Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Yohanna 6:63kusan 32 M.

    Ruhu ne yake ba da rai; jikin kam, ba ya amfana kome. Kalmomin da na faɗa muku, Ruhu ne, da kuma rai.

  2. Yohanna 6:64kusan 32 M.

    Duk da haka akwai waɗansunku da ba su gaskata ba.” Gama Yesu ya sani tun farko, waɗanda ba su gaskata ba, da kuma wanda zai bashe shi.

  3. Yohanna 6:65kusan 32 M.

    Ya ci gaba da cewa, “Shi ya sa na faɗa muku cewa ba mai iya zuwa wurina, sai dai Uba ya yardar masa.”

  4. Yohanna 6:66kusan 32 M.

    Daga wannan lokaci da yawa daga cikin almajiransa suka ja da baya, suka daina bin sa.

  5. Yohanna 6:67kusan 32 M.

    Sai Yesu ya tambayi Sha Biyun, “Ku ma za ku tafi ne?”

  6. Yohanna 6:68kusan 32 M.

    Sai Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Ubangiji wajen wa za mu tafi? Kai ne da kalmomin rai madawwami.

  7. Yohanna 6:69kusan 32 M.

    Mun gaskata mun kuma san cewa kai ne Mai Tsarkin nan na Allah.”

  8. Yohanna 6:70kusan 32 M.

    Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ba ni na zaɓe ku Sha Biyu ba? Amma ɗayanku Iblis ne!”

  9. Yohanna 6:71kusan 32 M.

    (Yana nufin Yahuda, ɗan Siman Iskariyot, wanda, ko da yake ɗaya ne cikin Sha Biyun, zai bashe shi daga baya.)

  10. Yohanna 7:1kusan 33 M.

    Bayan wannan, sai Yesu ya yi ta zagawa a cikin Galili, da ganga bai yarda yă je Yahudiya ba domin Yahudawa a can suna nema su kashe shi.

  11. Yohanna 7:2kusan 33 M.

    Amma sa’ad da Bikin Tabanakul na Yahudawa ya yi kusa,

  12. Yohanna 7:3kusan 33 M.

    sai ’yan’uwan Yesu suka ce masa, “Ya kamata ka bar nan ka tafi Yahudiya, don almajiranka su ga ayyukan banmamaki da kake yi.

  13. Yohanna 7:4kusan 33 M.

    Ba wanda yake so a san shi da zai yi abu a ɓoye. Da yake kana yin waɗannan abubuwa, sai ka nuna kanka ga duniya.”

  14. Yohanna 7:5kusan 33 M.

    Domin ko ’yan’uwansa ma ba su gaskata da shi ba.

  15. Yohanna 7:6kusan 33 M.

    Saboda haka Yesu ya ce musu, “Lokacina bai yi ba tukuna; amma a gare ku kowane lokaci daidai ne.

  16. Yohanna 7:7kusan 33 M.

    Duniya ba za tă iya ƙinku ba, amma ni take ƙi domin ina shaida cewa ayyukanta mugaye ne.

  17. Yohanna 7:8kusan 33 M.

    Ku ku tafi Bikin, ba zan haura zuwa wannan Bikin ba yanzu, domin lokacina bai yi ba tukuna.”

  18. Yohanna 7:9kusan 33 M.

    Da ya faɗa haka, sai ya dakata a Galili.

  19. Yohanna 7:10kusan 33 M.

    Amma fa, bayan ’yan’uwansa suka tafi Bikin, shi ma ya tafi, ba a fili ba, amma a ɓoye.

  20. Yohanna 7:11kusan 33 M.

    A Bikin kuwa, Yahudawa suka yi ta nemansa, suna cewa, “Ina mutumin yake?”

  21. Yohanna 7:12kusan 33 M.

    A cikin taron kuwa aka yi ta raɗe-raɗe game da shi. Waɗansu suka ce, “Shi mutumin kirki ne.” Waɗansu kuwa suka ce, “A’a, ai, ruɗin mutane yake.”

  22. Yohanna 7:13kusan 33 M.

    Amma ba wanda ya ce kome a fili game da shi don tsoron Yahudawa.

  23. Yohanna 7:14kusan 33 M.

    Sai bayan da aka kai tsakiyar Bikin, sa’an nan Yesu ya haura zuwa filin haikali ya fara koyarwa.

  24. Yohanna 7:15kusan 33 M.

    Yahudawa suka yi mamaki suna tambaya, “Yaya wannan mutum ya sami wannan sani haka ba tare da ya yi wani karatu ba?”

  25. Yohanna 7:16kusan 33 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “Koyarwata ba tawa ba ce, ta fito ne daga wurin wanda ya aiko ni.