Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Aaron

145 ayoyi · 27 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ahitub mahaifin Zadok, Zadok mahaifin Shallum,

  2. Shallum mahaifin Hilkiya, Hilkiya mahaifin Azariya,

  3. Azariya mahaifin Serahiya, Serahiya kuwa mahaifin Yehozadak.

  4. Yehozadak ne aka ɗauka sa’ad da Ubangiji ya tura Yahuda da Urushalima zuwa zaman bauta ta hannun Nebukadnezzar.

  5. Waɗannan su ne zuriyar Haruna, Eleyazar, Finehas, Abishuwa,

  6. Bukki, Uzzi, Zerahiya,

  7. Merahiyot, Amariya, Ahitub,

  8. Zadok da Ahimawaz.

  9. ’Ya’yan Amram maza su ne, Haruna da Musa. Haruna shi ne aka keɓe, shi da zuriyarsa har abada, don su tsarkake kayayyakin mafi tsarki, su miƙa hadayu a gaban Ubangiji, su yi hidima a gabansa su kuma furta albarku a cikin sunansa har abada.

  10. Waɗannan su ne sassan ’ya’yan Haruna maza. ’Ya’yan Haruna maza su ne Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar.

  11. Amma Nadab da Abihu sun mutu kafin mahaifinsu, ba su kuma haifi ’ya’ya maza ba; saboda haka Eleyazar da Itamar suka yi hidimar firistoci.

  12. Suka kalubalance shi suka ce, “Ba daidai ba ne, Uzziya, ka ƙone turare ga Ubangiji. Wannan aikin firistoci zuriyar Haruna ne, waɗanda aka tsarkake don ƙone turare. Ka bar wuri mai tsarki, gama ka kasance marar aminci; kuma Ubangiji Allah ba zai girmama ka ba.”

  13. Ka bi da mutanenka kamar garke ta hannun Musa da Haruna.

  14. Musa da Haruna suna cikin firistocinsa, Sama’ila yana cikin waɗanda suka kira bisa sunansa; sun kira ga Ubangiji ya kuwa amsa musu.

  15. Ya aiki Musa bawansa, da Haruna, wanda ya zaɓa.

  16. A sansani suka ji kishin Musa da kuma Haruna, wanda Ubangiji ya keɓe.

  17. Na fito da ku daga ƙasar Masar na kuma ’yantar da ku daga ƙasar bauta. Na aika da Musa yă jagorance ku, haka ma Haruna da Miriyam.

  18. Suka ce wa Haruna, ‘Ka yi mana allolin da za su yi mana jagora. Game da wannan Musa ɗin wanda ya fitar da mu daga Masar, ba mu san abin da ya faru da shi ba!’

  19. Ba wanda yakan kai kansa a wannan matsayi mai girma; sai ko Allah ya kira shi, kamar yadda aka yi wa Haruna.

  20. wanda yake da bagaden zinariya na turare da kuma akwatin alkawarin da aka dalaye da zinariya. A cikin akwatin alkawarin akwai tulun zinariya mai Manna a ciki, sandan Haruna wanda ya yi toho, da kuma allunan dutsen alkawari.