Tsallake zuwa abun ciki

circa 605–538 BC

The Babylonian Exile

Jerusalem falls and the temple burns; Ezekiel and Daniel minister among the exiles as Lamentations mourns the city's ruin.

1,784 ayoyi · 3 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Daniyel 5:12kusan 538 K.H.

    Wannan mutum Daniyel, wanda sarki ya kira Belteshazar, an gane yana da ruhu nagari, da ilimi, da ganewa don yin fassarar mafarkai, da bayyana ma’anar kacici-kacici, da warware al’amura masu wuya. Ka kira Daniyel shi kuwa zai faɗa maka abin da rubutun nan yake nufi.”

  2. Daniyel 5:13kusan 538 K.H.

    Saboda haka aka kawo Daniyel a gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Kai ne Daniyel ɗin nan, ɗaya daga cikin kamammu waɗanda mahaifina sarki ya kawo daga Yahuda?

  3. Daniyel 5:14kusan 538 K.H.

    Na sami labari cewa kana da ruhun alloli a cikinka da kuma basira, da hazaka da kuma fitacciyar hikima.

  4. Daniyel 5:15kusan 538 K.H.

    An kawo masu hikima da masu dabo a gabana domin su karanta wannan rubutu su kuma faɗa mini abin da yake nufi, amma ba su iya ba.

  5. Daniyel 5:16kusan 538 K.H.

    Na sami labari cewa kana iya ba da fassara da kuma warware matsaloli masu wuya. In har ka iya karanta wannan rubutun ka kuma faɗa mini abin da yake nufi, za a sa maka riga shunayya, a kuma sa sarƙar zinariya a wuyanka. Za ka zama na uku a cikin masu mulkin ƙasar.”

  6. Daniyel 5:17kusan 538 K.H.

    Sai Daniyel ya amsa wa sarki ya ce, “Za ka iya ajiye kyautar wa kanka ko kuma ka ba wa wani. Duk da haka, zan karanta wa sarki rubutun, in kuma faɗa abin da yake nufi.

  7. Daniyel 5:18kusan 538 K.H.

    “Ya sarki, Allah Mafi Ɗaukaka ya ba mahaifinka Nebukadnezzar sarauta, da girma, da ɗaukaka, da martaba.

  8. Daniyel 5:19kusan 538 K.H.

    Saboda irin matsayin da ya ba shi, dukan mutane da al’ummai da kuma dukan harsuna suka ji tsoronsa suka yi rawar jiki a gabansa. Bisa ga ganin damarsa yakan kashe wani, ya bar wani da rai, haka kuma yakan ɗaukaka wani, ya ƙasƙantar da wani.

  9. Daniyel 5:20kusan 538 K.H.

    Amma da lokacin da zuciyarsa ta cika da girman kai ta kuma taurare, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa.

  10. Daniyel 5:21kusan 538 K.H.

    Aka kore shi daga cikin mutane aka kuma ba shi tunani irin na dabba; ya yi zama tare da jakunan jeji, ya kuma ci ciyawa kamar shanu; jikinsa kuma ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.

  11. Daniyel 5:22kusan 538 K.H.

    “Amma kai ɗansa, Ya Belshazar, ba ka ƙasƙantar da kanka ba, ko da yake ka san wannan duka.

  12. Daniyel 5:23kusan 538 K.H.

    A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.

  13. Daniyel 5:24kusan 538 K.H.

    Saboda haka ya aiko da hannun da ya yi rubutun nan.

  14. Daniyel 5:25kusan 538 K.H.

    “Wannan shi ne rubutun da aka yi, Mene, mene, tekel, farsin

  15. Daniyel 5:26kusan 538 K.H.

    “Abin da kalmomin nan suke nufi shi ne, “Mene, Allah ya ƙayyade yawan kwanakin mulkinka ya kuma kawo su ga ƙarshe.

  16. Daniyel 5:27kusan 538 K.H.

    “Tekel, An kuma auna ka a ma’auni aka tarar ka kāsa.

  17. Daniyel 5:28kusan 538 K.H.

    “Feres, An raba mulkinka aka ba wa Medes da Farisa.”

  18. Daniyel 5:29kusan 538 K.H.

    Sai Belshazar ya umarta, aka sa wa Daniyel riga mai shunayya, aka sa sarƙar zinariya a wuyansa, aka kuma yi shela, cewa yanzu shi ne na uku a cikin masu mulkin ƙasar.

  19. Daniyel 5:30kusan 538 K.H.

    A wannan dare aka kashe Belshazar, sarkin Babiloniyawa,

  20. Daniyel 5:31kusan 538 K.H.

    Dariyus mutumin Medes kuwa ya karɓi mulkin, yana da shekara sittin da biyu.

  21. Daniyel 6:1kusan 538 K.H.

    Ya gamshi Dariyus ya naɗa muƙaddasai 120 su yi shugabanci a duk fāɗin masarautar,

  22. Daniyel 6:2kusan 538 K.H.

    ya naɗa mutum uku a bisa waɗannan muƙaddasan, Daniyel yana ɗaya daga cikin mutum ukun nan. Sai aka sa muƙaddasan nan a ƙarƙashin waɗannan uku ɗin domin kada sarki ya yi hasarar kome.

  23. Daniyel 6:3kusan 538 K.H.

    To, Daniyel dai ya yi ficce a cikin shugabannin nan uku har da muƙaddasan ma, saboda waɗansu halaye nagari da yake da su, wanda ya sa sarki ya yi shiri ya ɗora shi a kan dukan mulkinsa.

  24. Daniyel 6:4kusan 538 K.H.

    A kan haka, shugabannin nan uku da muƙaddasan nan suka yi ƙoƙari su sami wani laifi a kan Daniyel a yadda yake tafiyar da aikin shugabancinsa, amma ba su samu ba. Ba su same shi da wani laifin cin hanci ba, domin shi amintacce ne kuma babu wani aibi a kansa ko rashin kula.

  25. Daniyel 6:5kusan 538 K.H.

    A ƙarshe waɗannan mutane suka ce; “Ba za mu taɓa samun wani laifin da za mu kama Daniyel da shi ba, sai dai ko abin ya shafi dokar Allahnsa.”