin saninsa bawana mai adalci zai ’yantar da mutane masu yawa, zai kuma ɗauki laifofinsu.

  15. Saboda haka zan ba shi rabo tare da manya, zai kuma raba ganima tare da masu ƙarfi, domin ya ba da ransa har mutuwa, aka kuma lissafta shi tare da masu laifofi. Gama ya ɗauki zunubin mutane masu yawa, ya kuma yi roƙo saboda laifofinsu.

  16. Amma duk ya miƙa hadayar bijimi yana kama da wanda ya kashe mutum, kuma duk wanda ya miƙa ɗan rago, kamar wanda ya karye wuyan kare; duk wanda ya miƙa hadaya ta gari yana kama da wanda ya yi sadakar jinin alade, kuma duk wanda ya ƙone turaren tuni, kamar wanda yake bauta gunki ne. Sun zaɓi hanyoyinsu, rayukansu kuma suna jin daɗin abubuwan banƙyamarsu;

  17. Za su kuma dawo da dukan ’yan’uwanku, daga dukan al’ummai, zuwa dutsena mai tsarki a Urushalima kamar hadaya ga Ubangiji, a kan dawakai, a kekunan yaƙi da wagonu, da kuma a kan alfadarai da kuma raƙuma,” in ji Ubangiji. “Za su kawo su, kamar yadda Isra’ilawa suke kawo hadayun hatsi, zuwa haikalin Ubangiji a cikin tsabtatattun kore.

  18. Babu riba a kawo mini turare daga Sheba ko rake mai zaƙi daga ƙasa mai nisa? Ba zan karɓi hadayunku na ƙonawa ba; ba na jin daɗin sadakokinku.”

  19. “ ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa ci gaba, ku ƙara hadayun ƙonawarku da sauran sadakoki ku kuma yi ta cin naman!

  20. Gama sa’ad da na fitar da kakanninku daga Masar na kuma yi musu magana, ban ba su dokoki kawai game da hadayun ƙonawa da sadakoki ba,

  21. amma na ba su wannan umarni cewa ku yi mini biyayya, zan kuwa zama Allahnku ku kuma ku zama mutanena. Ku yi tafiya cikin dukan hanyoyin da na umarce ku, don ku zauna lafiya.

  22. Ko da yake suna azumi, ba zan saurari kukansu ba, ko da yake suna miƙa hadayun ƙonawa da hadayun gari, ba zan yarda da su ba. A maimako zan hallaka su da takobi, yunwa da annoba.”

  23. sowa ta farin ciki da murna, muryoyin amarya da na ango, da muryoyin waɗanda suka kawo hadayun salama a gidan Ubangiji suna cewa, “ ‘ “Ku yi godiya ga Ubangiji Maɗaukaki, gama Ubangiji mai alheri ne; ƙaunarsa za tă dawwama har abada.” Gama zan mayar da wadatar ƙasar kamar yadda suke a dā,’ in ji Ubangiji.

  24. Sa’ad da na kawo su cikin ƙasar da na rantse zan ba su suka kuma ga tudu mai tsawo ko itace mai ganye, a can suka miƙa hadayunsu, suka yi sadakokin da suka tsokane ni na yi fushi, suka miƙa turaren ƙanshinsu suka kuma zuba sadakokinsu na sha.

  25. “Mayaƙansa za su taso su ƙazantar da kagarar haikali za su kuma kawar da hadaya ta kullum. Sa’an nan za su kafa abin banƙyama da yake lalatarwa.