Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Humility

90 ayoyi · 43 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Shi wanda kuma ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.”

  2. “Amma mai karɓar harajin ya tsaya daga nesa. Bai ma iya ɗaga kansa sama ba, sai ya buga ƙirjinsa, yana cewa, ‘Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi ne.’

  3. “Ina gaya muku, wannan mutum ne, ba ɗayan ba, ya koma gida baratacce, babu laifi a gaban Allah. Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Wanda kuma ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.”

  4. Gardama ta tashi a tsakaninsu, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma.

  5. Yesu ya ce musu, “Sarakunan Al’ummai suna nuna iko a kan mutanensu, kuma waɗanda suke nuna iko a kansu, suna kiran kansu Masu Taimakon mutane.

  6. Amma ku, kada ku zama haka. A maimakon haka, sai dai wanda ya fi girma a cikinku, ya zama kamar wanda ya fi ƙanƙanta, wanda kuma ke mulki, ya zama kamar mai hidima.

  7. Wane ne ya fi girma? Wanda yake zaune a tebur ne, ko kuma shi da yake yin hidima? Ashe, ba wanda yake zaune a tebur ba ne? Amma ga ni, ni mai yin hidima ne a cikinku.

  8. Ango ne mai amarya. Abokin da yake masa hidima yakan jira ya kuma saurara masa, yakan kuma cika da farin ciki sa’ad da ya ji muryar ango. Wannan farin cikin kuwa nawa ne, ya kuma cika a yanzu.

  9. Dole ne yă yi ta ƙaruwa, ni kuma in yi ta raguwa.

  10. Da yake ni da nake Ubangijinku da kuma Malaminku, na wanke ƙafafunku, haka ku ma ya kamata ku wanke ƙafafun juna.

  11. Na ba ku misali domin ku yi yadda na yi muku.

  12. Gaskiya nake gaya muku, ba bawan da ya fi maigidansa, ko ɗan saƙon da ya fi wanda ya aike shi.

  13. Ya zaɓi abubuwa marasa martaba na wannan duniya da kuma abubuwan da aka rena da abubuwan da ba a ɗauka a bakin kome ba, domin a wofinta abubuwan da ake ganinsu da daraja,

  14. domin kada wani ya yi taƙama a gabansa.

  15. Da na zo wurinku ’yan’uwa, ban zo da iya magana ko wani mafificin hikima yayinda na yi muku shelar shaida game da Allah ba.

  16. Don na ƙudura a raina sa’ad da nake tare da ku cewa ba zan mai da hankali ga kome ba sai dai Yesu Kiristi wanda aka gicciye.

  17. Na zo wurinku cikin rashin ƙarfi da tsoro, da rawan jiki ƙwarai.

  18. Zan yi taƙama game da mutum irin wannan, sai dai ni ba zan yi taƙama da kaina ba, sai dai a kan rashin ƙarfina.

  19. Ko da zan so yin gadara ma, ba zan zama wawa ba, gama gaskiya zan faɗa. Amma na bar zancen haka, don kada wani ya ɗauke ni fiye da yadda yake ganina, ko yadda yake jin maganata.

  20. Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni.

  21. Sau uku na roƙi Ubangiji yă raba ni da wannan abu.

  22. Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni.

  23. Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi.

  24. Na yi wauta kam, amma ku ne kuke tilasta mini, ku ne kuwa ya kamata ku yaba mini, domin ba inda na kāsa waɗannan mafiffitan manzanni, ko da yake ni ba kome ba ne.

  25. Abubuwan da suke tabbatar da manzo, alamu, abubuwa da kuma ayyukan banmamaki, an aikata su a cikinku da matuƙar nacewa.