- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 800–400 BC
The Hebrew Prophets
God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ishaya 44:22kusan 712 K.H.
Na shafe laifofinka kamar girgije, zunubanka kamar hazon safe. Ka komo wurina, gama na kuɓutar da kai.”
- Ishaya 44:23kusan 712 K.H.
Ku rera don farin ciki, ya sammai, gama Ubangiji ya aikata wannan; ku yi sowa, ya duniya a ƙarƙashi. Ku ɓarke da waƙoƙi, ku duwatsu, ku jeji da dukan itatuwanku, gama Ubangiji ya kuɓutar da Yaƙub, ya nuna ɗaukakarsa a cikin Isra’ila.
- Ishaya 44:24kusan 712 K.H.
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansarka, wanda ya yi ka a cikin mahaifa. “Ni ne Ubangiji, wanda ya yi dukan abubuwa, wanda ya shimfiɗa sammai ya kuma kafa harsashen duniya da kansa,
- Ishaya 44:25kusan 712 K.H.
wanda ya sassāke alamun annabawan ƙarya ya masu duba suka zama wawaye, wanda ya tumɓuke koyon masu hikima ya mai da shi banza,
- Ishaya 44:26kusan 712 K.H.
wanda ya tabbatar da maganganun bayinsa ya kuma cika annabce-annabcen ’yan aikansa, “wanda ya ce game da Urushalima, ‘Za a zauna a cikinta,’ game da garuruwan Yahuda, ‘Za a gina su,’
- Ishaya 44:27kusan 712 K.H.
wanda ya ce wa zurfin ruwaye, ‘Ku bushe, zan kuma busar da rafuffukanku,’
- Ishaya 44:28kusan 712 K.H.
wanda ya yi zancen Sairus ya ce, ‘Shi ne makiyayina zan kuma cika dukan abin da na gan dama; zai yi zancen Urushalima cewa, “Bari a sāke gina ta,” game da haikali kuma cewa, “Bari a kafa harsashinsa.” ’
- Ishaya 45:1kusan 712 K.H.
“Ga abin da Ubangiji ya faɗa wa shafaffensa, ga Sairus, wanda hannun damansa yana riƙe da shi don yă ci al’ummai a gabansa ya kuma tuɓe makaman sarakuna, don yă buɗe ƙofofi a gabansa don kada a kulle ƙofofi.
- Ishaya 45:2kusan 712 K.H.
Zan sha gabanka in baje duwatsu; zan farfashe ƙofofin tagulla in kuma kakkarye ƙyamaren ƙarfe.
- Ishaya 45:3kusan 712 K.H.
Zan ba ka dukiyar duhu, arzikin da aka ajiye a asirtattun wurare, saboda ka san cewa ni ne Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya kira ka da suna.
- Ishaya 45:4kusan 712 K.H.
Saboda sunan Yaƙub bawana, Isra’ila zaɓaɓɓena, na kira ka da suna na ba ka matsayin bangirma, ko da yake ba ka san ni ba.
- Ishaya 45:5kusan 712 K.H.
Ni ne Ubangiji, kuma babu wani; in ban da ni babu wani Allah. Zan ƙarfafa ka, ko da yake ba ka san ni ba,
- Ishaya 45:6kusan 712 K.H.
saboda daga fitowar rana har zuwa fāɗuwarta mutane za su san cewa babu wani in ban da ni. Ni ne Ubangiji, kuma babu wani.
- Ishaya 45:7kusan 712 K.H.
Ni ne na siffanta haske na kuma halicci duhu, ni ne nake ba da nasara in kuma jawo bala’i; ni, Ubangiji ne ke aikata dukan waɗannan abubuwa.
- Ishaya 45:8kusan 712 K.H.
“Ku sammai, ku sauko da adalci kamar ruwan sama; bari gizagizai su zubar da yayyafi kamar adalci. Bari ƙasa ta buɗe, bari ceto ya tsiro, bari adalci ya yi girma tare da shi; ni, Ubangijine, na sa ya faru.
- Ishaya 45:9kusan 712 K.H.
“Kaitonka mai gardama da Wanda ya yi ka, da wanda yake kasko a cikin kasko a ƙasa. Yumɓu ya iya ce wa magini, ‘Me kake yi?’ Aikinka na iya cewa, ‘Ba shi da hannuwa’?
- Ishaya 45:10kusan 712 K.H.
Kaiton wanda yake cewa mahaifinsa, ‘Me ka manta?’ Ko kuwa ga mahaifiyarsa, ‘Me kin haifa?’
- Ishaya 45:11kusan 712 K.H.
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, da kuma Mahaliccinsa. Game da abubuwan da ke zuwa, kun tambaye ni game da ’ya’yana, ko kuwa kun ba ni umarni game da aikin hannuwana?
- Ishaya 45:12kusan 712 K.H.
Ai, ni ne wanda ya yi duniya na kuma halicci mutum a kanta. Hannuwana ne sun miƙe sammai; na umarci rundunar sararin sama.
- Ishaya 45:13kusan 712 K.H.
Zan tā da Sairus cikin adalcina. Zan sa dukan hanyoyinsa su miƙe. Zai sāke gina birnina ya kuma ’yantar da mutanena masu bautar talala, amma ba don wata haya ko lada ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki.”
- Ishaya 45:14kusan 712 K.H.
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kayayyakin Masar da hajar Kush, da waɗannan dogayen Sabenawa, za su ƙetaro zuwa wurinku za su kuma zama naku; za su bi bayanku, suna zuwa cikin sarƙoƙi. Za su rusuna a gabanku su roƙe ku, suna cewa, ‘Tabbas Allah yana tare da ku, babu kuma wani; babu wani allah.’ ”
- Ishaya 45:15kusan 712 K.H.
Tabbatacce kai ne Allah wanda ya ɓoye kanka, Ya Allah da Mai Ceton Isra’ila.
- Ishaya 45:16kusan 712 K.H.
Dukan masu yin gumaka za su sha kunya; za su fita da kunya gaba ɗaya.
- Ishaya 45:17kusan 712 K.H.
Amma Ubangiji zai ceci Isra’ila da madawwamin ceto; ba za ku sāke shan kunya ko ƙasƙanci ba, har abada.
- Ishaya 45:18kusan 712 K.H.
Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya halicci sammai, shi ne Allah; shi da ya sarrafa ya kuma yi duniya, ya kafa ta; bai halicce ta don ta zama ba kome ba, amma ya yi ta don a zauna a ciki, ya ce, “Ni ne Ubangiji, kuma babu wani.