God
Ayoyin da suka ambaci God
‘Ban aike su ba,’ in ji Ubangiji. ‘Suna annabcin ƙarya ne da sunana. Saboda haka, zan kore ku za ku kuwa hallaka, da ku da kuma annabawan da suke muku annabci.’ ”
Sai na ce wa firistoci da dukan waɗannan mutane, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, kada ku saurari annabawan da suke cewa, ‘Ba daɗewa ba za a komo da kayan gidan Ubangiji daga Babilon.’ Suna muku annabcin ƙarya ne.
In su annabawa ne da gaske suna kuma da maganar Ubangiji, bari su roƙi Ubangiji Maɗaukaki ya sa kada a kwashe kayayyakin da suka ragu a gidan Ubangiji da kuma a cikin fadar sarkin Yahuda da kuma cikin Urushalima a kai Babilon.
Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa game da ginshiƙai, kwatarniya, da dakalai, da sauran kayayyaki da aka bar su a birnin nan,
I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa game da abubuwan da aka bari a gidan Ubangiji da kuma a cikin fadar sarkin Yahuda da Urushalima,
‘Za a kwashe su zuwa Babilon a can kuwa za su kasance sai ranar da na neme su,’ in ji Ubangiji. ‘Sa’an nan zan komo da su in maido da su wannan wuri.’ ”
A wata na biyar na wannan shekara, shekara ta huɗu, a farkon sarautar Zedekiya sarkin Yahuda, sai annabi Hananiya ɗan Azzur, wanda ya fito daga Gibeyon, ya zo wurina a gidan Ubangiji a gaban firistoci da kuma dukan mutane,
“Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Zan karya karkiyar sarkin Babilon.
Cikin shekaru biyu zan komo da dukan kayayyakin gidan Ubangiji da Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwashe daga wannan wuri ya kai Babilon.
Zan kuma komo da Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda da kuma dukan sauran masu zaman bauta daga Yahuda waɗanda suka tafi Babilon,’ in ji Ubangiji, ‘gama zan karya karkiyar sarkin Babilon.’ ”
Sai annabi Irmiya ya amsa wa annabi Hananiya a gaban firistoci da kuma dukan mutane waɗanda suke tsaye a gidan Ubangiji.
Ya ce, “Amin! Ubangiji yă sa yă zama haka! Ubangiji yă cika maganar da ka yi annabci ta wurin komo da kayayyakin gidan Ubangiji da kuma dukan masu zaman bauta zuwa wannan wuri daga Babilon.
Amma annabin da ya yi annabcin salama shi za a ɗauka a matsayin wanda Ubangiji ya aika in har abin da ya furta ya zama gaskiya.”
ya ce a gaban dukan mutane, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘A haka zan karya karkiyar Nebukadnezzar sarkin Babilon daga wuyan dukan al’ummai a cikin shekaru biyu.’ ” Da wannan, annabi Irmiya ya yi tafiyarsa.
Ba a daɗe ba bayan annabi Hananiya ya karya karkiya daga wuyan annabi Irmiya, sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,
“Je ka faɗa wa Hananiya cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka karya karkiyar katako, amma a wurinsa za ka sami karkiyar ƙarfe.
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa zan sa karkiyar ƙarfe a wuyan dukan waɗannan al’ummai don in sa su bauta wa Nebukadnezzar sarkin Babilon, za su kuwa bauta masa. Zan ma sa shi ya mallaki namun jeji.’ ”
Sa’an nan annabi Irmiya ya ce wa annabi Hananiya, “Ka saurara, Hananiya! Ubangiji bai aike ka ba, duk da haka ka lallashe wannan al’umma su dogara ga ƙarya.
Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Ina shirin kawar da kai daga fuskar duniya. A wannan shekara za ka mutu, domin ka yi wa’azin tawaye a kan Ubangiji.’ ”
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ga dukan waɗanda aka kwashe zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon.
Haka kuma, ku nemi zaman salama da cin gaba a birnin da aka kai ku zaman bauta. Ku yi addu’a ga Ubangiji saboda birnin, domin in ya ci gaba, ku ma za ku ci gaba.”
I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa, “Kada ku bar annabawa da masu sihiri a cikinku su ruɗe ku. Kada ku saurari mafarkan da dā kuke ƙarfafa su su yi.
Suna muku annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba,” in ji Ubangiji.
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Sa’ad da shekaru saba’in suka cika a Babilon, zan zo muku in cika alkawarin alherina don in komo da ku zuwa wannan wuri.
Gama na san shirye-shiryen da na yi muku,” in ji Ubangiji, “shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba.