Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Humility

90 ayoyi · 43 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. A wannan rana ba za ku sha kunya saboda laifofin da kuka yi mini, gama zan ɗauke wa wannan birni waɗanda suke farin ciki cikin girmankansu. Ba kuma za ka ƙara yin kallon reni a tuduna mai tsarki ba.

  2. Amma zan zauna a cikinki masu tawali’u da masu ƙasƙantar da kai, waɗanda suke dogara ga sunan Ubangiji.

  3. Sai ya kira ƙaramin yaro ya sa shi yă tsaya a tsakiyarsu.

  4. Sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in ba kun canja kuka zama kamar ƙananan yara ba, labudda, ba za ku shiga mulkin sama ba.

  5. Saboda haka, duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar wannan yaro, shi ne mafi girma a mulkin sama.

  6. Ba haka zai kasance da ku ba. Maimakon haka, duk mai son zama babba a cikinku, dole yă zama bawanku,

  7. kuma duk mai son zama shugaba, dole yă zama bawanku,

  8. kamar yadda Ɗan Mutum bai zo don a bauta masa ba, sai dai don yă yi bauta, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”

  9. “Sa’an nan masu adalci za su amsa masa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka da yunwa muka ciyar da kai, ko da ƙishirwa muka ba ka abin sha?

  10. Yaushe kuma muka gan ka baƙo muka karɓe ka, ko cikin bukatar tufafi muka yi maka sutura?

  11. Yaushe kuma muka gan ka cikin rashin lafiya ko a kurkuku muka ziyarce ka?’

  12. “Sarkin zai amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan’uwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.’

  13. Suka iso Kafarnahum. Da yana cikin gida, sai ya tambaye su ya ce, “Gardamar me kuke yi a hanya?”

  14. Amma suka yi shiru, don a hanya suna gardama ne, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma?

  15. Da Yesu ya zauna, sai ya kira Sha Biyun ya ce, “In wani yana so yă zama na fari, dole yă zama na ƙarshe duka, da kuma bawan kowa.”

  16. Ya ɗauki wani ƙaramin yaro ya sa yă tsaya a tsakiyarsu. Ya ɗauke shi a hannunsa, ya ce musu,

  17. “Duk wanda ya karɓi ɗaya daga cikin waɗannan ƙananan yara a cikin sunana, ni ya karɓa. Duk wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, amma wanda ya aiko ni ne ya karɓa.”

  18. Ba haka ya kamata yă zama da ku ba. A maimakon, duk wanda yake so yă zama babba a cikinku, dole yă zama bawanku.

  19. Duk wanda kuma yake so yă zama na farko, dole yă zama bawan kowa.

  20. Sai Yesu ya tafi tare da su. Da ya yi kusa da gidan, sai jarumin nan, ya aiki abokai su ce masa, “Ubangiji, kada ka dami kanka, gama ban isa ka shiga gidana ba.

  21. Shi ya sa ban ma ga na isa in zo wurinka ba. Amma ka yi magana kawai, bawana zai warke.

  22. Wata gardama ta tashi a tsakanin almajiran, a kan ko wane ne a cikinsu zai zama mafi girma

  23. Da yake Yesu ya san tunaninsu, sai ya ɗauki wani ƙaramin yaro, ya sa ya tsaya kusa da shi.

  24. Sai ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi wannan ƙaramin yaron a cikin sunana, ni ya karɓa, kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne. Gama mafi ƙanƙanta duka a cikinku, shi ne kuma mafi girma.”

  25. Amma in an gayyace ka, ɗauki wuri mafi ƙasƙanci, don in wanda ya gayyace ka ya zo, zai ce maka, ‘Ka hawo nan aboki a wuri mafi girma.’ Wannan zai ɗaukaka ka a gaban dukan ’yan’uwanka baƙi.