Tsallake zuwa abun ciki

Levi

64 ayoyi · 18 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Levi

Tace bisa littafi
  1. sunan matan Amram shi ne Yokebed, ita zuriyar Lawi ce, wadda aka haifa wa Lawiyawa a Masar. A wajen Amram kuwa ta haifi Haruna, Musa da kuma ’yar’uwarsu Miriyam.

  2. A lokacin Ubangiji ya keɓe kabilar Lawi don su riƙa ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, su tsaya a gaban Ubangiji, su riƙa yin masa hidima, su kuma sa albarka a cikin sunansa, yadda suke yi har wa yau.

  3. Shi ya sa Lawiyawa ba su da rabo, ko gādo a cikin ’yan’uwansu; Ubangiji ne gādonsu yadda Ubangiji Allahnku ya faɗa musu.)

  4. Firistocin da suke Lawiyawa, tabbatacce dukan kabilar Lawi, ba za su sami rabo ko gādo tare da Isra’ila ba. Za su yi rayuwa a kan hadayun da aka kawo wa Ubangiji da wuta ne, gama wannan ne gādonsu.

  5. Firistoci, ’ya’yan Lawi maza, za su fito, gama Ubangiji Allahnku ya zaɓe su su yi masa hidima, su kuma furta albarku a cikin sunan Ubangiji, za su kuma daidaita duk rigimar cin mutunci.

  6. Sa’ad da kuka haye Urdun, sai waɗannan kabilai su tsaya a bisa Dutsen Gerizim su sa wa jama’a albarka, wato, kabilar Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar, Yusuf da Benyamin.

  7. Sai Musa ya rubuta wannan doka ya kuma ba da ita ga firistoci, ’ya’yan Lawi maza, waɗanda sukan ɗauka akwatin alkawarin Ubangiji, da kuma dukan dattawan Isra’ila.

  8. Game da Lawi ya ce, “Tummim da Urim na mutumin da ka nuna masa tagomashi ne. Ka gwada shi a Massa; ka yi faɗa da shi a ruwan Meriba.

  9. Kabilar Lawiyawa ne kaɗai Musa bai ba ta gādo ba, gama hadayun ƙonawa da ake miƙa wa Ubangiji, Allah na Isra’ila ne gādonsu, kamar yadda ya yi musu alkawari.

  10. Amma Musa bai ba kabilar Lawiyawa gādo ba; Ubangiji, Allah na Isra’ila, shi ne gādonsu kamar yadda ya yi musu alkawari.

  11. (ga garuruwan da aka ba wa zuriyar Haruna waɗanda suke daga iyalan Kohatawa na Lawiyawa, domin ƙuri’a ta farko ta fāɗa a kansu),

  12. Yerobowam ya gina masujadai da suke kan tuddai, ya kuma naɗa firistoci barkatai daga cikin mutanen da ba na zuriyar Lawi ba.

  13. Waɗannan su ne ’ya’yan Isra’ila maza. Ruben, Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar, Zebulun,

  14. ’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershon, Kohat da Merari.

  15. ’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershom, Kohat da Merari.

  16. ɗan Izhar, ɗan Kohat, ɗan Lawi, ɗan Isra’ila;

  17. ɗan Yahat, ɗan Gershom, ɗan Lawi;

  18. ɗan Mali, ɗan Mushi, ɗan Merari, ɗan Lawi.

  19. da aka ajiye a Ƙofar Sarki a gabas, har zuwa wannan lokaci. Waɗannan su ne matsaran ƙofofi na sansanin Lawiyawa.

  20. mutanen Lawi, su 4,600,

  21. Amma Yowab bai haɗa da mutanen Lawi da na Benyamin a ƙidayar ba, domin bai ji daɗin umarnin sarki ba.

  22. Dawuda ya rarraba Lawiyawa ƙungiya-ƙungiya bisa ga ’ya’yan Lawi maza. Gershon, Kohat da Merari.

  23. An ƙidaya aka kuma haɗa ’ya’yan Musa maza mutumin Allah a sashen kabilar Lawi.

  24. Waɗannan ne zuriyar Lawi bisa ga iyalansu, kawunan iyalai kamar yadda aka rubuta su a ƙarƙashin sunayensu aka kuma ƙirga kowa, wato, masu aikin da suke ’yan shekara ashirin da haihuwa ko fiye waɗanda suka yi hidima a cikin haikalin Ubangiji.

  25. Game da sauran zuriyar Lawi kuwa, Daga ’ya’yan Amram maza. Shubayel; daga ’ya’yan Shubayel maza. Yedehiya.