Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Integrity

96 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. ba ya kuwa ɓata sunan wani da harshensa, wanda ba ya yi wa maƙwabcinsa mugunta ba ya kuwa baza jita-jita a kan ɗan’uwansa,

  2. wanda yake ƙin mugun mutum amma yakan girmama masu tsoron Ubangiji, yakan cika alkawarinsa ko da ma ya zafe shi,

  3. wanda yake ba da rance ba tare da ruwa ba kuma ba ya karɓan cin hanci don yă kā da marar laifi. Shi wanda yake yin waɗannan abubuwa ba zai taɓa jijjiguwa ba.

  4. Wa zai iya hawan tudun Ubangiji? Wa zai iya tsaya a wurinsa mai tsarki?

  5. Sai wanda yake da hannu mai tsabta da kuma tsabtar zuciya, wanda ba ya ba da ransa ga bautar gunki ko ya rantse bisa abin da yake ƙarya.

  6. Zai sami albarka daga Ubangiji da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa.

  7. Ta Dawuda. Ka nuna rashin laifina, ya Ubangiji, gama na yi rayuwa marar zargi; Na dogara ga Ubangiji ba tare da kaucewa ba.

  8. Ka jarraba ni, ya Ubangiji, ka kuma gwada ni, ka bincike zuciyata da tunanina;

  9. gama ƙaunarka kullum tana a gabana, kuma ina cin gaba da tafiya a cikin gaskiyarka.

  10. Amma game da ni, ƙafafuna suna gab da yin santsi; tafin ƙafana ya yi kusan zamewa.

  11. Gama na yi kishin masu girman kai sa’ad da na ga cin gaban da masu mugunta suke yi.

  12. Ba sa yin wata fama; jikunansu lafiya suke da kuma ƙarfi.

  13. Ba sa shan wata wahalar da sauran mutane ke sha; ba su da damuwa irin na ’yan adam.

  14. Saboda girman kai ya zama musu abin wuya; tā da hankali ya zama musu riga.

  15. Daga mugayen zukatansu laifi kan fito mugaye ƙulle-ƙullen da suke cikin zukatansu ba su da iyaka.

  16. Suna ba’a, suna faɗin mugayen abubuwa; cikin girman kan suna barazana yin danniya.

  17. Bakunansu na cewa sama na su ne, kuma harsunansu sun mallaki duniya.

  18. Saboda haka mutanensu sun juya gare su suna kuma shan ruwa a yalwace.

  19. Suna cewa, “Yaya Allah zai sani? Mafi Ɗaukaka yana da sani ne?”

  20. Ga yadda mugaye suke, kullum ba su da damuwa, arzikinsu yana ta ƙaruwa.

  21. Tabbatacce a banza na bar zuciyata da tsabta; a banza na wanke hannuwa don nuna rashin laifi.

  22. Dukan yini na sha annoba; an hukunta ni kowace safiya.

  23. Da na ce, “Zan faɗa haka,” da na bashe ’ya’yanka.

  24. Sa’ad da na yi ƙoƙari in gane wannan, sai ya zama danniya a gare ni

  25. sai da na shiga wuri mai tsarki na Allah; sa’an nan na gane abin da ƙarshensu zai zama.