Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Offerings

433 ayoyi · 61 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. ku kuma yi rayuwar ƙauna, kamar yadda Kiristi ya ƙaunace mu, har ya ba da kansa dominmu a matsayin sadaka mai ƙanshi da kuma hadaya ga Allah.

  2. An biya ni duka, biyan da ya wuce misali. Bukatata ta biya, da yake na karɓi kyautarku da kuka aiko ta hannun Afaforiditus. Baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai.

  3. Akan zaɓi kowane babban firist daga cikin mutane ne, akan kuma naɗa shi domin yă wakilce su a kan al’amuran Allah, domin yă miƙa kyautai da hadayu saboda zunubai.

  4. Wannan ma yana da ma’ana wa mutane a yau. Ya nuna cewa ba za mu iya wanke lamirinmu ta wurin miƙa baye-baye da hadayu ba.

  5. Sa’ad da Musa ya sanar wa dukan mutane kowane umarni na doka, sai ya ɗauki jinin maruƙa tare da ruwa, jan ulu da kuma rassan hizzob, ya yayyafa a kan naɗaɗɗen littafin da kuma a kan dukan mutanen.

  6. Ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Allah ya umarce ku ku kiyaye.”

  7. Ta haka ya yayyafa jinin a kan tabanakul da kuma a kan dukan kayayyakin da ake amfani da su don yin hidima.

  8. Tabbatacce, doka ta bukaci a tsabtacce kusa kowane abu da jini, kuma in ba tare da zub da jini ba babu gafara.

  9. Waɗannan abubuwa hotuna ne kawai na abin da yake a sama, dole kuma a tsarkake su ta wurin waɗannan ƙa’idodi. Amma dole a tsarkake ainihin abubuwa na sama da wani abu mafi kyau.

  10. Gama Kiristi bai shiga wani wuri tsattsarka da mutum ya yi ba, wanda yake hoto ne kawai na gaskataccen, a’a sama kanta ya shiga, domin yă bayyana a gaban zatin Allah a yanzu saboda mu.

  11. Bai kuwa shiga sama domin yă yi ta miƙa kansa a kai a kai, yadda babban firist yake shiga Wuri Mafi Tsarki kowace shekara da jinin da ba nasa ba.

  12. Da a ce haka ne, ai, da Kiristi ya sha wahala sau da yawa tun halittar duniya. Amma yanzu ya bayyana sau ɗaya tak a ƙarshen zamanai domin yă kawar da zunubi ta wurin miƙa kansa hadaya.

  13. Kamar dai yadda aka ƙaddara wa mutum yă mutu sau ɗaya, bayan haka kuma sai shari’a,

  14. haka aka miƙa Kiristi hadaya sau ɗaya domin yă ɗauke zunuban mutane masu yawa; zai kuma bayyana sau na biyu, ba don yă ɗauki zunubi ba, sai dai don yă kawo ceto ga waɗanda suke jiransa.

  15. Dokar, inuwa ce kawai ta kyawawan abubuwa masu zuwa, wannan inuwar ba ita ce ainihin abubuwan ba ne. Saboda haka ba za tă taɓa mai da masu matsowa kusa don yin sujada cikakku ta wurin irin hadayun da ake maimaitawa ba fasawa shekara-shekara ba.

  16. Da a ce za tă iya, da ba su daina miƙa hadayu ba? Ai, da an riga an tsabtacce masu yin sujada sau ɗaya tak, da kuma ba za su ƙara damuwa da zunubansu ba.

  17. Amma waɗancan hadayu abin tunawa da zunubai ne na kowace shekara,

  18. domin ba zai taɓa yiwuwa jinin bijimai da na awaki yă kawar da zunubai ba.

  19. Saboda haka, sa’ad da Kiristi ya shigo duniya ya ce, “Hadaya da sadaka kam ba ka so, sai dai ka tanadar mini jiki;

  20. hadayun ƙonawa da kuma hadayun zunubi ba ka ji daɗin.

  21. Sai na ce, ‘Ga ni nan, a rubuce yake cikin naɗaɗɗen littafi na zo in aikata nufinka, ya Allah.’ ”

  22. Da farko ya ce, “Hadayu da sadakoki, hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka so, ba ka kuwa jin daɗinsu” (ko da yake doka ta bukaci a yi su).

  23. Sa’an nan ya ce, “Ga ni nan, na zo in aikata nufinka.” Ya kawar da na farkon domin yă kafa na biyun.

  24. Kuma bisa ga wannan nufi, aka mai da mu masu tsarki ta wurin miƙa hadayar jikin Yesu Kiristi sau ɗaya tak.

  25. Kowace rana kowane firist yakan tsaya yin hidimar ibadarsa; sau da sau yakan miƙa hadayu iri ɗaya, waɗanda ba za su taɓa kawar da zunubai ba.