Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Holy Spirit

145 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Manufar Allah ita ce cewa mu da muka fara sa bege a cikin Kiristi, mu yi zaman yabon ɗaukakar Allah.

  2. An kuma haɗa ku a cikin Kiristi lokacin da kuka ji saƙon nan na gaskiya, wanda yake labari mai daɗi na cetonku. Da kuka ba da gaskiya, sai aka yi muku alamar shaida a cikinsa da Ruhu Mai Tsarki.

  3. Ruhu Mai Tsarkin nan shi ne tabbacin da Allah ya yi na cewa zai ba mu kome da ya yi alkawari, har ya sa muka sani nan gaba Allah zai ceci waɗanda suke nasa. Wannan kuwa domin yabon ɗaukakarsa ne.

  4. Ku yi ƙoƙari sosai ku kiyaye zaman ɗayan nan da Ruhu ya ba ku, ku yi haka ta wurin zaman lafiya da juna.

  5. Dukanku jiki ɗaya ne, kuna kuma da Ruhu guda. An ba ku bege guda sa’ad da aka kira ku.

  6. Ku kuma ɗauki hular kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah.

  7. A koyaushe ku kasance kuna addu’a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fasawa. A kan wannan manufa ku zauna a faɗake da matuƙar naci, kuna yin wa dukan mutanen Ubangiji addu’a.

  8. domin bishararmu ba tă zo gare ku da kalmomi kawai ba, amma da iko, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma cikakken tabbaci. Kun san irin rayuwar da muka yi a cikinku don amfaninku.

  9. Har kuka zama masu koyi da mu da kuma Ubangiji; duk da tsananin wahala, kuka karɓi saƙon nan da farin ciki wanda Ruhu Mai Tsarki ya bayar.

  10. Saboda haka, duk wanda ya ƙi wannan umarni ba mutum ne ya ƙi ba sai ko Allah, wanda ya ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.

  11. Yanzu kuwa game da ƙaunar ’yan’uwa, ba ma bukata mu rubuta muku, gama ku kanku Allah ya riga ya koya muku ku ƙaunaci juna.

  12. sai ya cece mu, ba saboda abubuwan adalcin da muka aikata ba, sai dai saboda jinƙansa. Ya cece mu ta wurin wankan nan na sāke haihuwa da kuma sabuntawan nan ta Ruhu Mai Tsarki,

  13. wanda ya zubo mana a yalwace ta wurin Yesu Kiristi Mai Cetonmu,

  14. suna ƙoƙari su san lokaci da kuma yanayin da Ruhun Kiristi da yake cikinsu yana nunawa sa’ad da ya yi faɗi a kan wahalolin Kiristi da kuma ɗaukaka da za tă bi.

  15. Aka bayyana musu cewa ba kansu ne suke bauta wa ba sai ku, sa’ad da suka yi maganar abubuwan da aka faɗa muku ta wurin waɗanda suka yi muku wa’azin bishara, ta wurin Ruhu Mai Tsarki wanda aka aika daga sama. Ko mala’iku ma suna marmari su ga waɗannan abubuwa.

  16. Ga wanda ya zo ta wurin ruwa da jini, wato, Yesu Kiristi. Bai zo ta wurin ruwa kaɗai ba, sai dai ta wurin ruwa da kuma jini. Ruhu ne kuwa yake ba da shaida, gama Ruhu shi ne gaskiya.

  17. Akwai shaidu uku, wato,

  18. Ruhu, da ruwa, da kuma jini; waɗannan uku kuwa manufarsu ɗaya ce.

  19. Waɗannan mutanen ne, suke kawo rabe-rabe, masu bin abin da jiki yake so, marasa Ruhu.

  20. Amma ku, abokaina ƙaunatattu, ku gina kanku cikin bangaskiyarku mafi tsarki, ku kuma yi addu’a cikin Ruhu Mai Tsarki.