Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Altar of Incense

32 ayoyi · 17 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Ka yi bagade da itacen ƙirya don ƙona turare.

  2. Zai zama murabba’i, tsawon zai zama kamu ɗaya, fāɗi kuma kamu ɗaya, amma tsayin yă zama kamu biyu, ƙahoninsa kuma su zama ɗaya da shi.

  3. Ka dalaye bisansa da kuma dukan gefe-gefensa da kuma ƙahoninsa da zinariya zalla, ka kuma yi zubi na zinariya kewaye da shi.

  4. Ka yi zobai biyu na zinariya domin bagade a ƙarƙashin zubin, biyu a gefe da gefe su fuskanci juna, don su riƙe sandunan da ake amfani da su don ɗaukarsa.

  5. Ka yi sandunan nan da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya.

  6. Ka sa bagaden a gaban labulen da yake gaban akwatin alkawari, a gaba murfin kafara wanda yake bisa akwatin alkawari, inda zan sadu da kai.

  7. “Haruna zai ƙone turare a bisa bagaden kowace safiya, sa’ad da yake shirya fitilu.

  8. Dole Haruna yă ƙone turare sa’ad da ya ƙuna fitilu da yamma, ta haka za a riƙa ƙona turare a gaban Ubangiji, daga tsara zuwa tsara.

  9. Ba za a ƙona wani irin turare dabam a bisa wannan bagade ba, ba kuma za a miƙa hadaya ta ƙonawa, ko ta hatsi, ko ta sha a bisansa ba.

  10. Sau ɗaya a shekara, Haruna zai yi kafara a bisa ƙahoninsa. Dole a yi wannan kafara ta shekara-shekara da jinin kafara ta hadaya don zunubi daga tsara zuwa tsara. Gama bagaden mafi tsarki ne ga Ubangiji.”

  11. Sa’an nan ka yi amfani da shi don shafa wa Tentin Sujada, da akwatin alkawari,

  12. da tebur da kuma dukan kayansa, da wurin ajiye fitila da dukan kayansa, da bagaden ƙona turare,

  13. Suka yi bagaden ƙona turare da itacen ƙirya. Shi bagaden, murabba’i ne, tsawonsa kamu ɗaya, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu biyu, ƙahoninsa kuwa a haɗe suke da shi.

  14. Suka dalaye saman da dukan gefe-gefen da kuma ƙahonin da zinariya zalla, suka kuma yi zubin zinariya kewaye da shi.

  15. Suka yi zobai biyu na zinariya a ƙarƙashin zubin, biyu-biyu ɗaura da juna, don su riƙe sandunan da za a ɗauka shi.

  16. bagade na zinariya, da man shafewa, da turare mai ƙanshi, da labulen ƙofar shiga tenti,

  17. Ka sa bagaden zinariya na ƙona turare a gaban akwatin Alkawari, ka kuma sa labule a ƙofar shiga tabanakul.

  18. Musa ya sa bagaden zinariya a cikin Tentin Sujada a gaban labulen

  19. Sa’an nan firist ɗin zai zuba jinin a ƙahonin bagaden turare masu ƙanshi da suke a gaban Ubangiji a Tentin Sujada. Sauran jinin bijimin zai zuba a gindin bagaden hadaya ta ƙonawa a ƙofar zuwa Tentin Sujada.

  20. Zai zuba jinin a ƙahonin bagaden da suke gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada. Zai zuba sauran jinin a gindin bagaden hadaya ta ƙonawa a ƙofar zuwa Tentin Sujada.

  21. ’Ya’yan Haruna maza, Nadab da Abihu suka ɗauki farantansu, suka sa wuta a ciki, suka zuba turare a kai; suka kuma miƙa haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji, ba irin wadda Ubangiji ya umarta ba.

  22. Sai wuta ta fito daga Ubangiji ta cinye su, suka kuma mutu a gaban Ubangiji.

  23. “Sa’an nan zai fita zuwa bagade da yake a gaban Ubangiji, yă yi kafara dominsa. Zai ɗibi jinin bijimi da na akuya yă zuba a ƙahonin bagade.

  24. Zai yayyafa jinin a kan bagade da yatsarsa sau bakwai, yă tsabtacce shi yă kuma tsarkake shi daga ƙazantar Isra’ilawa.

  25. “A kan bagaden zinariya, za su shimfiɗa zane mai ruwan shuɗi, su kuma rufe shi da fatar shanun teku, sai a zura masa sandunansa.