Tsallake zuwa abun ciki

circa 605–538 BC

The Babylonian Exile

Jerusalem falls and the temple burns; Ezekiel and Daniel minister among the exiles as Lamentations mourns the city's ruin.

1,784 ayoyi · 3 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ezekiyel 22:10kusan 593 K.H.

    A cikinki akwai waɗanda suke kwana da matan mahaifansu; a cikinki akwai waɗanda suke kwana da mata a lokacin da suke al’adarsu, sa’ad da suke da rashin tsarki.

  2. Ezekiyel 22:11kusan 593 K.H.

    A cikinki mutum guda yakan yi laifi abin ƙyama da matar maƙwabcinsa, wani cikin rashin kunya ya ƙazantar da matar ɗansa, wani kuma ya kwana da ’yar’uwansa, ’yar mahaifinsa.

  3. Ezekiyel 22:12kusan 593 K.H.

    A cikinki mutane suna karɓan cin hanci don su yi kisankai; kina ba da rance da ruwa da ƙari, kina kuma cin riba a kan maƙwabcinki ta wurin ƙwace. Kina kuma manta da ni, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  4. Ezekiyel 22:13kusan 593 K.H.

    “ ‘Tabbatacce zan tafa hannuwana a kan ƙazamar riba da kika ci da jinin da kin zubar a cikinki.

  5. Ezekiyel 22:14kusan 593 K.H.

    Ƙarfin halinki zai jure ko kuwa hannuwanki za su yi ƙarfi a ranar da na gamu da ke? Ni Ubangiji na faɗa, zan kuma aikata.

  6. Ezekiyel 22:15kusan 593 K.H.

    Zan watsar da ke cikin al’ummai in warwatsa ke cikin ƙasashe; zan kuma kawo ƙarshen rashin tsarkinki.

  7. Ezekiyel 22:16kusan 593 K.H.

    Sa’ad da ki ƙazantu a idanun al’umma, za ki san cewa ni ne Ubangiji.’ ”

  8. Ezekiyel 22:17kusan 593 K.H.

    Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  9. Ezekiyel 22:18kusan 593 K.H.

    “Ɗan mutum, gidan Isra’ila ta zama ƙwan maƙera a gare ni; dukansu tagulla ne, kuza, ƙarfe da darma da suka rage a tanderu. Su ƙwan maƙerar azurfa ne kawai.

  10. Ezekiyel 22:19kusan 593 K.H.

    Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin ku duka kun zama ƙwan maƙera, zan tattara ku a Urushalima.

  11. Ezekiyel 22:20kusan 593 K.H.

    Kamar yadda mutane sukan tattara azurfa, tagulla, ƙarfe, darma da kuza a cikin tanderu don su narkar da su da wuta, haka zan tattara ku cikin fushina da kuma hasalata in sa ku cikin birnin in narkar da ku.

  12. Ezekiyel 22:21kusan 593 K.H.

    Zan tattara ku zan kuma hura muku wutar hasalata, za ku kuma narke a cikinta.

  13. Ezekiyel 22:22kusan 593 K.H.

    Kamar yadda azurfa kan narke a tanderu, haka za ku narke a cikinta, kuma za ku san cewa Ni Ubangiji na zubo muku da zafin fushina.’ ”

  14. Ezekiyel 22:23kusan 593 K.H.

    Har yanzu maganar Ubangiji ta zo gare ni cewa,

  15. Ezekiyel 22:24kusan 593 K.H.

    “Ɗan mutum, ka faɗa wa ƙasar, ‘Ke ƙasa ce marar ruwan sama ko yayyafi a ranar hasala.’

  16. Ezekiyel 22:25kusan 593 K.H.

    Akwai haɗin bakin sarakunanki a cikinki kamar rurin zaki mai yayyage ganimarsa; suna cin mutane, suna kwashe dukiya da abubuwa masu daraja suna mai da yawanci gwauraye a cikinki.

  17. Ezekiyel 22:26kusan 593 K.H.

    Firistocinki suna karya dokokina, sun ƙazantar da tsarkakan abubuwana; ba sa bambanta tsakanin tsarki da marar tsarki; suna koyarwa cewa babu bambanci tsakanin marar tsarki da mai tsarki; suna kuma rufe idanunsu ga kiyaye Asabbataina, da haka suke saɓon sunana.

  18. Ezekiyel 22:27kusan 593 K.H.

    Shugabanninki a cikinki suna kama da kyarketai masu yayyage ganimarsu; suna kisa suna kuma kashe mutane don samun ƙazamar riba.

  19. Ezekiyel 22:28kusan 593 K.H.

    Annabawanki sun yi wa waɗannan ayyuka shafe da farar ƙasa ta wurin wahayin ƙarya da duban ƙarya. Suna cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa’ alhali kuwa Ubangiji bai faɗa ba.

  20. Ezekiyel 22:29kusan 593 K.H.

    Mutanen ƙasar na yin ƙwace suna yin fashi; suna cin zalin matalauta da mabukata suna wulaƙanta baƙo suna hana musu adalci.

  21. Ezekiyel 22:30kusan 593 K.H.

    “Na nemi mutum guda a cikinsu wanda zai gina katanga ya tsaya a gabana a tsakani a madadin ƙasar don kada in hallaka ta, amma ban sami ko ɗaya ba.

  22. Ezekiyel 22:31kusan 593 K.H.

    Saboda haka zan zuba hasalata a kansu in cinye su da wutar fushina, ina ɗora alhakin ayyukansu a bisa kawunansu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”

  23. Ezekiyel 23:1kusan 593 K.H.

    Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  24. Ezekiyel 23:2kusan 593 K.H.

    “Ɗan mutum, an yi mata biyu, ’yan matan mahaifiya guda.

  25. Ezekiyel 23:3kusan 593 K.H.

    Suka zama karuwai a Masar, suka yi karuwanci tun daga ƙuruciyarsu. A wancan ƙasar an rungumi mamansu da ƙirjinsu na budurwanci.