Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Integrity

96 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kada ku ɓata shari’a, ko ku nuna bambanci. Kada ku karɓi cin hanci, gama cin hanci yakan makanta idanu mai hikima, yă murɗe maganar mai gaskiya.

  2. Gaskiya ce kaɗai za ku bi don ku rayu, ku kuma mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.

  3. bakina ba zai faɗi mugun abu ba, harshena kuma ba zai yi ƙarya ba.

  4. Ba zan taɓa yarda cewa kuna da gaskiya ba; har in mutu, ba zan daina kāre mutuncina ba.

  5. Zan ci gaba da adalcina, ba zan fasa ba; lamirina ba zai taɓa yashe ni ba, dukan kwanakin raina.

  6. “Na yi alkawari da idanuna kada su dubi budurwa da muguwar sha’awa.

  7. Gama mene ne rabon mutum daga Allah a sama, gādonsa daga Maɗaukaki a sama?

  8. Ba masifa ba ne domin mugaye, hallaka kuma ga waɗanda suka yi ba daidai ba?

  9. Bai ga hanyoyina ba ne bai ƙirga kowace takawata ba?

  10. “In da na yi tafiya cikin rashin gaskiya ko kuma ƙafata ta yi sauri zuwa yin ƙarya,

  11. Bari Allah yă auna a kan ma’auni na gaskiya zai kuma san cewa ni marar laifi ne.

  12. In takawata ta kauce daga hanya, in zuciyata ta bi abin da idanuna ke so, ko kuma in hannuwana suna da laifi;

  13. bari waɗansu su ci abin da na shuka, kuma bari a tuge amfanin gonata.

  14. “In sha’awar mace ya shiga mini zuciya, ko kuma na laɓe a ƙofar maƙwabcina,

  15. sai matata ta niƙa hatsin wani kuma waɗansu maza su kwana da ita.

  16. Gama wannan zai zama abin kunya, zunubin da za a yi shari’a a kai.

  17. Wuta ce take ƙuna har ta hallakar; za tă cinye saiwar abin da na shuka ƙurmus.

  18. “In da na danne wa bayina maza da mata hakkinsu, sa’ad da suke da damuwa da ni,

  19. me zan yi lokacin da Allah ya tuhume ni? Me zan ce lokacin da ya tambaye ni?

  20. Shi wanda ya yi ni a cikin uwata ba shi ne ya yi su ba? Ba shi ne ya yi mu a cikin uwayenmu ba?

  21. “In na hana wa matalauta abin da suke so, ko kuma in sa idanun gwauruwa su yi nauyi don kuka,

  22. in na ajiye burodina don kaina kaɗai, ban kuwa ba wa marayu abinci sa’ad da suke jin yunwa,

  23. amma tun suna tasowa na lura da su, kamar yadda mahaifi zai lura da ɗa, kuma tun da aka haife ni ina lura da gwauruwa.

  24. In da na ga wani yana mutuwa don rashin sutura, ko wani mai bukata da ba shi da riga,

  25. kuma zuciyarsa ba tă gode mini ba don na yi masa sutura da gashin tumakina,