Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Integrity

96 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Tabbatacce ka sa su a ƙasa mai santsi; ka jefar da su ga hallaka.

  2. Duba yadda suka hallaka farat ɗaya, razana ta share su gaba ɗaya!

  3. Kamar yadda mafarki yake sa’ad da mutum ya farka, haka yake sa’ad da ka farka, ya Ubangiji, za ka rena su kamar almarai.

  4. Sa’ad da zuciyata ta ɓaci hankalina kuma ya tashi,

  5. na zama marar azanci da jahili; na zama kamar dabba a gabanka.

  6. Kada ka bar ƙauna da aminci su rabu da kai; ka ɗaura su kewaye da wuyanka, ka rubuta su a allon zuciyarka.

  7. Sa’an nan za ka sami tagomashi da kuma suna mai kyau a gaban Allah da kuma a gaban mutane.

  8. Bari idanunka su dubi gaba sosai, ka kafa idanunka kai tsaye a gabanka.

  9. Ka san inda ƙafafunka suke takawa ka bi hanyoyin da suke daram kawai.

  10. Kada ka kauce dama ko hagu; ka kiyaye ƙafarka daga mugunta.

  11. Shi da yake tafiya cikin adalci yana kuma magana abin da yake daidai, wanda yake ƙin riba daga cuta yana kuma kiyaye hannunsa daga karɓan cin hanci, wanda yake hana kunnuwansa daga ƙulla kisa ya kuma rufe idanunsa a kan tunanin aikata mugunta,

  12. shi ne mutumin da zai zauna a bisa, wanda mafakarsa za tă zama kagarar dutse. Za a tanada abincinsa, kuma ruwa ba zai kāsa masa ba.

  13. Ba ya cin zalin wani, amma yakan mayar wa wanda ya ba shi jingina abin da ya jinginar masa. Ba ya yi fashi amma yakan ba wa mayunwata abinci ya kuma tanada wa marasa tufafi riga.

  14. Ba ya ba da bashi da ruwa ko ya karɓa ƙarin riba. Yakan janye hannunsa daga aikata mugunta yakan kuma yi shari’a cikin gaskiya tsakanin mutum da mutum.

  15. Yana bin ƙa’idodina yana kuma kiyaye dokokina da aminci. Wannan mutumin adali ne; tabbatacce zai rayu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  16. Ya ce musu, “Kada ku karɓa fiye da abin da aka ce a karɓa.”

  17. Sai waɗansu sojoji suka tambaye shi, “Mu fa? Me ya kamata mu yi?” Sai ya amsa ya ce, “Kada ku ƙwace kuɗin mutane, kada kuma ku yi shaidar ƙarya. Ku yi haƙuri da abin da ake biyanku.”

  18. Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya cikin kome; kada ku yi aikin ganin ido kamar masu neman yabon mutane, sai dai ku yi aiki tsakaninku da Allah, kamar masu tsoron Ubangiji.

  19. Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba.

  20. Da yake an danƙa wa mai kula da ikkilisiya riƙon amana saboda Allah, dole yă zama marar aibi ba mai girman kai ba, ba mai saurin fushi ba, ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba, ba kuma mai son ƙazamar riba ba.

  21. A maimakon haka dole yă zama mai karɓan baƙi, mai son abu nagari, mai kamunkai, mai adalci, mai tsarki da kuma natsattse.