Tsallake zuwa abun ciki

Jerusalem

753 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Jerusalem's

31.7700, 35.2300 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Jerusalem

Tace bisa littafi
  1. A wannan lokaci, Hazayel sarkin Aram ya haura, ya kai wa Gat hari, ya kuma ci ta da yaƙi. Sa’an nan ya juya don yă yaƙi Urushalima.

  2. Amma Yowash sarkin Yahuda ya kwashe tsarkakan kayan da kakanninsa, Yehoshafat, Yehoram da Ahaziya, sarakunan Yahuda suka keɓe, da kyautai da shi kansa ya keɓe, da kuma dukan azurfan da aka samu a ɗakunan ajiya haikalin Ubangiji da na fada, ya aika da su wa Hazayel sarkin Aram, shi kuma ya janye daga Urushalima.

  3. Ya zama sarki yana da shekaru ashirin da biyar, ya kuma yi mulki a Urushalima shekaru ashirin da tara. Sunan mahaifiyarsa Yehoyaddin, mutuniyar Urushalima.

  4. Yehowash sarkin Isra’ila ya kama Amaziya sarkin Yahuda, ɗan Yowash, ɗan Ahaziya, a Bet-Shemesh. Sa’an nan Yehowash ya tafi Urushalima ya rushe katangar Urushalima daga Ƙofar Efraim har zuwa Ƙofar Kusurwa, ratarta ta kai wajen ƙafa ɗari shida.

  5. Suka ƙulla masa maƙarƙashiya a Urushalima, ya gudu zuwa Lakish, amma suka aika har Lakish aka kashe shi a can.

  6. Aka ɗauko shi a kan doki aka kawo shi Urushalima, aka kuwa binne shi tare da kakanninsa, a Birnin Dawuda.

  7. Yana da shekara goma sha shida sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyu. Sunan mahaifiyarsa Yekoliya daga Urushalima.

  8. Ya zama sarki yana da shekara ashirin da biyar, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Sunan mahaifiyarsa Yerusha, ’yar Zadok.

  9. Ahaz ya zama sarki yana da shekara ashirin, ya kuma yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima ba kamar Dawuda mahaifinsa ba. Ahaz bai yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji Allahnsa ba.

  10. Sai Rezin sarkin Aram, da Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila suka haura don su kai wa Urushalima hari, suka kuma kewaye Ahaz, amma ba su iya shan ƙarfinsa ba.

  11. Yana da shekara ashirin da biyar da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara ashirin da tara a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Abiya ’yar Zakariya.

  12. Sai sarkin Assuriya ya aika da babban shugaban sojojinsa, da shugaban dattawansa, da wakilinsa daga birnin Lakish tare da ƙungiyar sojoji masu yawa zuwa Urushalima domin su yaƙi Sarki Hezekiya. Da suka haura sai suka tsaya a wurin lambatun da yake kawo ruwa daga Tafkin Tudu, kusa da hanyar Filin Mai Wanki.

  13. Sai ya ci gaba da cewa, in kuma ka ce mini “Muna dogara ga Ubangiji Allahnmu ne,” ba masujadansa da bagadansa ne Hezekiya ya ciccire, yana ce wa Urushalima da Yahuda, “Dole ku yi sujada a gaban wannan bagade a Urushalima”?

  14. Wanne a cikin dukan allolin ƙasashen nan ya iya ceton ƙasarsa da gare ni? Shugaban sojojin ya kuma ci gaba da cewa, ta yaya Ubangiji zai ceci Urushalima daga hannuna?”

  15. “Ku faɗa wa Hezekiya sarkin Yahuda, kada ka bar allahn da kake dogara gare shi yă ruɗe ka cewa, ‘Urushalima ba za tă fāɗi a hannun sarkin Assuriya ba.’

  16. Ga abin da Ubangiji yana cewa game da shi, “ ‘Budurwar Sihiyona ta rena ka tana kuma yin maka ba’a. Diyar Urushalima ta kaɗa kanta yayinda kake gudu.

  17. Gama daga Urushalima za a sami ragowa, daga Dutsen Sihiyona kuma za a sami waɗanda suka tsira. Himmar Ubangiji Maɗaukaki za tă cika wannan.

  18. Manasse yana da shekara goma sha biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki shekara hamsin da biyar a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hefziba.

  19. Ya gina bagadai a haikalin Ubangiji, wurin da Ubangiji ya ce, “A Urushalima ne zan sa Sunana.”

  20. Ya ɗauki siffar ginshiƙin Asherar da ya yi, ya sa a haikalin da Ubangiji ya ce wa Dawuda da ɗansa Solomon, “A cikin wannan haikali, da kuma cikin Urushalima inda na zaɓa daga kabilan Isra’ila, zan sa Sunana har abada.

  21. Saboda haka ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, zan jawo wa Urushalima da kuma Yahuda masifar da duk kunnen da ya ji, sai ya kusa suma.

  22. Zan auna Urushalima da ma’aunin da na yi amfani da shi a kan Samariya, zan kuma yi amfani da magwajin da na yi amfani da shi a kan gidan Ahab. Zan shafe Urushalima yadda mutum yake wanke kwano yă kife.

  23. Ban da haka ma, Manasse ya zub da jinin marasa laifi har ya cika Urushalima daga wannan ɓangare zuwa wancan, ban da zunubin da ya sa Yahuda ta aikata, ta haka suka yi mugunta a gaban Ubangiji.

  24. Amon yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki shekara biyu a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Meshullemet ’yar Haruz; ita mutuniyar Yotba ce.

  25. Yosiya yana da shekara takwas sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara talatin da ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Yedida ’yar Adahiya; mutuniyar Bozkat.