Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Aaron: Murmured against, by the people

28 ayoyi · 27 fannoni

Ayoyi game da Murmured against, by the people

Tace bisa littafi
  1. Da suka bar Fir’auna, sai suka sadu da Musa da Haruna suna jira su sadu da su,

  2. sai suka ce, “Bari Ubangiji yă duba, yă kuma hukunta ku! Kun maishe mu abin ƙyama ga Fir’auna da bayinsa, kuka kuma sa musu takobi a hannunsu don su kashe mu.”

  3. A hamadan, dukan taro suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna.

  4. Isra’ilawa suka ce musu, “Da ma a hannun Ubangiji ne muka mutu a Masar, inda muka zauna kewaye da tukwanen nama, muna cin duk abincin da muke so, amma kun kawo mu cikin wannan hamada don ku kashe dukan wannan taro da yunwa.”

  5. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan zubo muku burodi kamar ruwa daga sama. Mutanen za su fita kowace rana su tattara abin da zai ishe su na ranan. Ta haka zan gwada su in ga ko za su bi umarnaina.

  6. A rana ta shida za su shirya abin da suka kwaso, wannan kuwa zai zama ninki biyu na abin da sukan tattara na sauran ranaku.”

  7. Saboda haka Musa da Haruna suka ce wa dukan Isra’ila, “Da yamma za ku sani Ubangiji ne ya fitar da ku daga Masar.

  8. Da safe za ku ga ɗaukakar Ubangiji, saboda ya ji gunaguninku a kansa. Wane mu, da za ku yi gunaguni a kanmu?”

  9. Musa ya kuma ce, “Za ku san cewa shi ne Ubangiji, sa’ad da ya ba ku nama ku ci da yamma, da kuma duk burodin da kuke so da safe, saboda ya ji gunagunin da kuka yi a kansa. Namu a wane? Ai, gunaguninku ba a kanmu ba, amma a kan Ubangiji ne.”

  10. Sai Musa ya ce wa Haruna, “Ka faɗa wa dukan taron Isra’ila, ‘Ku zo gaban Ubangiji, gama ya ji gunaguninku.’ ”

  11. Yayinda Haruna yake magana da dukan taron Isra’ila, sai suka duba wajen hamada, sai ga ɗaukakar Ubangiji tana bayyana a girgije.

  12. Dukan Isra’ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna, dukan taron kuwa suka ce musu, “Da ma mun mutu a Masar! Ko kuma a wannan hamada ma!

  13. Don me Ubangiji yana kawo mu wannan ƙasa yă bar mu kawai mu mutu da takobi? A kuma kwashe matanmu da ’ya’yanmu ganima. Ashe, bai fi mana mu koma Masar ba?”

  14. Sai suka ce wa junansu, “Mu naɗa wa kanmu shugaba, mu koma Masar.”

  15. Sai Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki a gaban jama’ar Isra’ilawa da suka taru a can.

  16. Amma taron jama’a suka ce za su jajjefe su da duwatsu. Sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana a Tentin Sujada ga dukan Isra’ilawa.

  17. tare kuwa suka zo wurin Musa da Haruna, suka ce musu, “Kun wuce gona da iri! Dukan jama’an nan masu tsarki ne, kowannensu, Ubangiji kuma yana tare da su. Me ya sa kuke ɗaukan kanku fiye da taron jama’ar Ubangiji?”

  18. Da Musa ya ji haka, sai ya fāɗi rubda ciki ya yi addu’a

  19. Sai ya ce wa Kora da dukan waɗannan da suke tare shi, “Da safe, Ubangiji zai nuna wane ne yake nasa, da kuma wane ne yake da tsarki. Zai kuma sa mutumin yă zo kusa da shi. Mutumin da ya zaɓa kuwa zai sa yă zo kusa da shi.

  20. Kai Kora da ƙungiyarka, gobe, za ku ɗauki farantai,

  21. ku zuba wuta a ciki, ku kuma zuba musu turaren wuta a gaban Ubangiji. Sa’an nan wanda Ubangiji ya zaɓa a tsakaninmu sh ne mai tsarki. Ku Lawiyawa ku ne kuka wuce gona da iri!”

  22. Musa ya kuma ce wa Kora, “Yanzu ku saurara, ku Lawiyawa!

  23. Ashe, bai ishe ku ba, cewa Allah na Isra’ila, ya keɓe ku daga sauran jama’ar Isra’ilawa, ya kuma kawo ku kusa da shi don ku yi aiki a tabanakul na Ubangiji, ku kuma tsaya a gaba jama’a don ku yi musu aiki?

  24. Ya kawo ku da kuma dukan ’yan’uwanku Lawiyawa kusa da shi, amma yanzu kuna ƙoƙari ku karɓi aikin firist.

  25. Kai da ƙungiyarka kun haɗa kai kuna yi wa Haruna gunaguni, amma wane ne Haruna? A zahiri tawaye ne kuke wa Ubangiji.”