Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ishaya 47:6kusan 712 K.H.

    Na yi fushi da mutanena na ƙazantar da gādona; na ba su ga hannunki, ba ki kuwa nuna musu jinƙai ba. Har ma da tsofaffi kin jibga musu kaya masu nauyi sosai.

  2. Ishaya 47:7kusan 712 K.H.

    Kika ce, ‘Zan ci gaba har abada, madawwamiyar sarauniya!’ Amma ba ki lura da waɗannan abubuwa ko ki yi la’akari a kan abin da zai faru ba.

  3. Ishaya 47:8kusan 712 K.H.

    “To, yanzu fa, ki kasa kunne, ke mai ƙaunar nishaɗi, mai zama da rai kwance kina kuma ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni. Ba zan taɓa zama gwauruwa ko in sha wahalar rashin ’ya’ya ba.’

  4. Ishaya 47:9kusan 712 K.H.

    Duk waɗannan za su sha kanki cikin farat ɗaya, a rana guda, rashin ’ya’ya da gwauranci. Za su zo a kanki da cikakken minzani, duk da yawan masu dubanki da kuma dukan sihirinki.

  5. Ishaya 47:10kusan 712 K.H.

    Kin dogara a muguntarki kika kuma ce, ‘Babu wanda ya gan ni.’ Hikimarki da saninki sun ɓad da ke sa’ad da kika ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni.’

  6. Ishaya 47:11kusan 712 K.H.

    Bala’i zai fāɗo a kanki, kuma ba za ki san yadda za ki rinjaye shi yă janye ba. Masifa za tă fāɗo a kanki da ba za ki iya tsai da ita da kuɗin fansa ba; lalacewar da ba ki taɓa mafarkinta ba za tă auko miki nan da nan.

  7. Ishaya 47:12kusan 712 K.H.

    “Ki dai ci gaba, da sihirinki da kuma makarunki masu yawa, waɗanda kika yi ta wahala tun kina jaririya. Mai yiwuwa ki yi nasara, mai yiwuwa ki jawo fargaba.

  8. Ishaya 47:13kusan 712 K.H.

    Dukan shawarwarin da kika samu sun dai gajiyar da ke ne kawai! Bari masananki na taurari su zo gaba, waɗannan masu zāna taswirar sammai suna kuma faɗa miki dukan abin da zai faru da ke wata-wata, bari su cece ki daga abin da zai faru da ke.

  9. Ishaya 47:14kusan 712 K.H.

    Tabbas suna kama da bunnu; wuta za tă cinye su ƙaf. Ba za su ma iya ceton kansu daga ikon wutar ba. Ba wutar da wani zai ji ɗumi; ba wutar da za a zauna kusa da ita.

  10. Ishaya 47:15kusan 712 K.H.

    Abin da za su iya yi miki ke nan kawai, waɗannan da kika yi ta fama da su kika kuma yi ciniki da su tun kina jaririya. Kowannensu zai tafi cikin kuskurensa; babu ko ɗayan da zai cece ki.

  11. Ishaya 48:1kusan 712 K.H.

    “Ku kasa kunne ga wannan, ya gidan Yaƙub, waɗanda ake kira da sunan Isra’ila suka kuma fito daga zuriyar Yahuda, ku da kuke yin rantsuwa da sunan Ubangiji kuna kuma kira sunan Allah na Isra’ila, amma ba da gaskiya ko adalci ba,

  12. Ishaya 48:2kusan 712 K.H.

    ku da kuke kiran kanku ’yan ƙasar birni mai tsarki kuna kuma dogara ga Allah na Isra’ila, Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa,

  13. Ishaya 48:3kusan 712 K.H.

    na nanata abubuwan da suka riga suka faru tuntuni, bakina ya yi shelar su na kuma sanar da su; sai nan da nan na aikata, suka kuma faru.

  14. Ishaya 48:4kusan 712 K.H.

    Gama na san yadda kuke da taurinkai; jijiyoyin wuyanku ƙarafa ne, goshinku tagulla ne.

  15. Ishaya 48:5kusan 712 K.H.

    Saboda haka na faɗa waɗannan abubuwa tuntuni; kafin su faru na yi shelarsu gare ku saboda kada ku ce, ‘Gumakana ne suka yi su; siffar itacena da allahn zinariyana ne ya ƙaddara su.’

  16. Ishaya 48:6kusan 712 K.H.

    Kun riga kun ji waɗannan abubuwa; kuka gan su duka. Ba za ku yarda da su ba? “Daga yanzu zuwa gaba zan faɗa muku sababbin abubuwa, na ɓoyayyun abubuwan da ba ku sani ba.

  17. Ishaya 48:7kusan 712 K.H.

    Yanzu an halicce su, ba da daɗewa ba; ba ku riga kun ji game da su kafin yau ba. Saboda haka ba za ku ce, ‘I, na san da su ba.’

  18. Ishaya 48:8kusan 712 K.H.

    Ba ku ji ko balle ku gane ba; tun da kunnenku bai buɗu ba. Tabbatacce na san yadda kun zama masu tayarwa; an kira ku ’yan tawaye daga haihuwa.

  19. Ishaya 48:9kusan 712 K.H.

    Saboda girman sunana na jinkirta fushina; saboda girman yabona na janye shi daga gare ku, don dai kada a yanke ku.

  20. Ishaya 48:10kusan 712 K.H.

    Duba, na tace ku, ko da yake ba kamar azurfa ba; na gwada ku cikin wutar wahala.

  21. Ishaya 48:11kusan 712 K.H.

    Saboda girmana, saboda girmana, na yi haka. Yaya zan ƙyale a ƙazantar da kaina? Ba zan raba ɗaukakata da wani ba.

  22. Ishaya 48:12kusan 712 K.H.

    “Ka kasa kunne gare ni, ya Yaƙub, Isra’ila, wanda na kira cewa, Ni ne shi; ni ne na farko ni ne kuma na ƙarshe.

  23. Ishaya 48:13kusan 712 K.H.

    Hannuna ne ya kafa harsashen duniya, hannuna na dama kuma ya shimfiɗa sammai; sa’ad da na kira su, duka suka miƙe tsaye gaba ɗaya.

  24. Ishaya 48:14kusan 712 K.H.

    “Ku tattaru, dukanku ku kuma saurara, Wanne a cikin gumakan ya iya faɗa waɗannan abubuwa? Zaɓaɓɓen da Ubangiji yake ƙauna zai aikata nufinsa a kan Babilon; hannunsa zai yi gāba da Babiloniyawa.

  25. Ishaya 48:15kusan 712 K.H.

    Ni kaina, na faɗa; I, na kira shi. Zan kawo shi, zai kuma yi nasara a cikin aikinsa.