Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Abihu

8 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Haruna ya auri Elisheba, ’yar Amminadab, ’yar’uwar Nashon, sai ta haifa masa Nadab da Abihu, Eleyazar da Itamar.

  2. Musa da Haruna, Nadab da Abihu, da dattawa saba’in, Allah na Isra’ila suka haura

  3. “Ka sa a kawo maka Haruna ɗan’uwanka, tare da ’ya’yansa Nadab da Abihu, Eleyazar da Itamar daga cikin Isra’ilawa, domin su yi mini hidima a matsayin firistoci.

  4. ’Ya’yan Haruna maza, Nadab da Abihu suka ɗauki farantansu, suka sa wuta a ciki, suka zuba turare a kai; suka kuma miƙa haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji, ba irin wadda Ubangiji ya umarta ba.

  5. Sai wuta ta fito daga Ubangiji ta cinye su, suka kuma mutu a gaban Ubangiji.

  6. Sunayen ’ya’yan Haruna su ne, Nadab ɗan fari, da Abihu, da Eleyazar da Itamar.

  7. Amma Nadab da Abihu suka fāɗi suka mutu a gaban Ubangiji a Hamadar Sinai a sa’ad da suka ƙona turare da haramtacciyar wuta a gabansa. Ba su kuwa da ’ya’ya; saboda haka Eleyazar da Itamar kaɗai suka yi aiki firist a zamanin mahaifinsu Haruna.

  8. Amma Nadab da Abihu sun mutu sa’ad da suka miƙa hadaya da haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji.)