Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka, waɗanda suke shan wahala bisa ga nufin Allah ya kamata su danƙa kansu ga Mahaliccinsu mai aminci, su kuma ci gaba da aikata abin da yake daidai.

  2. Ku zama makiyayan garken Allah da yake a ƙarƙashin kulawarku, kuna hidima kamar masu kula, ba kan dole ba, sai dai da yardar rai, yadda Allah yake so ku zama; ban da kwaɗayin kuɗi, sai dai marmarin yin hidima;

  3. Samari, ku ma, ku yi biyayya ga waɗanda suka girme ku. Dukanku, ku yafa sauƙinkai ga juna, domin, “Allah yana gāba da mai girman kai, amma yakan yi alheri ga mai sauƙinkai.”

  4. Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yă ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama.

  5. Allah mai dukan alheri, wanda ya kira ku ga madawwamiyar ɗaukaka cikin Kiristi, bayan kun sha wahala na ɗan lokaci, shi da kansa zai raya ku, yă kuma sa ku yi ƙarfi, ku kahu, ku kuma tsaya daram.

  6. Da taimakon Sila, wanda na ɗauka a matsayin ɗan’uwa mai aminci, na rubuta muku a taƙaice, ina ƙarfafa ku ina kuma shaida muku cewa wannan shi ne alherin Allah na gaske. Ku tsaya daram a cikinsa.

  7. Siman Bitrus, bawa da kuma manzon Yesu Kiristi, Zuwa ga waɗanda ta wurin adalcin Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi sun sami bangaskiya mai daraja irin tamu.

  8. Alheri da salama su zama naku a yalwace ta wurin sanin Allah da Yesu Ubangijinmu.

  9. Gama ya sami girma da ɗaukaka daga Allah Uba sa’ad da murya ta zo masa daga Mafificiyar Ɗaukaka cewa, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; da shi nake jin daɗi ƙwarai.”

  10. Mu kanmu mun ji wannan muryar da ta zo daga sama sa’ad da muke tare da shi a kan dutse mai tsarki.

  11. Gama annabci bai taɓa samo tushensa daga nufin mutum ba, sai dai mutane sun yi magana daga Allah yayinda Ruhu Mai Tsarki ya bishe su.

  12. Gama in har Allah bai ƙyale mala’iku sa’ad da suka yi zunubi ba, amma ya tura su cikin lahira, domin a tsare su don hukunci;

  13. Amma da gangan suke manta cewa tun dā can ta wurin maganar Allah sammai suka kasance aka kuma yi ƙasa daga ruwa ta wurin ruwa kuma.

  14. yayinda kuke zuba ido ga zuwan ranar Allah kuna gaggauta zuwanta. Wannan rana za tă kawo wa sammai hallaka ta ƙunan wuta, abubuwa kuma za su narke don zafi.

  15. Wannan Rai ya bayyana, muka kuwa gan shi, muka kuma shaida shi, muna kuwa yin muku shelar wannan rai madawwami, wanda dā yake tare da Uba, ya kuma bayyana a gare mu.

  16. Muna yin muku shelar abin da muka gani, muka kuma ji ne, domin ku ma ku yi zumunci tare da mu. Zumuncinmu kuwa yana tare da Uba da kuma Ɗansa, Yesu Kiristi.

  17. Wannan shi ne saƙon da muka ji daga wurinsa, muna kuma sanar da ku cewa Allah haske ne; a cikinsa kuwa babu duhu ko kaɗan.

  18. ’Ya’yana ƙaunatattu, ina rubuta muku wannan ne don kada ku yi zunubi. Amma in wani ya yi zunubi, muna da wani wanda yake magana da Uba don taimakonmu, wato, Yesu Kiristi, Mai Adalci.

  19. Amma in wani ya yi biyayya da maganarsa, ƙaunar Allah ta zama cikakkiya ke nan a cikinsa. Ta haka muka san cewa muna cikinsa.

  20. Ina rubuta muku, ubanni, domin kun san shi wanda yake tun farko. Ina rubuta muku, samari, domin kun ci nasara a kan mugun nan.

  21. Ina rubuta muku, ’ya’yana ƙaunatattu, domin kun san Uba. Ina rubuta muku, ubanni, domin kun san shi wanda yake tun farko. Ina rubuta muku, samari, domin kuna da ƙarfi, maganar Allah kuwa tana zaune a cikinku, kun kuma ci nasara a kan mugun nan.

  22. Kada ku ƙaunaci duniya, ko wani abin da yake cikinta. In wani yana ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa.

  23. Gama duk abin da yake na duniya, kamar sha’awace-sha’awacen mutuntaka, sha’awar idanunsa, da kuma taƙama da abin da yake da shi, yake kuma yi, ba daga wurin Uba suke fitowa ba sai dai daga duniya.

  24. Duniya da sha’awace-sha’awacenta suna shuɗewa, amma mutumin da yake aikata nufin Allah, zai rayu har abada.

  25. Wane ne maƙaryaci? Ai, shi ne mutumin da yake mūsun cewa Yesu shi ne Kiristi. Irin wannan mutum shi ne magabcin Kiristi, ya yi mūsun Uban da kuma Ɗan.