Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ishaya 48:16kusan 712 K.H.

    “Ku zo kusa da ni ku kuma saurari wannan. “Daga farkon shela ban yi magana a ɓoye ba; a lokacin da ya faru, ina nan a wurin.” Yanzu kuwa Ubangiji Mai Iko Duka ya aiko ni, da Ruhunsa.

  2. Ishaya 48:17kusan 712 K.H.

    Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansarku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya ce, “Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya koya muku abin da ya fi muku kyau, wanda ya muku hanyar da za ku bi.

  3. Ishaya 48:18kusan 712 K.H.

    Da a ce kawai za ku mai da hankali ga umarnaina, da salamarku ta zama kamar kogi, adalcinku kamar raƙuman teku.

  4. Ishaya 48:19kusan 712 K.H.

    Da zuriyarku ta zama kamar yashi, ’ya’yanku kamar tsabar hatsin da ba a iya ƙidayawa; da ba za a taɓa yanke sunansu balle a hallaka su daga gabana ba.”

  5. Ishaya 48:20kusan 712 K.H.

    Ku bar Babilon, ku gudu daga Babiloniyawa! Ku yi shelar wannan da sowa ta farin ciki ku kuma furta shi. Ku aika shi zuwa iyakokin duniya; ku ce, “Ubangiji ya fanshi bawansa Yaƙub.”

  6. Ishaya 48:21kusan 712 K.H.

    Ba su ji ƙishi ba sa’ad da ya bishe su a cikin hamada; ya sa ruwa ya malalo dominsu daga dutse; ya tsage dutse ruwa kuwa ya kwararo.

  7. Ishaya 48:22kusan 712 K.H.

    “Babu salama ga mugaye” in ji Ubangiji.

  8. Ishaya 49:1kusan 712 K.H.

    Ku kasa kunne gare ni, ku tsibirai; ku ji wannan, ku al’ummai masu nesa. Kafin a haife Ni Ubangiji ya kira ni; tun daga haihuwata ya ambaci sunana.

  9. Ishaya 49:2kusan 712 K.H.

    Ya yi bakina kamar takobi mai kaifi, cikin inuwar hannunsa ya ɓoye ni; ya sa na zama kamar kibiya mai tsini ya kuma ɓoye ni cikin kwarinsa.

  10. Ishaya 49:3kusan 712 K.H.

    Ya ce mini, “Kai bawana ne, Isra’ila, a cikinka zan bayyana darajata.”

  11. Ishaya 49:4kusan 712 K.H.

    Amma na ce, “Na yi aiki a banza; na kashe duk ƙarfina a banza da wofi. Duk da haka abin da yake nawa yana a hannun Ubangiji, ladana kuma tana a wurin Allahna.”

  12. Ishaya 49:5kusan 712 K.H.

    Yanzu fa Ubangiji ya ce ya siffanta ni a cikin mahaifa don in zama bawansa don in dawo da Yaƙub gare shi in kuma tattara Isra’ila gare shi, gama an girmama ni a gaban Ubangiji Allahna kuma ne ƙarfina

  13. Ishaya 49:6kusan 712 K.H.

    ya ce, “Ɗan ƙaramin abu ne ka zama bawana don ka maido da kabilar Yaƙub ka kuma dawo da waɗannan na Isra’ilawan da na kiyaye. Zan kuma mai da kai haske ga Al’ummai, don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.”

  14. Ishaya 49:7kusan 712 K.H.

    Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansa da kuma Mai Tsarkin nan na Isra’ila gare shi wanda al’ummai suka rena suka kuma ki, ga bawan masu mulki. “Sarakuna za su gan ka su kuma miƙe tsaye, sarakuna za su gani su kuma rusuna, saboda Ubangiji, wanda yake mai aminci, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, wanda ya zaɓe ka.”

  15. Ishaya 49:8kusan 712 K.H.

    Ga abin da Ubangiji yana cewa, “A lokacin tagomashina zan amsa muku, kuma a ranar ceto zan taimake ku; zan kiyaye ku zan kuma sa ku zama alkawari ga mutane, don ku maido da ƙasa ku kuma sāke raba gādon kufai,

  16. Ishaya 49:9kusan 712 K.H.

    don ku ce wa waɗanda suke cikin kurkuku, ‘Ku fito,’ ga waɗanda suke cikin duhu kuma, ‘Ku ’yantu!’ “Za su yi kiwo kusa da hanyoyi su kuma sami wurin kiwo a kowane tudu.

  17. Ishaya 49:10kusan 712 K.H.

    Ba za su taɓa jin yunwa ko ƙishi ba, ba kuwa zafin hamada ko rana ta buge su ba. Shi da ya yi musu jinƙai zai jagorance su ya kuma bishe su kusa da maɓulɓulan ruwa.

  18. Ishaya 49:11kusan 712 K.H.

    Zan mayar da dukan duwatsu su zama hanyoyi, a kuma gyara manyan hanyoyina.

  19. Ishaya 49:12kusan 712 K.H.

    Duba, za su zo daga nesa waɗansu daga arewa, waɗansu daga yamma, waɗansu daga yankin Aswan.”

  20. Ishaya 49:13kusan 712 K.H.

    Ku yi sowa don farin ciki, ya ku sammai; ki yi farin ciki, ya ke duniya; ku ɓarke da waƙa, ya ku duwatsu! Gama Ubangiji ya ta’azantar da mutanensa zai kuma ji tausayin mutanensa da suke shan wahala.

  21. Ishaya 49:14kusan 712 K.H.

    Amma Sihiyona ta ce, “Ubangiji ya yashe ni, Ubangiji ya manta da ni.”

  22. Ishaya 49:15kusan 712 K.H.

    “Yana yiwuwa mahaifiya ta manta da jariri a ƙirjinta ta kuma kāsa nuna tausayi ga yaron da ta haifa? Mai yiwuwa ta manta, amma ba zan taɓa manta da ke ba!

  23. Ishaya 49:16kusan 712 K.H.

    Duba, na zāna ki a tafin hannuwana; katangarki kullum suna a gabana.

  24. Ishaya 49:17kusan 712 K.H.

    ’Ya’yanki maza su komo da gaggawa, waɗanda suka lalatar da ke kuwa za su bar ki.

  25. Ishaya 49:18kusan 712 K.H.

    Ki ɗaga idanunki ki duba kewaye; dukan ’ya’yanki sun taru suka kuma dawo gare ki. Muddin ina raye,” in ji Ubangiji, “Za ki yafa su duka kamar kayan ado; za ki yi ado da su, kamar amarya.