Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Humility

90 ayoyi · 43 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku.

  2. Bai kamata kowannenku yă kula da sha’anin kansa kawai ba, sai dai yă kula da sha’anin waɗansu ma.

  3. A cikin dangantakarku da juna, ya kamata halayenku su zama kamar na Kiristi Yesu.

  4. Wanda, ko da yake cikin ainihin surar Allah yake, bai mai da daidaitakansa nan da Allah wani abin riƙewa kam-kam ba,

  5. amma ya mai da kansa ba kome ba, yana ɗaukan ainihin surar bawa, aka yi shi cikin siffar mutum.

  6. Aka kuma same shi a kamannin mutum, ya ƙasƙantar da kansa ya kuma zama mai biyayya wadda ta kai shi har mutuwa, mutuwar ma ta gicciye!

  7. Saboda haka Allah ya ɗaukaka shi zuwa mafificin wuri ya kuma ba shi sunan da ya fi dukan sunaye,

  8. don a sunan Yesu kowace gwiwa za tă durƙusa, a sama da a ƙasa da kuma a ƙarƙashin ƙasa,

  9. kowane harshe kuma yă furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne, don ɗaukakar Allah Uba.

  10. Ba cewa na riga na sami dukan wannan ba ne, ko kuma an riga an mai da ni cikakke ba, sai dai ina nacewa don in kai ga samun abin da Kiristi Yesu ya riƙe ni saboda shi.

  11. ’Yan’uwa, ban ɗauki kaina a kan cewa na riga na sami abin ba. Sai dai abu guda nake yi. Ina mantawa da abin da yake baya, ina kuma nacewa zuwa ga samun abin da yake gaba,

  12. Bari ɗan’uwan da yake cikin halin ƙasƙanci yă yi taƙama a matsayinsa na ɗaukaka.

  13. Amma wanda yake mai arziki, ya kamata yă yi taƙama a matsayinsa na ƙasƙanci, gama ba zai daɗe ba kamar furen jeji.

  14. Samari, ku ma, ku yi biyayya ga waɗanda suka girme ku. Dukanku, ku yafa sauƙinkai ga juna, domin, “Allah yana gāba da mai girman kai, amma yakan yi alheri ga mai sauƙinkai.”

  15. Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yă ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama.