Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Holy Spirit

145 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Waɗanda mutuntaka yake mulkinsu ba za su iya su gamshi Allah ba.

  2. Ku kam, ana mulkinku ba ta wurin mutuntaka ba, sai dai ta wurin Ruhu, in Ruhun Allah yana zaune a cikinku. In kuma wani ba shi da Ruhun Kiristi, shi ba na Kiristi ba ne.

  3. Amma in Kiristi yana a cikinku, jikinku matacce ne saboda zunubi, duk da haka ruhunku yana a raye saboda adalci.

  4. In kuwa Ruhu wannan da ya tā da Yesu daga matattu yana zama a cikinku, shi wanda ya tā da Kiristi daga matattu zai ba da rai ga jikunanku masu mutuwa ta wurin Ruhunsa, wanda yake zama a cikinku.

  5. Saboda haka ’yan’uwa, muna da hakki, amma ba na wanda za mu yi rayuwar mutuntaka da yake so ba.

  6. Gama in kuna rayuwa bisa ga mutuntaka, za ku mutu; amma in ta wurin Ruhu kuka kashe ayyukan jikin nan, za ku rayu.

  7. Domin waɗanda Ruhun Allah yake bi da su ne ’ya’yan Allah.

  8. Gama ba ku karɓi ruhun da ya mai da ku bayi da za ku sāke jin tsoro ba ne, sai dai kun karɓi Ruhun zaman ɗa. Ta wurinsa kuwa muke kira, “Abba, Uba.”

  9. Ruhu kansa yana ba da shaida tare da ruhunmu cewa mu ’ya’yan Allah ne.

  10. In kuwa mu ’ya’ya ne, to, mu magāda ne, magādan Allah da kuma abokan gādo tare da Kiristi, in kuwa muna tarayya a cikin shan wuyarsa to, za mu yi tarayya a cikin ɗaukakarsa.

  11. A ganina, wuyar da muke sha a wannan lokaci ba su isa a kwatanta da ɗaukakar da za a bayyana a cikinmu ba.

  12. Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar ’ya’yan Allah.

  13. Gama an sa halitta a cikin wulaƙanci, ba da son ta ba, sai dai ta wurin nufin wannan da ya mai da ita haka, da bege

  14. cewa za a ’yantar da halitta kanta daga bautarta ga ruɓewa a kuma kawo ta cikin ’yancin ɗaukakar ’ya’yan Allah.

  15. Mun san cewa dukan halitta tana nishi sai ka ce mace mai naƙuda har yă zuwa wannan lokaci.

  16. Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu ’ya’yan riƙo na Allah, fansar jikunanmu.

  17. Gama a wannan begen ne muka sami ceto. Amma begen da ake gani ba bege ba ne sam. Wa yake begen abin da ya riga ya samu?

  18. Amma in muna begen abin da ba mu riga mun samu tukuna ba, mukan jira da haƙuri.

  19. Haka nan ma, Ruhu yana taimakonmu cikin rashin ƙarfinmu. Ba mu san abin da ya kamata mu roƙa cikin addu’a ba, amma Ruhu kansa yana roƙo a madadinmu da nishe-nishen da kalmomi ba sa iya bayyanawa.

  20. Shi kuma wanda yake binciken zukatanmu ya san halin Ruhu, domin Ruhu yana roƙo a madadin tsarkaka bisa ga nufin Allah.

  21. Kai, zurfin yalwar hikima da kuma sanin Allah yana nan a yalwace! Hukunce-hukuncensa kuma su fi gaban bincike, hanyoyinsa kuwa sun wuce gaban ganewa!

  22. “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji? Ko kuwa yă ba shi shawara?”

  23. Ba zan yi karambani in faɗi kome ba sai dai abin da Kiristi ya aikata ta wurina a jagorantar da Al’ummai su yi biyayya ga Allah ta wurin abin da na faɗa da kuma aikata

  24. ta wurin ikon alamu da ayyukan banmamaki, da kuma ikon Ruhun Allah. Ta haka daga Urushalima har yă zuwa kewayen Illirikum, na yi wa’azin bisharar Kiristi.

  25. Amma Allah ya bayyana mana shi ta wurin Ruhunsa. Ruhu yana bincika dukan abubuwa, har ma da abubuwa masu zurfi na Allah.