Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Obedience to God: Christ, an example of

7 ayoyi · 45 fannoni

Ayoyi game da Christ, an example of

  1. Yesu ya amsa ya ce, “Bari yă zama haka yanzu; ya dace mu yi haka don mu cika dukan adalci.” Sa’an nan Yohanna ya yarda.

  2. Ku tuna da kalmomin da na yi muku cewa, ‘Ba bawan da ya fi maigidansa,’In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun yi biyayya da koyarwata, da za su yi biyayya da taku ma.

  3. A cikin dangantakarku da juna, ya kamata halayenku su zama kamar na Kiristi Yesu.

  4. Wanda, ko da yake cikin ainihin surar Allah yake, bai mai da daidaitakansa nan da Allah wani abin riƙewa kam-kam ba,

  5. amma ya mai da kansa ba kome ba, yana ɗaukan ainihin surar bawa, aka yi shi cikin siffar mutum.

  6. Aka kuma same shi a kamannin mutum, ya ƙasƙantar da kansa ya kuma zama mai biyayya wadda ta kai shi har mutuwa, mutuwar ma ta gicciye!

  7. Ko da yake shi ɗa ne, ya yi biyayya ta wurin shan wahala