Jesus
An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ
Ayoyin da suka ambaci Jesus
amma sai ya bi ta tsakiyar taron ya yi tafiyarsa.
Suka yi ta mamakin koyarwarsa, domin saƙonsa yana da iko.
“Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki na Allah!”
Yesu ya tsawata masa da ƙarfin cewa, “Yi shiru! Ka fita daga cikinsa!” Sai aljanin ya fyaɗa mutumin da ƙasa a gabansu duka, sa’an nan ya fita, ya bar shi ba wani rauni.
Dukan mutanen suka yi mamaki, suka ce wa junansu, “Wace irin koyarwa ce haka? Da ƙarfi da iko, yana ba wa mugayen ruhohin umarni suna kuma fita!”
Labarinsa kuwa ya bazu ko’ina a cikin ƙasar.
Yesu ya fita daga majami’ar, ya tafi gidan Siman. Surukar Siman kuwa tana fama da zazzaɓi mai tsanani, sai suka roƙi Yesu yă taimake ta.
Sai ya sunkuya kusa da ita, ya kuma tsawata wa zazzaɓin, sai zazzaɓin ya sāke ta. Nan take ta tashi, ta yi musu hidima.
Rana tana fāɗuwa, sai mutane suka yi ta kawo wa Yesu dukan waɗanda suke da cuta iri-iri, sai ya ɗibiya wa kowannensu hannuwansa, ya warkar da su.
Bugu da ƙari, aljanu suka fiffita daga cikin mutane da yawa suna ihu suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne!” Amma ya kwaɓe su, ya hana su magana, don sun san cewa shi ne Kiristi.
Da gari yana wayewa, sai Yesu ya je inda ba kowa. Mutane suka yi ta nemansa, da suka zo inda yake, sai suka yi ƙoƙari su hana shi barinsu.
Amma ya ce, “Dole in yi wa’azin bisharar mulkin Allah ga sauran garuruwa, saboda wannan ne aka aiko ni.”
Sai ya dinga yin wa’azi a majami’un Yahudiya.
Wata rana, Yesu yana tsaye a bakin Tafkin Gennesaret, mutane kuma suna ta matsawa kewaye da shi, domin su ji maganar Allah,
Sai ya shiga ɗaya jirgin ruwan da yake na Siman, ya kuma roƙe shi yă tura shi kaɗan daga gaci. Sai ya zauna a jirgin ruwan, ya koyar da mutane daga ciki.
Da ya gama magana, sai ya ce wa Siman, “Ka tuƙa jirgin zuwa inda akwai zurfi, ka saukar da abin kamun kifinka ka kama kifi.”
Siman ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, duk dare mun yi ta fama ba mu kama kome ba, amma tun da ka ce haka, zan saki abin kamun kifin.”
Da Siman Bitrus ya ga wannan, sai ya fāɗi a gaban Yesu ya ce, “Rabu da ni, Ubangiji. Ni mai zunubi ne!”
Yaƙub da Yohanna, ’ya’yan Zebedi, abokan aikin Siman su ma suka yi mamaki. Sai Yesu ya ce wa Siman, “Kada ka ji tsoro, daga yanzu za ka riƙa kama mutane ne.”
Sai suka jawo jiragen ruwansu zuwa gaci, suka bar kome da kome, suka bi shi.
Yayinda Yesu yake ɗaya daga cikin garuruwan nan, sai ga wani mutum wanda kuturta ta ci ƙarfinsa. Da ganin Yesu, sai ya fāɗi da fuskarsa a ƙasa, ya roƙe shi ya ce, “Ubangiji, in ka yarda, kana iya ka tsabtacce ni.”
Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin ya ce, “Na yarda, ka zama da tsabta!” Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi.
Sai Yesu ya umarce shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa, amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayu da Musa ya umarta, saboda tsarkakewarka ta zama shaida a gare su.”
Duk da haka, labarinsa ya ƙara bazuwa sosai, har taron mutane suka dinga zuwa don jinsa, da kuma neman warkarwa daga cututtukansu.
Amma Yesu sau da yawa, yakan keɓe kansa zuwa wuraren da ba kowa, yă yi addu’a.