Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ishaya 28:16kusan 725 K.H.

    Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Duba, na kafa dutse a Sihiyona, dutsen da aka gwada, dutsen kusurwa mai daraja don tabbataccen tushe; wanda ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.

  2. Ishaya 28:17kusan 725 K.H.

    Zan mai da gaskiya igiyar gwaji adalci kuma ɗan katakon gwajin ginin; ƙanƙara za tă share mafakarku, ƙarya, da ruwa kuma za su mamaye maɓuyanku.

  3. Ishaya 28:18kusan 725 K.H.

    Za a soke alkawarinku da mutuwa; yarjejjeniyarku da kabari ba zai zaunu ba. Sa’ad da zafi mai ɓarna ya ratsa, zai hallaka ku.

  4. Ishaya 28:19kusan 725 K.H.

    A duk sa’ad da ya zo; ko da safiya, ko dare ko kuma da rana, zai yi ta ratsawa yana kwasanku.” Za ku zama kamar mutumin da ya zama abin karin magana,

  5. Ishaya 28:20kusan 725 K.H.

    wanda ya yi ƙoƙari yă kwanta a gajeren gado, yă kuma rufa da ɗan siririn bargo.

  6. Ishaya 28:21kusan 725 K.H.

    Ubangiji zai tashi kamar yadda ya yi a Dutsen Feratsim, zai tā da kansa kamar a Kwarin Gibeyon don yă aikata aikinsa, aikinsa da ba a saba gani ba, yă kuma yi aikinsa, baƙon aikinsa.

  7. Ishaya 28:22kusan 725 K.H.

    Yanzu ku daina ba’arku, in ba haka ba sarƙoƙinku za su ƙara nauyi; Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, ya faɗa mini game da hallakar da aka ƙaddara a kan dukan ƙasar.

  8. Ishaya 28:23kusan 725 K.H.

    Ku saurara ku kuma ji muryata; ku kasa kunne ku kuma ji abin da na faɗa.

  9. Ishaya 28:24kusan 725 K.H.

    Sa’ad da manomi ya yi noma don shuki, yakan ci gaba da noma ne? Yakan ci gaba da sara yana yin kunyoyi a ƙasa ne?

  10. Ishaya 28:25kusan 725 K.H.

    Sa’ad da ya shirya wuri da kyau, ba yakan shuka kanumfari ya kuma yayyafa ɗaɗɗoya ba? Ba yakan shuka alkama a kunyoyinsa sha’ir a kunyoyinsa, tamba kuma a filinsa ba?

  11. Ishaya 28:26kusan 725 K.H.

    Allahnsa ya umarce shi ya kuma koya masa hanyar da take daidai.

  12. Ishaya 28:27kusan 725 K.H.

    Ba a bugan kanumfari da ƙaton sanda ko a yi ta jujjuye ƙafar keke a kan ɗaɗɗoya; akan buga kanumfari da siririn sanda ɗaɗɗoya kuma da tsumagiya.

  13. Ishaya 28:28kusan 725 K.H.

    Dole a niƙa hatsi don a yi burodi; saboda haka mutum ba zai yi ta bugun alkama, har yă ɓata tsabar ba. Ya san yadda zai sussuke alkamarsa, ba tare da ya ɓata tsabarta ba.

  14. Ishaya 28:29kusan 725 K.H.

    Dukan wannan hikimar takan zo daga Ubangiji Maɗaukaki ne, shi da yake mashawarci mai banmamaki, mafifici kuma cikin hikima.

  15. Ishaya 29:1kusan 712 K.H.

    Kaitonki, Ariyel, Ariyel birnin da Dawuda ya zauna! Ƙara shekara ga shekara a kuma bar shagulgulanki su yi ta kewayewa.

  16. Ishaya 29:2kusan 712 K.H.

    Duk da haka zan yi wa Ariyel kwanto za tă kuma yi kuka da makoki, za tă zama mini kamar bagaden jini.

  17. Ishaya 29:3kusan 712 K.H.

    Zan kafa sansani kewaye da ke duka; zan kewaye ki da hasumiyoyi in tasar miki da ayyukan kwantona na yaƙi.

  18. Ishaya 29:4kusan 712 K.H.

    Za a ƙasƙantar da ke, za ki ƙi yin magana daga ƙasa; maganarki za tă yi ƙasa-ƙasa daga ƙura. Muryarki za tă zama kamar fatalwa daga ƙasa; daga ƙura maganarki zai fito ƙasa-ƙasa.

  19. Ishaya 29:5kusan 712 K.H.

    Amma abokan gābanki masu yawa za su zama kamar ƙura mai laushi, sojojinsu masu firgitarwa za su yi ta tashi kamar yayin da iska ta hura. Farat ɗaya, cikin ɗan lokaci,

  20. Ishaya 29:6kusan 712 K.H.

    Ubangiji Maɗaukaki zai zo da tsawa da rawar ƙasa da ƙara mai girma, da hadarin iska da guguwa da harshe na wuta mai ci.

  21. Ishaya 29:7kusan 712 K.H.

    Sa’an nan sojojin dukan al’umman da suka yi yaƙi da Ariyel, da suka fāɗa mata da kagararta suka kuma yi mata kwanto, za su zama kamar yadda yake da mafarki, wahayi da dare,

  22. Ishaya 29:8kusan 712 K.H.

    kamar sa’ad da mai yunwa yana mafarki cewa yana cin abinci, amma sai ya farka, yunwan tana nan; kamar sa’ad da mai ƙishirwa yana mafarki cewa yana shan ruwa, amma sai ya farka yana suma, da ƙishinsa. Haka zai zama da sojoji na dukan al’ummai da suka yi yaƙi da Dutsen Sihiyona.

  23. Ishaya 29:9kusan 712 K.H.

    Ku firgita ku kuma yi mamaki, ku makance kanku ku kuma zama a makance; ku bugu, amma ba da ruwan inabi ba, ku yi tangaɗi, amma ba daga barasa ba.

  24. Ishaya 29:10kusan 712 K.H.

    Ubangiji ya kawo muku barci mai nauyi, Ya rufe idanunku (annabawa); ya rufe kawunanku (masu duba).

  25. Ishaya 29:11kusan 712 K.H.

    Gare ku duk wannan wahayi ba kome ba ne sai dai maganganun da aka rufe a cikin littafi. In kuma kun ba da littafin ga wani wanda zai iya karanta, kuka kuma ce masa, “Karanta wannan, muna roƙonka,” zai amsa ya ce, “Ba zan iya ba; an rufe shi.”