- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 800–400 BC
The Hebrew Prophets
God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ishaya 49:19kusan 712 K.H.
“Ko da yake an lalatar da ke aka kuma mai da ke kufai ƙasarki kuma ta zama kango, yanzu za ki kāsa sosai saboda yawan mutanenki, kuma waɗanda suka cinye ki za su kasance can da nisa.
- Ishaya 49:20kusan 712 K.H.
’Ya’yan da aka haifa a lokacin baƙin cikinki za su ce a kunnenki, ‘Wannan wuri ya yi mana kaɗan ƙwarai; ki ƙara mana wurin zama.’
- Ishaya 49:21kusan 712 K.H.
Sa’an nan za ki ce a zuciyarki, ‘Wa ya haifa waɗannan? Na yi baƙin ciki na kuma zama wadda ba ta haihuwa; an yi mini daurin talala aka kuma ƙi ni. Wane ne ya yi renon waɗannan? An bar ni ni kaɗai, amma waɗannan, ina suka fito?’ ”
- Ishaya 49:22kusan 712 K.H.
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Duba, zan yi alama wa Al’ummai, zan ɗaga tutana wa mutane; za su kawo ’ya’yanki maza a hannuwansu su riƙe ’ya’yanki mata a kafaɗunsu.
- Ishaya 49:23kusan 712 K.H.
Sarakuna za su zama kamar iyayen reno, sarauniyoyinsu kuma za su yi renonku kamar uwaye. Za su rusuna a gabanki da fuskokinsu har ƙasa; za su lashe ƙura a ƙafafunki. Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji; waɗanda suke sa zuciya gare ni ba za su sha kunya ba.”
- Ishaya 49:24kusan 712 K.H.
Za a iya ƙwace ganima daga jarumawa, ko a kuɓutar da kamammu daga hannun marasa tsoro?
- Ishaya 49:25kusan 712 K.H.
Amma ga abin da Ubangiji yana cewa, “I, za a ƙwace kamammu daga jarumawa, a kuma karɓe ganima daga hannun marasa tsoro; zan gwabza da waɗanda suke gwabzawa da ke, zan kuwa ceci ’ya’yanki.
- Ishaya 49:26kusan 712 K.H.
Zan sa masu zaluntarki su ci naman jikinsu; za su bugu da jininsu, sai ka ce sun sha ruwan inabi. Sa’an nan dukan mutane za su sani cewa ni, Ubangiji, ni ne Mai Cetonki, Mai Fansarki, Maɗaukakin nan na Yaƙub.”
- Ishaya 50:1kusan 712 K.H.
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ina takardar shaida na saki mahaifiyarka daga aure wadda na kora? Ko kuwa ga wanda mutumin da nake bin bashi ne na sayar da kai? Saboda zunubanka aka sayar da kai; saboda laifofinka ne ya sa aka kori mahaifiyarka.
- Ishaya 50:2kusan 712 K.H.
Sa’ad da na zo, me ya sa babu kowa? Sa’ad da na yi kira, me ya sa babu wani da ya amsa? Hannuna ya kāsa ne sosai don fansarka? Na rasa ƙarfin kuɓutar da kai ne? Ta wurin tsawatawa kawai na busar da teku, na mai da koguna hamada; kifayensu duk sun ruɓe saboda rashin ruwa suka kuma mutu saboda ƙishi.
- Ishaya 50:3kusan 712 K.H.
Na suturar da sararin sama da duhu na kuma mai da tsummoki abin rufuwarsa.”
- Ishaya 50:4kusan 712 K.H.
Ubangiji Mai Iko Duka ya ba ni harshen umarni, don in san maganar da za tă ƙarfafa gajiyayye. Ya farkar da ni da safe, ya farkar da kunnena don in saurara kamar wanda ake koya masa.
- Ishaya 50:5kusan 712 K.H.
Ubangiji Mai Iko Duka ya buɗe kunnuwana, kuma ban yi tayarwa ba; ban ja da baya ba.
- Ishaya 50:6kusan 712 K.H.
Na ba da bayana ga masu dūkana, kumatuna ga masu jan gemuna; ban ɓoye fuskata daga masu ba’a da masu tofa mini miyau ba.
- Ishaya 50:7kusan 712 K.H.
Gama Ubangiji Mai Iko Duka zai taimake ni, ba zan sha kunya ba. Saboda haka na kafa fuskata kamar dutsen ƙanƙara, na kuma sani ba zan sha kunya ba.
- Ishaya 50:8kusan 712 K.H.
Gama shi da zai tabbatar da ni, marar laifi ne yana kusa. Wane ne zai kawo ƙararraki game da ni? Bari mu je ɗakin shari’a tare! Wane ne mai zargina? Bari yă kalubalance ni!
- Ishaya 50:9kusan 712 K.H.
Ubangiji Mai Iko Duka ne zai taimake ni. Wane ne zai iya tabbatar da ni mai laifi? Duk za su koɗe kamar riga; asu za su cinye su.
- Ishaya 50:10kusan 712 K.H.
Wane ne a cikinku yake tsoron Ubangiji yana kuma yin biyayya ga maganar bawansa? Bari wanda yake tafiya cikin duhu, wanda ba shi da haske, ya dogara a sunan Ubangiji ya kuma dogara ga Allahnsa.
- Ishaya 50:11kusan 712 K.H.
Amma yanzu fa, dukanku waɗanda kuke ƙuna wuta kuna kuma tanada wa kanku fitilu masu ci, ku je ku yi tafiya a cikin hasken wutarku da na fitilun da kuka ƙuna. Abin da za ku karɓa ke nan daga hannuna. Za ku kwanta a cikin azaba.
- Ishaya 51:1kusan 712 K.H.
“Ku kasa kunne gare ni, ku da kuna neman adalci kuke kuma neman Ubangiji. Dubi dutse daga inda aka yanke ku da kuma mahaƙar duwatsu inda aka fafe ku;
- Ishaya 51:2kusan 712 K.H.
dubi Ibrahim, mahaifinku, da Saratu, wadda ta haife ku. Sa’ad da na kira shi kaɗai ne, na kuma albarkace shi na kuma mai da shi da yawa.
- Ishaya 51:3kusan 712 K.H.
Tabbatacce Ubangiji zai ta’azantar da Sihiyona zai kuma duba da tausayi a kan dukan kufanta; zai sa hamadanta ta zama kamar Eden, ƙeƙasasshiyar ƙasarta kamar lambun Ubangiji. Za a sami farin ciki da murna a cikinta, godiya da ƙarar rerawa.
- Ishaya 51:4kusan 712 K.H.
“Ku kasa kunne gare ni, mutanena; ku ji ni, al’ummata. Doka za tă fito daga gare ni; shari’ata za tă zama haske ga al’ummai.
- Ishaya 51:5kusan 712 K.H.
Adalcina na zuwa da sauri, cetona yana a kan hanya, hannuna kuma zai kawo adalci ga al’ummai. Tsibirai za su dube ni su kuma jira da sa zuciya don hannuna.
- Ishaya 51:6kusan 712 K.H.
Ku daga idanunku zuwa sammai ku dubi duniya a ƙasa; sammai za su ɓace kamar hayaƙi, duniya za tă shuɗe kamar riga mazaunanta kuma su mutu kamar ƙudaje. Amma cetona zai dawwama har abada, adalcina ba zai taɓa kāsa ba.