Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Sa’an nan za ku kira gare ni ku zo ku kuma yi addu’a gare ni, zan kuwa ji ku.

  2. Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku.

  3. Za ku same ni,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku daga bauta. Zan tattaro ku daga dukan al’ummai in sa ku inda na kore ku,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku zuwa wurin da na kwashe ku zuwa zaman bauta.”

  4. Za ku iya ce, “Ubangiji ya tā da annabawa saboda mu a Babilon.”

  5. Amma ga abin da Ubangiji yana cewa game da sarki, wanda yake zaune a kursiyin Dawuda da kuma dukan mutanen da suka ragu a wannan birni, ’yan’uwanku waɗanda ba su tafi tare da ku zuwa zaman bauta ba.

  6. I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Zan aika da takobi, yunwa da annoba a kansu zan kuma sa su zama kamar ɓaure marar amfani da suka yi munin da ba a iya ci.

  7. Zan fafare su da takobi, yunwa da annoba zan kuma sa su zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya da kuma abin la’ana da abin bantsoro, abin dariya da abin reni, a cikin dukan al’umman da aka kore su zuwa.

  8. Gama ba su saurari maganata ba,” in ji Ubangiji, “maganar da na aika gare su sau da sau ta bayina annabawa. Ku kuma masu zaman bauta ba ku saurara ba,” in ji Ubangiji.

  9. Saboda haka, ku ji maganar Ubangiji, dukanku masu zaman bauta waɗanda na aika daga Urushalima zuwa Babilon.

  10. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa game da Ahab ɗan Kolahiya da Zedekiya ɗan Ma’asehiya, waɗanda suke muku annabcin ƙarya da sunana. “Zan ba da su ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, zai kuwa kashe su a gaban idanunku.

  11. Saboda su, dukan masu zaman bauta daga Yahuda waɗanda suke a Babilon za su yi amfani da wannan la’ana cewa, ‘Ubangiji ka yi da mu kamar Zedekiya da Ahab waɗanda sarkin Babilon ya ƙone da wuta.’

  12. Gama sun aikata munanan abubuwa a Isra’ila; sun yi zina da matan maƙwabtansu kuma da sunana suka yi ƙarya, waɗanda ban faɗa musu su yi ba. Na san wannan kuma ni shaida ne ga haka,” in ji Ubangiji.

  13. “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ka aika da wasiƙu da sunanka ga dukan mutane a Urushalima, zuwa ga Zefaniya ɗan Ma’asehiya firist da kuma ga sauran firistoci. Ka ce wa Zefaniya,

  14. ‘Ubangiji ya naɗa ka firist a wurin Yehohiyada don ka lura da gidan Ubangiji; ya kamata ka sa kowane mahaukaci wanda yake yi kamar annabi cikin turu da kuma a kangi.

  15. Sa’an nan maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,

  16. “Ka aika da wannan saƙo zuwa ga dukan masu zaman bauta cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa game da Shemahiya, mutumin Nehelam. Domin Shemahiya ya yi muku annabci, ko da yake ban aike shi ba, ya kuma sa kuka gaskata ƙarya,

  17. ga abin da Ubangiji yana cewa, tabbatacce zan hukunta Shemahiya mutumin Nehelam da zuriyarsa. Ba zai kasance da wani da ya rage a cikin wannan mutane ba, ba kuwa zai ga abubuwa alherin da zan yi wa mutanena ba, in ji Ubangiji, domin ya yi wa’azin tawaye a kaina.’ ”

  18. Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga Ubangiji.

  19. “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Ka rubuta a cikin littafi dukan maganganun da na yi maka.

  20. Kwanaki suna zuwa,’ in ji Ubangiji, ‘sa’ad da zan komo da mutanena Isra’ila da Yahuda daga bauta in kuma maido da su ga ƙasar da na ba wa kakanninsu mallaka,’ in ji Ubangiji.”

  21. Ga kalmomin Ubangiji da ya yi game da Isra’ila da Yahuda,

  22. “Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Ana jin kukan tsoro, razana, ba salama ba.

  23. Ku tambaya ku ji. Namiji zai iya haifi ’ya’ya? To, me ya sa kuke ganin kowane mai ƙarfi da hannuwansa a kwankwaso kamar mace mai naƙuda, kowace fuska ta koma fari?

  24. “ ‘A wannan rana,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki, ‘Zan karya karkiya daga wuyansu zan kuma cire musu kangi; baƙi ba za su ƙara bautar da su ba.

  25. A maimakon haka, za su bauta wa Ubangiji Allahnsu Dawuda sarkinsu kuwa, wanda na tayar musu.