Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ƙidaya 16:11kusan 1471 K.H.

    Kai da ƙungiyarka kun haɗa kai kuna yi wa Haruna gunaguni, amma wane ne Haruna? A zahiri tawaye ne kuke wa Ubangiji.”

  2. Ƙidaya 16:12kusan 1471 K.H.

    Sai Musa ya aika a kira Datan da Abiram, ’ya’yan Eliyab maza, amma suka ce, “Ba za mu zo ba!

  3. Ƙidaya 16:13kusan 1471 K.H.

    Bai isa ba ne da ka fitar da mu daga ƙasar mai zub da madara da zuma, ka kawo mu nan hamada don ka kashe mu? Yanzu kuma so kake ka mai da kanka sarki a bisanmu?

  4. Ƙidaya 16:14kusan 1471 K.H.

    Ban da haka ma, ai, ba ka riga ka kai mu ƙasar mai zub da madara da zuma ba, ba ka ba mu gādon filaye da gonakin annabi ba, yanzu kuma kana so ka ruɗe mu. Mun ƙi, ba za mun zo ba!”

  5. Ƙidaya 16:15kusan 1471 K.H.

    Sai Musa ya husata ƙwarai, ya ce wa Ubangiji, “Kada ka karɓi hadayarsu. Ban ƙwace wani jakinsu ba, ban kuwa cuce waninsu ba.”

  6. Ƙidaya 16:16kusan 1471 K.H.

    Musa ya ce wa Kora, “Da kai da kuma dukan ƙungiyarka za ku bayyana a gaban Ubangiji gobe, kai da su. Haruna ma zai kasance a can.

  7. Ƙidaya 16:17kusan 1471 K.H.

    Kowannenku zai ɗauki faranti yă zuba turare a ciki. Wato, farantai 250 ke nan, a kuma miƙa su a gaban Ubangiji. Kai da Haruna za ku miƙa farantanku, ku ma.”

  8. Ƙidaya 16:18kusan 1471 K.H.

    Sai kowane mutum ya ɗauki farantinsa, ya sa wuta da kuma turare a ciki, suka tsaya da Musa da Haruna a ƙofar Tentin Sujada.

  9. Ƙidaya 16:19kusan 1471 K.H.

    Sa’ad da Kora ya tara mabiyansa don su yi hamayya da Musa da Haruna a ƙofar Tentin Sujada, sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan taron.

  10. Ƙidaya 16:20kusan 1471 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

  11. Ƙidaya 16:21kusan 1471 K.H.

    “Ku ware kanku daga taron nan don in gama da su nan take.”

  12. Ƙidaya 16:22kusan 1471 K.H.

    Amma Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki suka tā da murya suka ce, “Ya Allah, Allahn ruhohin dukan ’yan adam, za ka husata da dukan taron ne, bayan mutum ɗaya ne ya yi zunubi?”

  13. Ƙidaya 16:23kusan 1471 K.H.

    Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

  14. Ƙidaya 16:24kusan 1471 K.H.

    “Faɗa wa taron cewa, ‘Ku nisanci tentin Kora, da na Datan, da na Abiram.’ ”

  15. Ƙidaya 16:25kusan 1471 K.H.

    Musa ya tashi ya tafi wurin Datan da Abiram, dattawan Isra’ilawa kuwa suka bi shi.

  16. Ƙidaya 16:26kusan 1471 K.H.

    Ya gargaɗe taron ya ce, “Ku ƙaurace wa tentin waɗannan mugayen mutane! Kada ku taɓa kome da yake nasu, domin kada a shafe ku saboda zunubansu.”

  17. Ƙidaya 16:27kusan 1471 K.H.

    Sai suka tashi daga inda tentin Kora, da Datan, da Abiram suke. Datan da Abiram kuwa suka fita suna tsaye tare da matansu da ’ya’yansu da ’yan ƙananansu a ƙofar tentinsu.

  18. Ƙidaya 16:28kusan 1471 K.H.

    Sai Musa ya ce musu, “Da haka za ku san cewa Ubangiji ne ya aiko ni, in yi dukan waɗannan abubuwa, ba da nufin kaina na yi su ba.

  19. Ƙidaya 16:29kusan 1471 K.H.

    In waɗannan mutane sun mutu kamar yadda mutane suke mutuwa, in abin da yakan sami kowa shi ne ya same su, to, ba Ubangiji ne ya aiko ni ba.

  20. Ƙidaya 16:30kusan 1471 K.H.

    Amma in Ubangiji ya kawo wani abu sabo, ya sa ƙasa ta buɗe bakinta, ta haɗiye su da dukan abin da suke da shi, suka gangara cikin kabari a raye, ta haka za ku sani mutanen nan sun rena Ubangiji.”

  21. Ƙidaya 16:31kusan 1471 K.H.

    Nan da nan da ya gama faɗi wannan, sai ƙasa ta tsage inda Datan da Abiram suke tsaye,

  22. Ƙidaya 16:32kusan 1471 K.H.

    ta kuma buɗe bakinta, ta haɗiye su tare da mutanen gidansu da dukan mutanen Kora da dukan abin da yake mallakarsu.

  23. Ƙidaya 16:33kusan 1471 K.H.

    Suka gangara cikin kabari da rai, tare dukan mallakarsu; ƙasa ta rufe su, suka hallaka, suka rabu da jama’ar.

  24. Ƙidaya 16:34kusan 1471 K.H.

    Da jin kukansu, dukan Isra’ilawa da suke kewaye da su suka gudu, suna ihu, “Ƙasa za tă haɗiye mu, mu ma!”

  25. Ƙidaya 16:35kusan 1471 K.H.

    Sai wuta ta fito daga wurin Ubangiji ta cinye mutane 250 da suke miƙa hadaya da turare.