God
Ayoyin da suka ambaci God
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka tsaya a filin gidan Ubangiji ka kuma yi magana ga dukan mutanen garuruwan Yahuda waɗanda suka zo sujada a gidan Ubangiji. Ka faɗa musu kome da na umarce ka; kada ka bar wata magana.
Wataƙila su saurara kowanne kuma ya juyo daga mugun hanyarsa. Sa’an nan in yi juyayi in kuma janye masifar da nake shirin kawo a kansu saboda muguntar da suka aikata.
Ka faɗa musu, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, in ba ku saurare ni, ku kuma bi dokata, wadda na sa a gabanku ba,
in kuma ba ku saurari maganganun bayina annabawa, waɗanda na aika muku sau da sau ba (ko da yake ba ku saurara ba),
to, sai in mai da gidan nan kamar Shilo, birnin nan kuma abin la’ana a cikin al’umman duniya.’ ”
Firistoci, annabawa da dukan mutane suka ji Irmiya yana waɗannan maganganu a gidan Ubangiji.
Amma da Irmiya ya gama faɗar wa dukan mutanen abin da Ubangiji ya umarce shi ya faɗa, sai firistoci, annabawa da dukan mutane suka kama shi suka ce, “Mutuwa za ka yi!
Me ya sa ka yi annabci da sunan Ubangiji cewa wannan gida zai zama kamar Shilo, wannan birni kuma zai zama kango da hamada?” Sai duk mutane suka tattaru kewaye da Irmiya a cikin gidan Ubangiji.
Da fadawan Yahuda suka ji haka, sai suka haura daga fada zuwa gidan Ubangiji suka zazzauna a wuraren zamansu a mashigin Sabuwar Ƙofar gidan Ubangiji.
Sai Irmiya ya ce wa dukan fadawa da kuma dukan mutane, “Ubangiji ya aiko ni in yi annabci gāba da wannan gida da wannan birni dukan abin da na faɗa.
Yanzu sai ku gyara hanyoyinku da kuma ayyukanku ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku. Sa’an nan Ubangiji zai yi juyayi ya kuma janye masifar da ya furta zai kawo a kanku.
Ku tabbata dai, cewa in kuka kashe ni, za ku jawo wa kanku alhakin jini marar laifi a kanku da a kan birnin nan da kuma a kan masu zama a cikinsa, gama a gaskiya Ubangiji ne ya aiko ni wurinku domin in faɗa muku dukan maganan nan a kunnuwanku.”
Sai fadawa da dukan mutane suka ce wa firistoci da annabawa. “Wannan mutum bai yi abin da ya isa hukuncin kisa ba, gama ya yi magana da sunan Ubangiji Allahnmu.”
“Mika mutumin Moreshet, ya yi annabci a kwanakin Hezekiya sarkin Yahuda. Ya ce wa dukan mutanen Yahuda, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “ ‘Za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za tă zama tsibin juji, ƙwanƙolin dutsen haikali kuwa zai zama kurmi.’
“Hezekiya sarkin Yahuda ko kuwa wani a Yahuda ya kashe shi? Ashe, Hezekiya bai ji tsoron Ubangiji ya nemi tagomashinsa ba? Ubangiji kuwa bai yi juyayi ya kuma janye masifar da ya furta zai kawo a kansu ba? Muna gab da jawo wa kanmu muguwar masifa!”
(To, fa, Uriya ɗan Shemahiya daga Kiriyat Yeyarim wani mutum ne wanda ya yi annabci da sunan Ubangiji; ya yi annabci irin abu ɗaya gāba da wannan birni da wannan ƙasa yadda Irmiya ya yi.
A farkon sarautar Zedekiya ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wannan magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji.
Ga abin da Ubangiji ya ce mini, “Ka yi karkiyar itace da maɗaurai ka ɗaura a wuyanka.
Ka ba su saƙo wa iyayengijinsu su ce, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Ku faɗa wa iyayengijinku wannan.
Da ikon mai ƙarfi da kuma hannuna da na miƙa na yi duniya da mutanenta da kuma dabbobin da suke ciki, na ba da ita ga duk wanda na ga dama.
Yanzu zan ba da dukan ƙasashenku ga bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon; zan sa namun jeji ma su bauta masa.
“ ‘ “Amma fa, duk al’umma ko mulkin da bai bauta wa Nebukadnezzar sarkin Babilon ba bai kuwa rusunar da wuyarsa ga karkiyarsa ba, zan hukunta wannan al’umma da takobi, yunwa da annoba, in ji Ubangiji, har sai na hallaka ta ta wurin hannunsa.
Suna muku annabcin ƙaryar ne kawai da za tă kau da ku daga ƙasarku; zan kore ku za ku kuwa hallaka.
Amma duk al’ummar da ta rusuna da wuyarta a ƙarƙashin karkiyar sarkin Babilon ta kuma bauta masa, zan bar al’ummar ta zauna a ƙasarta ta noma ta, ta kuma zauna a can, in ji Ubangiji.” ’ ”
Me ya sa kai da mutanenka za ku mutu saboda takobi, yunwa da annoba waɗanda Ubangiji ya yi barazana wa duk al’ummar da ba za tă bauta wa sarkin Babilon ba?