Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Ba wanda yake mūsun Ɗan, sa’an nan yă ce yana da Uban; duk wanda ya yarda da Ɗan, yana da Uban a cikinsa ke nan.

  2. Ku lura fa cewa abin da kuka ji daga farko, bari yă ci gaba da kasance a cikinku. In kuwa ya ci gaba da zama a cikinku, za ku kasance a cikin Ɗan, da kuma a cikin Uban.

  3. Dubi irin ƙaunar da Uba ya ƙaunace mu da ita mana, har ana ce da mu ’ya’yan Allah! Haka kuwa muke! Dalilin da ya sa duniya ba tă san mu ba shi ne, don ba tă san shi ba.

  4. Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ’ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.

  5. Duk mai aikata abin da yake zunubi shi na Iblis ne, domin Iblis mai aikata zunubi ne tun farko. Dalilin da ya sa Ɗan Allah ya bayyana kuwa shi ne don yă rushe aikin Iblis.

  6. Babu haifaffe na Allah da zai ci gaba da yin zunubi, domin iri na Allah yana a cikinsa; ba zai iya ci gaba da yin zunubi ba, domin haifaffe ne na Allah.

  7. Ta haka muka san waɗanda suke ’ya’yan Allah da kuma waɗanda suke ’ya’yan Iblis. Duk wanda ba ya yin abin da yake daidai, ba ɗan Allah ba ne; haka ma wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa.

  8. Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, Yesu Kiristi ya ba da ransa dominmu. Ya kamata mu ma mu ba da rayukanmu domin ’yan’uwanmu.

  9. In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa?

  10. Idan zuciyarmu ta nuna mana muna da laifi, mun san cewa Allah ya fi zuciyarmu, ya kuma san dukan kome.

  11. Abokaina ƙaunatattu, in zukatanmu ba su ba mu laifi ba, muna da ƙarfin halin tsayawa a gaban Allah ke nan.

  12. Abokaina ƙaunatattu, ba kowane ruhu za ku gaskata ba, sai dai ku gwada ruhohi don ku ga ko daga Allah ne, domin annabawan ƙarya da yawa sun fito duniya.

  13. Ga yadda za ku gane Ruhun Allah, duk ruhun da ya yarda cewa Yesu Kiristi ya zo cikin jiki, to, daga Allah yake.

  14. Amma duk ruhun da bai yarda da Yesu ba, ba daga Allah ba ne, ruhun magabcin Kiristi ne, wanda kuka ji yana zuwa, har ma ya riga ya shigo duniya.

  15. Ku, ’ya’yana ƙaunatattu, ku daga Allah ne, kun kuma yi nasara a kan magabtan Kiristi, domin wanda yake a cikinku ya fi wanda yake a duniya girma.

  16. Mu daga Allah ne, kuma duk wanda ya san Allah yakan saurare mu. Amma duk wanda ba daga Allah ba, ba ya sauraronmu. Ta haka ne muke gane Ruhun gaskiya, da kuma ruhun ƙarya.

  17. Abokaina ƙaunatattu, mu ƙaunaci juna, domin ƙauna tana zuwa daga Allah ne. Duk mai ƙauna, haifaffe ne na Allah, ya kuma san Allah.

  18. Duk wanda ba ya ƙauna, bai san Allah ba, domin Allah ƙauna ne.

  19. Ga yadda Allah ya nuna ƙaunarsa a cikinmu, Allah ya aiki makaɗaici Ɗansa zuwa duniya domin mu rayu ta wurinsa.

  20. Wannan ita ce ƙauna, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya kuma aiko Ɗansa yă zama hadaya ta kafara saboda zunubanmu.

  21. Abokaina ƙaunatattu, da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ya kamata mu ma mu ƙaunaci juna.

  22. Ba wanda ya taɓa ganin Allah; amma in muna ƙaunar juna, Allah yana raye a cikinmu, ƙaunarsa kuwa ta zama cikakkiya a cikinmu ke nan.

  23. Mun gani, mun kuma shaida cewa Uba ya aiko Ɗansa domin yă zama Mai Ceton duniya.

  24. Duk wanda ya yarda cewa Yesu Ɗan Allah ne, Allah yana raye a cikinsa, shi kuma a cikin Allah.

  25. Ta haka muka sani, muke kuma dogara ga ƙaunar da Allah yake mana. Allah ƙauna ne. Duk wanda yake rayuwa cikin ƙauna, yana rayuwa a cikin Allah ne, Allah kuma a cikinsa.