Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Obedience to God: Abram

7 ayoyi · 45 fannoni

Ayoyi game da Abram

  1. Ubangiji ya ce wa Abram, “Tashi ka bar ƙasarka, da mutanenka, da iyalin mahaifinka, ka tafi ƙasar da zan nuna maka.

  2. “Zan mai da kai al’umma mai girma, zan kuma albarkace ka; zan sa sunanka yă zama mai girma, ka kuma zama sanadin albarka.

  3. Zan albarkaci duk wanda ya albarkace ka, in kuma la’anci duk wanda ya la’anta ka, dukan mutanen duniya za su sami albarka ta wurinka.”

  4. Saboda haka Abram ya tashi yadda Ubangiji ya faɗa masa; Lot ma ya tafi tare da shi. Abram yana da shekaru 75, sa’ad da ya tashi daga Haran.

  5. Kashegari da sassafe, Ibrahim ya tashi ya ɗaura wa jakinsa sirdi. Ya ɗauki bayinsa biyu, da ɗansa Ishaku. Bayan ya faskare isashen itace saboda hadaya ta ƙonawa sai ya kama hanya zuwa wurin da Allah ya faɗa masa.

  6. Mala’ikan ya ce, “Kada ka yi wa yaron nan rauni. Kada kuma ka ji masa ciwo. Yanzu na san cewa kana tsoron Allah, gama ba ka hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba.”

  7. Ta wurin bangaskiya ne Ibrahim, sa’ad da aka kira shi ya fita zuwa wata ƙasar da zai karɓi gādo daga baya, ya kuwa yi biyayya ya tafi, ko da yake bai san inda za shi ba.