Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ƙidaya 16:36kusan 1471 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,

  2. Ƙidaya 16:37kusan 1471 K.H.

    “Ka gaya wa Eleyazar ɗan Haruna, firist, yă kawar da farantan ƙona turare daga wurin da wutar ta cinye, yă watsar da gawayin a wani wuri, gama farantan tsarkakakku ne,

  3. Ƙidaya 16:38kusan 1471 K.H.

    gama an yi amfani da farantan don miƙa mini turare. Sai ka ɗauki farantan mutanen da suka yi zunubin da ya jawo musu mutuwa ka ƙera farantan, ka yi murfin bagade da su, gama an miƙa su a gaban Ubangiji, suka zama tsarkakakku. Bari su zama alama ga Isra’ilawa.”

  4. Ƙidaya 16:39kusan 1471 K.H.

    Haka Eleyazar, firist, ya tattara farantan tagulla waɗanda mutanen da aka hallaka suka kawo, ya ƙera murfin bagade da su,

  5. Ƙidaya 16:40kusan 1471 K.H.

    yadda Ubangiji ya umarce shi, ta wurin Musa. Wannan ya zama abin tuni ga Isra’ilawa domin kada wani da ba firist ba, bai kuwa fito a cikin zuriyar Haruna ba, yă zo don yă ƙona turare a gaban Ubangiji, domin kada yă zama kamar Kora da mabiyansa.

  6. Ƙidaya 16:41kusan 1471 K.H.

    Kashegari dukan taron Isra’ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna suka ce, “Kun kashe mutanen Ubangiji.”

  7. Ƙidaya 16:42kusan 1471 K.H.

    Bayan haka, sai dukan jama’a suka taru domin su nuna rashin yardansu da abin da suke zato Musa da Haruna ne suka aikata. Da suka fuskanci Tentin Sujada, nan take sai girgije ya rufe shi, ɗaukaka Ubangiji kuwa ta bayyana.

  8. Ƙidaya 16:43kusan 1471 K.H.

    Sai Musa da Haruna suka je gaban Tentin Sujada,

  9. Ƙidaya 16:44kusan 1471 K.H.

    Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

  10. Ƙidaya 16:45kusan 1471 K.H.

    “Ku nisanci wannan taro, gama yanzu nan zan hallaka su.” Sai Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki.

  11. Ƙidaya 16:46kusan 1471 K.H.

    Sai Musa ya ce wa Haruna, “Ka ɗauki farantinka ka sa turare a ciki, da wuta daga bagade, ka yi maza ka tafi wajen taron, ka yi kafara dominsu. Gama fushin Ubangiji ya riga ya sauko; an kuma fara annoba.”

  12. Ƙidaya 16:47kusan 1471 K.H.

    Saboda haka Haruna ya yi kamar yadda Musa ya faɗa, ya ruga a guje zuwa tsakiyar taron. An riga an fara annobar a cikin mutane, amma Haruna ya miƙa turaren ya kuma yi kafara dominsu.

  13. Ƙidaya 16:48kusan 1471 K.H.

    Ya tsaya tsakanin matattu da masu rai, annobar kuwa ta tsaya.

  14. Ƙidaya 16:49kusan 1471 K.H.

    Amma mutane 14,700 ne suka mutu a annobar, ban da waɗanda suka mutu a sanadin Kora.

  15. Ƙidaya 16:50kusan 1471 K.H.

    Sai Haruna ya komo wurin Musa a ƙofar Tentin Sujada, gama annobar ta ƙare.

  16. Ƙidaya 17:1kusan 1471 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,

  17. Ƙidaya 17:2kusan 1471 K.H.

    “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka kuma karɓi sanduna goma sha biyu daga wurinsu, sanda guda daga kowane shugaban gidan kakanninsu. Ka rubuta sunan kowa a sandansa.

  18. Ƙidaya 17:3kusan 1471 K.H.

    A kan sandan Lawi kuwa ka rubuta sunan Haruna, gama dole a sami sanda ɗaya saboda shugaban gidan kakanninsu.

  19. Ƙidaya 17:4kusan 1471 K.H.

    Ka ajiye su a Tentin Sujada, a gaba akwatin Alkawari, inda zan sadu da kai.

  20. Ƙidaya 17:5kusan 1471 K.H.

    Sandan mutumin da na zaɓa zai yi toho, da haka zan raba kaina da gunagunin da Isra’ilawa suke yi.”

  21. Ƙidaya 17:6kusan 1471 K.H.

    Saboda haka Musa ya yi magana da Isra’ilawa, sai shugabanninsu suka ba shi sanduna goma sha biyu, sanda ɗaya don shugaba, bisa ga gidajen kakanninsu, sandan Haruna kuma yana a cikinsu.

  22. Ƙidaya 17:7kusan 1471 K.H.

    Sai Musa ya ajiye sandunan a gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada.

  23. Ƙidaya 17:8kusan 1471 K.H.

    Kashegari da Musa ya shiga cikin Tentin Sujada sai ga sandan Haruna na gidan Lawiyawa ya yi toho, ya yi furanni, ya kuma yi ’ya’yan almon.

  24. Ƙidaya 17:9kusan 1471 K.H.

    Sai Musa ya fitar wa dukan Isra’ilawa dukan sandunan da suke daga gaban Ubangiji. Suka duba, kowa kuma ya ɗauki sandansa.

  25. Ƙidaya 17:10kusan 1471 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka mayar da sandan Haruna a akwatin Alkawari, don a ajiye shi alama ga masu tawaye. Wannan zai kawo ƙarshen gunaguninsu a kaina, domin kada su mutu.”