Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Nation: Prayer for peace
Ayoyi game da Prayer for peace
Haka kuma, ku nemi zaman salama da cin gaba a birnin da aka kai ku zaman bauta. Ku yi addu’a ga Ubangiji saboda birnin, domin in ya ci gaba, ku ma za ku ci gaba.”
Da farko dai, ina gargaɗe ku cewa a yi roƙe-roƙe, ana addu’o’i, ana yin addu’a a madadin waɗansu da kuma a yi godiya saboda kowane mutum
da sarakuna da dukan masu mulki, domin mu zauna lafiya, rai kuma kwance, muna bin Allah sosai a cikin natsuwa.