Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Kings

580 ayoyi · 175 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Fadawan Amon suka ƙulla maƙarƙashiya suka kashe shi a cikin fadarsa.

  2. Sai mutanen ƙasar suka kashe duk waɗanda suka ƙulla wa Sarki Amon maƙarƙashiya, sa’an nan suka naɗa ɗansa sarki a maimakonsa.

  3. Game da sauran ayyukan mulkin Amon, da abubuwan da ya aikata, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.

  4. Aka binne shi a kabarinsa a lambun Uzza. Yosiya ɗansa kuma ya gāje shi.

  5. Yehoyahaz yana da shekara ashirin da uku sa’ad da ya zama sarki. Ya yi mulki na wata uku a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hamutal ’yar Irmiya; mutuniyar Libna.

  6. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, yadda kakanninsa suka yi.

  7. Fir’auna Neko ya sa shi a sarƙa a Ribla a ƙasar Hamat don kada yă yi mulki a Urushalima, sa’an nan ya sa wa Yahuda harajin talenti ɗari na azurfa, da talenti ɗaya na zinariya.

  8. Yehohiyacin yana da shekara goma sha takwas da ya zama sarki, ya kuma yi mulki wata uku a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Nehushta ’yar Elnatan, mutuniyar Urushalima.

  9. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda mahaifinsa ya yi.

  10. A wannan lokaci, hafsoshin Nebukadnezzar sarkin Babilon suka kawo wa Urushalima yaƙi, suka kuma kewaye ta.

  11. Nebukadnezzar na Babilon da kansa kuwa ya zo birnin yayinda hafsoshinsa suka kewaye ta.

  12. Yehohiyacin sarkin Yahuda, da mahaifiyarsa, da masu yi masa hidima, da hakimansa, da kuma fadawansa duk suka miƙa kansu ga Nebukadnezzar. A shekara ta takwas ta mulkin sarkin Babilon, sarkin Babilon ya mai da Yehohiyacin ɗan kurkuku.

  13. Yadda Ubangiji ya faɗa, Nebukadnezzar ya kwashe dukan dukiyar haikalin Ubangiji, da ta fadan sarki, ya kuma kwashe dukan kayan zinariyar da Solomon sarkin Isra’ila ya ƙera domin haikalin Ubangiji.

  14. Ya kwashi dukan mutanen Urushalima zuwa bauta, ya kwashi dukan fadawa, da mayaƙa, da masu sana’a, da maƙera, yawansu ya kai dubu goma. Ba wanda ya ragu, sai matalautan ƙasar.

  15. Nebukadnezzar ya ɗauki Yehohiyacin ya kai bauta a Babilon. Ya kuma kwashe mahaifiyar sarki, da matansa, da fadawansa, da manyan mutanen ƙasar daga Urushalima ya kai Babilon.

  16. Sarkin Babilon kuma ya kwashe dukan mayaƙa dubu bakwai, ƙarfafu, shiryayyu don yaƙi, da masu sana’a, da maƙera dubu ɗaya, ya kai Babilon.

  17. To, fa, Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra’ilawa; Isra’ilawa kuwa suka gudu a gabansu, da yawa kuma suka mutu a kan Dutsen Gilbowa.

  18. Filistiyawa suka matsa sosai suna bin Shawulu da ’ya’yansa maza, suka kuma kashe ’ya’yansa maza Yonatan, Abinadab da Malki-Shuwa.

  19. Yaƙin ya yi tsanani kewaye da Shawulu, kuma sa’ad da maharba suka rutsa shi, sai suka ji masa rauni.

  20. Sai Shawulu ya ce wa mai riƙe masa kayan yaƙi, “Zare takobinka ka soke ni, in ba haka ba waɗannan marasa kaciya za su zo su yi mini ba’a.” Amma mai ɗaukar masa kayan yaƙi ya ji tsoro bai kuwa yi haka ba; saboda haka Shawulu ya zāre takobinsa ya fāɗi a kansa.

  21. Da mai ɗaukar masa kayan yaƙi ya ga Shawulu ya mutu, sai shi ma ya fāɗi a kan takobinsa ya mutu.

  22. Ta haka Shawulu da ’ya’yansa maza uku suka mutu, dukan gidansa kuwa suka mutu tare.

  23. Sa’ad da dukan Isra’ilawa a cikin kwari suka ga cewa mayaƙansu suna gudu, kuma cewa Shawulu da ’ya’yansa maza sun mutu, sai suka bar garuruwansu suka gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka zauna a cikinsu.

  24. Kashegari, da Filistiyawa suka zo don su tuttuɓe waɗanda suka mutu, sai suka sami Shawulu da ’ya’yansa maza sun mutu a Dutsen Gilbowa.

  25. Suka tuttuɓe shi suka yanke kansa suka ɗauka duk da kayan yaƙinsa, suka kuma aika ’yan aika ko’ina a ƙasar Filistiyawa, a yi shela labarin a cikin gumakansu da kuma mutanensu.