Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Integrity

96 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. in na ɗaga hannuna don in cuci maraya, domin na san in na faɗa za a ji ni a wurin masu shari’a,

  2. bari hannuna yă guntule daga kafaɗata, bari yă tsinke daga inda aka haɗa shi.

  3. Gama ina jin tsoron hallaka daga Allah, kuma domin tsoron ɗaukakarsa ba zan iya yin waɗannan abubuwa ba.

  4. “In na dogara ga zinariya ko kuma na ce wa zallan zinariya, ‘Gare ki nake dogara,’

  5. in na yi fahariya don yawan dukiyata, arzikin da hannuwana suka samu.

  6. In na dubi rana cikin haskenta, ko kuma wata yana tafiyarsa,

  7. zuciyata ta jarrabtu gare su a ɓoye, hannuna kuma ya sumbace su.

  8. Waɗannan ma za su zama zunubin da za a shari’anta ke nan don zai zama na yi wa Allah na sama rashin aminci.

  9. “In na yi murna domin mugun abu ya faru da maƙiyina; ko kuma domin wahala ta same shi,

  10. ban bar bakina yă yi zunubi ta wurin la’anta shi ba,

  11. in mutanen gidana ba su taɓa cewa, ‘Wane ne bai ƙoshi da naman Ayuba ba?’

  12. Ba baƙon da ya taɓa kwana a titi, gama koyaushe ƙofata tana buɗe domin matafiya,

  13. in na ɓoye zunubina yadda mutane suke yi, ta wurin ɓoye laifina a cikin zuciyata,

  14. domin ina tsoron taron mutane kuma ina tsoron wulaƙancin da dangina za su yi mini, sai na yi shiru kuma ban fita waje ba.

  15. (“Kash, da ina da wanda zai ji ni! Na sa hannu ga abin da na faɗa don kāre kaina, bari Maɗaukaki yă amsa mini; bari mai tuhumata da laifi yă yi ƙarata a rubuce.

  16. Ba shakka sai in ɗora a kafaɗata, zan aza a kaina kamar rawani.

  17. Zan ba shi lissafin duk abin da na taɓa yi; zan zo gabansa kamar ɗan sarki.)

  18. “In ƙasata tana kuka da ni kunyoyinta duk sun cika da hawaye,

  19. in na kwashe amfaninta ban biya ba ko kuma na kashe masu ita,

  20. bari ƙaya ta fito a maimakon alkama ciyawa kuma a maimakon sha’ir.” Maganar Ayuba ta ƙare.

  21. Ya Ubangiji Allahna, in na yi kuskure aka kuwa sami laifi a hannuwana,

  22. in na yi mugunta ga wanda yake zaman lafiya da ni ko kuwa ba da wani dalilin cuci abokin gābana,

  23. to, bari abokin gābana yă bi yă kuma cim mini; bari yă tattake raina a ƙasa ya sa in kwana a ƙura. Sela

  24. Zabura ta Dawuda. Ubangiji, wa zai zauna cikin wuri mai tsarkinka? Wa zai zauna a kan tudunka mai tsarki?

  25. Sai wanda ba shi da laifi kuma yana yin abin da yake daidai, wanda yake faɗin gaskiya daga zuciyarsa