Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Holy Spirit

145 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Da wannan yana nufin Ruhu ke nan, wanda waɗanda suka gaskata da shi za su karɓa daga baya. Har yă zuwa wannan lokaci ba a ba da Ruhu ba tukuna, da yake ba a riga an ɗaukaka Yesu ba.

  2. Zan kuwa roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimakon da zai kasance tare da ku har abada,

  3. Ruhun gaskiya. Duniya ba ta iya karɓarsa, don ba ta ganinsa ba ta kuma san shi ba. Amma kun san shi, saboda yana zama tare da ku zai kuma kasance a cikinku.

  4. Amma gaskiya nake gaya muku. Don amfaninku ne zan tafi. Sai ko na tafi, in ba haka ba Mai Taimakon nan ba zai zo muku ba. Amma in na tafi, zan aiko shi gare ku.

  5. Sa’ad da ya zo kuwa, zai kā da duniya a kan zunubi da adalci da kuma hukunci,

  6. a kan zunubi, domin mutane ba su gaskata da ni ba;

  7. a kan adalci, domin zan tafi wurin Uba, inda ba za ku ƙara ganina ba;

  8. a kan hukunci kuma, domin an yanke hukunci a kan mai mulkin duniyan nan.

  9. “Ina da sauran abubuwa da yawa da zan faɗa muku, amma ba za ku iya ɗauka a yanzu ba.

  10. Amma sa’ad da shi, Ruhun gaskiya ya zo, zai bi da ku zuwa ga dukan gaskiya. Ba zai yi magana don kansa ba; zai faɗi abin da ya ji ne kaɗai, zai kuma faɗa muku abin da bai faru ba tukuna.

  11. Zai kawo ɗaukaka gare ni ta wurin ɗaukan abin da yake nawa, ya bayyana muku.

  12. Ba zato ba tsammani sai aka ji motsi kamar ta babbar iska tana hurowa daga sama ta kuma cika dukan gidan da suke zaune.

  13. Suka ga wani abin da ya yi kama da harsunan wuta, suka rarrabu suna kuma sassauka a kan kowannensu.

  14. Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka kuma fara magana da waɗansu harsuna yadda Ruhu ya sa suka iya.

  15. Sai Bitrus ya ce, “Ananiyas, ta yaya Shaiɗan ya cika zuciyarka haka da ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya ka kuma ajiye wa kanka sauran kuɗin da ka karɓa na filin?

  16. Ba naka ba ne kafin ka sayar da shi? Bayan da ka sayar da shi kuma, kuɗin ba naka ba ne? Me ya sa ka yi tunanin yin irin wannan abu? Ba mutum ne ka yi wa ƙarya ba, Allah ne ka yi masa.”

  17. Da suka iso, sai suka yi musu addu’a domin su karɓi Ruhu Mai Tsarki,

  18. domin Ruhu Mai Tsarki bai riga ya sauka wa waninsu ba tukuna, an dai yi musu baftisma ne kawai a cikin sunan Ubangiji Yesu.

  19. Sa’an nan Bitrus da Yohanna suka ɗibiya hannuwansu a kansu, suka kuwa karɓi Ruhu Mai Tsarki.

  20. Sa’ad da Siman ya ga cewa ana ba da Ruhu ta wurin ɗibiya hannuwan manzannin, sai ya miƙa musu kuɗi,

  21. ya ce, “Ni ma ku ba ni wannan iyawa don kowa na ɗibiya wa hannuwana yă karɓi Ruhu Mai Tsarki.”

  22. Bitrus ya amsa ya ce, “Bari kuɗinka ya hallaka tare da kai, domin ka yi tsammani za ka iya saya kyautar Allah da kuɗi!

  23. Ba ruwanka da wannan hidimar, domin zuciyarka ba daidai take a gaban Allah ba.

  24. Ka tuba daga wannan mugunta ka kuma yi addu’a ga Ubangiji. Wataƙila zai gafarta maka don irin tunanin da yake a zuciyarka.

  25. Yayinda Bitrus yana cikin tunani game da wahayin, sai Ruhu ya ce masa, “Siman, ga mutum uku suna nemanka.