Tsallake zuwa abun ciki

Abihu

12 ayoyi · 5 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Abihu

  1. Haruna ya auri Elisheba, ’yar Amminadab, ’yar’uwar Nashon, sai ta haifa masa Nadab da Abihu, Eleyazar da Itamar.

  2. Ana nan sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ku hauro zuwa wurina, kai da Haruna, Nadab da Abihu, da kuma dattawa saba’in a cikin Isra’ila. Za ku yi sujada da ɗan nisa,

  3. Musa da Haruna, Nadab da Abihu, da dattawa saba’in, Allah na Isra’ila suka haura

  4. “Ka sa a kawo maka Haruna ɗan’uwanka, tare da ’ya’yansa Nadab da Abihu, Eleyazar da Itamar daga cikin Isra’ilawa, domin su yi mini hidima a matsayin firistoci.

  5. ’Ya’yan Haruna maza, Nadab da Abihu suka ɗauki farantansu, suka sa wuta a ciki, suka zuba turare a kai; suka kuma miƙa haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji, ba irin wadda Ubangiji ya umarta ba.

  6. Sunayen ’ya’yan Haruna su ne, Nadab ɗan fari, da Abihu, da Eleyazar da Itamar.

  7. Amma Nadab da Abihu suka fāɗi suka mutu a gaban Ubangiji a Hamadar Sinai a sa’ad da suka ƙona turare da haramtacciyar wuta a gabansa. Ba su kuwa da ’ya’ya; saboda haka Eleyazar da Itamar kaɗai suka yi aiki firist a zamanin mahaifinsu Haruna.

  8. Haruna shi ne mahaifin Nadab, Abihu, Eleyazar da kuma Itamar.

  9. Amma Nadab da Abihu sun mutu sa’ad da suka miƙa hadaya da haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji.)

  10. Yaran Amram su ne, Haruna, Musa da Miriyam. ’Ya’yan Haruna maza su ne, Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar.

  11. Waɗannan su ne sassan ’ya’yan Haruna maza. ’Ya’yan Haruna maza su ne Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar.

  12. Amma Nadab da Abihu sun mutu kafin mahaifinsu, ba su kuma haifi ’ya’ya maza ba; saboda haka Eleyazar da Itamar suka yi hidimar firistoci.