Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Aaron: Not permitted to enter Canaan

8 ayoyi · 27 fannoni

Ayoyi game da Not permitted to enter Canaan

  1. Amma Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna. “Tun da yake ba ku gaskata ni ba, ba ku kuwa ɗaukaka ni a idon Isra’ilawa ba, to, ba za ku kai taron jama’an nan a ƙasar da na ba su ba.”

  2. A Dutsen Hor, kusa da iyakar Edom, Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

  3. “Haruna zai rasu. Ba zai shiga ƙasar da na ba Isra’ilawa ba, domin ku biyu, kun ƙi ku bi umarnina a ruwan Meriba.

  4. Ka kawo Haruna da ɗansa Eleyazar, ka kai su a bisan Dutsen Hor.

  5. Ka tuɓe taguwar Haruna ka sa wa ɗansa Eleyazar, gama Haruna zai rasu a can.”

  6. Musa ya yi yadda Ubangiji ya umarta. Suka hau Dutsen Hor a idon dukan jama’a.

  7. Musa ya tuɓe taguwar Haruna, ya kuma sa wa Eleyazar ɗan Haruna. Nan kuwa Haruna ya mutu a bisa dutsen. Sa’an nan Musa da Eleyazar suka sauka daga dutsen,

  8. sa’ad da dukan jama’a kuwa suka ji cewa Haruna ya mutu, sai dukan gidan Isra’ila suka yi makoki dominsa har kwana talatin.