- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446–1406 BC
The Wilderness Years
Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ƙidaya 18:23kusan 1471 K.H.
Lawiyawa ne za su yi aikin Tentin Sujada, su kuma ɗauki nauyin kowane laifin da aka aikata a wurin. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce daga yanzu har tsararraki masu zuwa. Ba za su sami gādo a cikin Isra’ilawa ba.
- Ƙidaya 18:24kusan 1471 K.H.
A maimako haka, na ba wa Lawiyawa zakka da Isra’ilawa suka kawo domin hadaya ga Ubangiji, a matsayin gādonsu. Shi ya sa na ce game da su, ‘Ba su da gādo a cikin Isra’ilawa.’ ”
- Ƙidaya 18:25kusan 1471 K.H.
Ubangiji ya ce wa Musa,
- Ƙidaya 18:26kusan 1471 K.H.
“Ka yi wa Lawiyawa magana, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka karɓi zakka daga Isra’ila da na ba ku gādo, dole ku miƙa kashi ɗaya bisa goma na wannan zakka a matsayin hadaya ga Ubangiji.
- Ƙidaya 18:27kusan 1471 K.H.
Za a lissafta hadayarku kamar hatsin da aka sussuka daga masussuka, ko ruwan inabi daga wurin matsewar inabi.
- Ƙidaya 18:28kusan 1471 K.H.
Ta haka za ku miƙa hadaya ga Ubangiji daga cikin dukan zakkar da kuka karɓa daga wurin Isra’ilawa. Daga waɗannan zakka kuwa dole ku ba Haruna firist rabon Ubangiji.
- Ƙidaya 18:29kusan 1471 K.H.
Dole ku miƙa wa Ubangiji rabo mafi kyau da kuma sashi mafi tsarki na kowane abin da aka ba ku.’
- Ƙidaya 18:30kusan 1471 K.H.
“Ka faɗa wa Lawiyawa cewa, ‘Sa’ad da kuka miƙa sashi mafi kyau, za a lissafta shi a matsayin abin da ya fito daga masussuka, ko wurin matsewar ruwan inabi ne.
- Ƙidaya 18:31kusan 1471 K.H.
Da kai da gidanka, za ku iya cin abin da ya rage a ko’ina, gama ladan aikinku ne a Tentin Sujada.
- Ƙidaya 18:32kusan 1471 K.H.
Ta wurin miƙa masa sashi mafi kyau, ba za ku zama masu laifi a wannan batu ba; ta haka ba za ku ƙazantar da tsarkakakkun hadayu na Isra’ilawa ba, ba kuwa za ku mutu ba.’ ”
- Ƙidaya 19:1kusan 1471 K.H.
Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,
- Ƙidaya 19:2kusan 1471 K.H.
“Wannan ita ce ƙa’ida wadda Ubangiji ya umarta. Faɗa wa Isra’ilawa su kawo maka jan karsana marar lahani, ko marar aibi wadda ba a taɓa sa ta tă yi noma ba.
- Ƙidaya 19:3kusan 1471 K.H.
Ka ba wa Eleyazar firist; a kuma kai ta bayan sansani, a yanka a gaban Eleyazar.
- Ƙidaya 19:4kusan 1471 K.H.
Sa’an nan Eleyazar firist zai ɗiba jininta a yatsarsa, yă yayyafa sau bakwai wajen gaban Tentin Sujada.
- Ƙidaya 19:5kusan 1471 K.H.
Sa’an nan a ƙone dukan karsanar, haɗe da fatarta, naman, jinin da kayan cikin, yayinda Eleyazar yake kallo.
- Ƙidaya 19:6kusan 1471 K.H.
Firist zai ɗauki itacen al’ul, da hizzob, da jan ulu, yă jefa su a kan karsanar da ake ƙonewa.
- Ƙidaya 19:7kusan 1471 K.H.
Bayan haka, dole firist yă wanke rigunarsa, yă kuma yi wanka. Sa’an nan zai iya shiga cikin sansani, amma zai kasance da ƙazanta har yamma.
- Ƙidaya 19:8kusan 1471 K.H.
Dole mutumin da ya ƙone ta yă wanke rigunarsa, yă kuma yi wanka, shi ma zai kasance da ƙazanta har yamma.
- Ƙidaya 19:9kusan 1471 K.H.
“Mutumin da yake da tsarki, zai tara tokar karsanar, yă sa ta a wurin da yake da tsabta a bayan sansani. Jama’ar Isra’ilawa ne za su adana shi don amfani a ruwan tsabtaccewa; wannan domin tsarkakewa ne daga zunubi.
- Ƙidaya 19:10kusan 1471 K.H.
Dole mutumin da ya tara tokar karsanar yă wanke rigunarsa, zai kuwa kasance da ƙazanta har yamma. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ta har abada ga Isra’ilawa, da kuma baƙin da suke zama a cikinsu.
- Ƙidaya 19:11kusan 1471 K.H.
“Duk wanda ya taɓa gawa, zai kasance da ƙazanta har kwana bakwai.
- Ƙidaya 19:12kusan 1471 K.H.
Dole yă tsarkake kansa da ruwa a rana ta uku, da kuma a rana ta bakwai; sa’an nan zai zama da tsarki. Amma in bai tsarkake kansa a rana ta uku da kuma a rana ta bakwai ba, ba zai kasance da tsarki ba.
- Ƙidaya 19:13kusan 1471 K.H.
Duk wanda ya taɓa gawar wani, bai kuma tsarkake kansa ba, ya ƙazantar da tabanakul na Ubangiji ke nan. Dole a ware wannan mutum daga cikin Isra’ilawa. Gama ba a yayyafa ruwan tsabtaccewa a kansa ba; ya ƙazantu, ya kasance da ƙazanta ke nan.
- Ƙidaya 19:14kusan 1471 K.H.
“Ga ƙa’idar da za a bi in mutum ya mutu a cikin tenti. Duk wanda ya shiga tentin, kuma duk wanda yake cikinsa, za su zama da ƙazanta har kwana bakwai,
- Ƙidaya 19:15kusan 1471 K.H.
kuma kowane abin da ake zuba kaya, wanda ba shi da murfi a kansa, zai zama da ƙazanta.