Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Nation

183 ayoyi · 11 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Duwatsu za su kawo wadata ga mutane, tuddai kuma su ba da amfani na adalci.

  2. A kwanakinsa adalai za su haɓaka wadata za tă yalwata har sai babu sauran wata.

  3. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Na ’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ka nuna wa ƙasarka alheri, ya Ubangiji; ka mai da nasarorin Yaƙub.

  4. Ka gafarta laifin mutanenka ka kuma shafe dukan zunubansu. Sela

  5. Ka kau da dukan fushinka ka kuma juye daga hasalar fushinka.

  6. Ka sāke mai da mu, ya Allah Mai Cetonmu, ka kau da rashin jin daɗinka daga gare mu.

  7. Za ka ci gaba da fushi da mu har abada ne? Za ka ja fushinka cikin dukan tsararraki?

  8. Ba za ka sāke raya mu ba, don mutanenka su yi farin ciki a cikinka?

  9. Ka nuna mana ƙaunarka marar ƙarewa, ya Ubangiji, ka kuma ba mu cetonka.

  10. Masu albarka ne waɗanda suka koyi yin maka kirari waɗanda suke tafiya cikin hasken da yake gabanka, Ubangiji.

  11. Suna farin ciki a cikin sunanka dukan yini; suna samun ɗaukaka cikin adalcinka.

  12. Gama kai ne ɗaukakarsu da ƙarfinsu, kuma ta wurin alherinka ka ɗaukaka ƙahonka.

  13. Tabbatacce, garkuwarmu ta Ubangiji ce, ta sarkinmu ce, da kuma ta Mai Tsarki na Isra’ila ce.

  14. bari kuma ka rayu ka ga ’ya’ya ’ya’yanka. Salama tă kasance tare da Isra’ila.

  15. Gama yana ƙarfafa ƙyamaren ƙofofinki yana kuma albarkace mutanenki a cikinki.

  16. Yana ba da salama ga iyakokinki yana kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau.

  17. Adalci yakan ɗaukaka al’umma, amma zunubi kan kawo kunya ga kowane mutane.

  18. Lokacin ƙauna da lokacin ƙiyayya, lokacin yaƙi da lokacin salama.

  19. Zai shari’anta tsakanin al’ummai zai kuma sulhunta faɗar mutane masu yawa. Za su mai da takubansu su zama garemani māsunsu su zama wuƙaƙen askin itatuwa. Al’umma ba za tă ƙara ɗauki takobi a kan al’umma ba, ba kuwa za su ƙara yin horarwar yaƙi.

  20. za ku yi wa sarkin Babilon wannan ba’a. Mai danniya ya zo ga ƙarshe! Dubi yadda fushinsa ya ƙare!

  21. Ubangiji ya karye sandar mugaye, sandan mulkin masu mulki,

  22. wanda cikin fushi ya kashe mutane da bugu marar ƙarewa, kuma cikin fushi ya mamaye al’ummai da fushi ba ƙaƙƙautawa.

  23. Dukan ƙasashe suna hutawa suna kuma cikin salama; sun ɓarke da waƙa.

  24. Wannan shi ne shirin da na yi domin dukan duniya; wannan shi ne hannun da aka miƙa a bisa dukan al’ummai ke nan.

  25. Gama Ubangiji Maɗaukaki ya ƙudura ya yi wannan, wa kuwa zai hana shi? Ya riga ya miƙa hannunsa, wa zai komar da shi?