- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446–1406 BC
The Wilderness Years
Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ƙidaya 20:19kusan 1471 K.H.
Sai Isra’ilawa suka amsa, suka ce, “Za mu bi ta babbar hanya, in mu, ko dabbobinmu suka sha ruwanku, za mu biya. Mu dai muna so mu wuce ne kawai.”
- Ƙidaya 20:20kusan 1471 K.H.
Sai mutanen Edom suka sāke amsa suka ce, “Ba za ku bi nan ba dai.” Sai Edom ya fito da runduna mai ƙarfi da yawa gaske a kan Isra’ila.
- Ƙidaya 20:21kusan 1471 K.H.
Da yake Edom suka ƙi su bar su su ratsa yankinsu, sai Isra’ila suka juya suka janye daga gare su.
- Ƙidaya 20:22kusan 1471 K.H.
Dukan Jama’ar Isra’ilawa suka tashi daga Kadesh, suka zo Dutsen Hor.
- Ƙidaya 20:23kusan 1471 K.H.
A Dutsen Hor, kusa da iyakar Edom, Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,
- Ƙidaya 20:24kusan 1471 K.H.
“Haruna zai rasu. Ba zai shiga ƙasar da na ba Isra’ilawa ba, domin ku biyu, kun ƙi ku bi umarnina a ruwan Meriba.
- Ƙidaya 20:25kusan 1471 K.H.
Ka kawo Haruna da ɗansa Eleyazar, ka kai su a bisan Dutsen Hor.
- Ƙidaya 20:26kusan 1471 K.H.
Ka tuɓe taguwar Haruna ka sa wa ɗansa Eleyazar, gama Haruna zai rasu a can.”
- Ƙidaya 20:27kusan 1471 K.H.
Musa ya yi yadda Ubangiji ya umarta. Suka hau Dutsen Hor a idon dukan jama’a.
- Ƙidaya 20:28kusan 1471 K.H.
Musa ya tuɓe taguwar Haruna, ya kuma sa wa Eleyazar ɗan Haruna. Nan kuwa Haruna ya mutu a bisa dutsen. Sa’an nan Musa da Eleyazar suka sauka daga dutsen,
- Ƙidaya 20:29kusan 1471 K.H.
sa’ad da dukan jama’a kuwa suka ji cewa Haruna ya mutu, sai dukan gidan Isra’ila suka yi makoki dominsa har kwana talatin.
- Ƙidaya 21:1kusan 1453 K.H.
Sa’ad da sarkin Arad, mutumin Kan’ana, wanda yake zaune a Negeb, da ya ji cewa Isra’ila yana zuwa ta hanyar Atarim, sai ya fito, yă yaƙi Isra’ilawa, yă kuma kama waɗansunsu.
- Ƙidaya 21:2kusan 1453 K.H.
Sai Isra’ila suka yi alkawari wa Ubangiji suka ce, “In ka ba da waɗannan mutane a hannunmu, za mu hallaka dukan garuruwansu ƙaf.”
- Ƙidaya 21:3kusan 1453 K.H.
Ubangiji kuwa ya saurari kukan Isra’ila, ya kuma ba da Kan’aniyawa a gare su. Suka hallaka su da biranensu ƙaf; saboda haka aka sa wa wurin suna Horma.
- Ƙidaya 21:4kusan 1453 K.H.
Suka kama hanya daga Dutsen Hor ta hanya zuwa Jan Teku, don su kauce wa Edom. Amma mutane suka rasa haƙuri a hanya;
- Ƙidaya 21:5kusan 1453 K.H.
suka yi wa Allah da Musa gunaguni, suka ce, “Me ya sa kuka fitar da mu daga Masar, kuka kawo mu mu mutu a wannan hamada? Babu abinci! Babu ruwa! Mu dai mun gaji da wannan abinci marar amfani!”
- Ƙidaya 21:6kusan 1453 K.H.
Sai Ubangiji ya aiko da macizai masu dafin a cikinsu, suka sassari mutane, Isra’ilawa masu yawa kuwa suka mutu.
- Ƙidaya 21:7kusan 1453 K.H.
Mutanen suka zo wurin Musa, suka ce, “Mun yi zunubi, da muka yi wa Ubangiji da kai gunaguni. Ka yi addu’a don Ubangiji yă ɗauke mana macizan nan.” Saboda haka Musa ya yi addu’a domin mutane.
- Ƙidaya 21:8kusan 1453 K.H.
Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙera siffar maciji ka rataye shi a bisa doguwar sanda; kowa da maciji ya sare shi, idan ya dubi macijin nan da ka rataye, zai rayu.”
- Ƙidaya 21:9kusan 1453 K.H.
Saboda haka Musa ya ƙera macijin tagulla, ya kuma rataye shi bisa doguwar sanda. Sa’an nan duk wanda maciji ya sare shi, ya kuma dubi macijin tagullar, zai warke.
- Ƙidaya 21:10kusan 1453 K.H.
Isra’ilawa suka kama hanya, suka yi sansani a Obot.
- Ƙidaya 21:11kusan 1453 K.H.
Sai suka tashi daga Obot, suka yi sansani a Iye Abarim a hamadar da take fuskantar Mowab, wajen fitowar rana.
- Ƙidaya 21:12kusan 1453 K.H.
Daga nan kuma suka ci gaba, suka yi sansani a Kwarin Zered.
- Ƙidaya 21:13kusan 1453 K.H.
Suka tashi daga nan, suka sauka kusa da Arnon wanda yake a hamadar da ta miƙe zuwa iyakar Amoriyawa. Arnon shi ne iyakar Mowab, wanda yake tsakanin Mowab da Amoriyawa.
- Ƙidaya 21:14kusan 1453 K.H.
Shi ya sa Littafin Yaƙoƙin Ubangiji ya ce, “Waheb ta cikin yankin Sufa, da kwaruruka na tuddan Arnon,