Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Aaron: Rod of, preserved

14 ayoyi · 27 fannoni

Ayoyi game da Rod of, preserved

  1. Ubangiji ya ce wa Musa,

  2. “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka kuma karɓi sanduna goma sha biyu daga wurinsu, sanda guda daga kowane shugaban gidan kakanninsu. Ka rubuta sunan kowa a sandansa.

  3. A kan sandan Lawi kuwa ka rubuta sunan Haruna, gama dole a sami sanda ɗaya saboda shugaban gidan kakanninsu.

  4. Ka ajiye su a Tentin Sujada, a gaba akwatin Alkawari, inda zan sadu da kai.

  5. Sandan mutumin da na zaɓa zai yi toho, da haka zan raba kaina da gunagunin da Isra’ilawa suke yi.”

  6. Saboda haka Musa ya yi magana da Isra’ilawa, sai shugabanninsu suka ba shi sanduna goma sha biyu, sanda ɗaya don shugaba, bisa ga gidajen kakanninsu, sandan Haruna kuma yana a cikinsu.

  7. Sai Musa ya ajiye sandunan a gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada.

  8. Kashegari da Musa ya shiga cikin Tentin Sujada sai ga sandan Haruna na gidan Lawiyawa ya yi toho, ya yi furanni, ya kuma yi ’ya’yan almon.

  9. Sai Musa ya fitar wa dukan Isra’ilawa dukan sandunan da suke daga gaban Ubangiji. Suka duba, kowa kuma ya ɗauki sandansa.

  10. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka mayar da sandan Haruna a akwatin Alkawari, don a ajiye shi alama ga masu tawaye. Wannan zai kawo ƙarshen gunaguninsu a kaina, domin kada su mutu.”

  11. Musa kuwa ya aikata kamar dai yadda Ubangiji ya umarce shi.

  12. Sai Isra’ilawa suka ce wa Musa, “To, ai in haka ne, mun ƙare ke nan!

  13. Idan an ce duk wanda ya zo kusa da tabanakul na Ubangiji zai mutu, ai rayuwarmu kamar mun mutu ke nan.”

  14. wanda yake da bagaden zinariya na turare da kuma akwatin alkawarin da aka dalaye da zinariya. A cikin akwatin alkawarin akwai tulun zinariya mai Manna a ciki, sandan Haruna wanda ya yi toho, da kuma allunan dutsen alkawari.