God
Ayoyin da suka ambaci God
Ba ku kawo mini tumaki don hadaya ta ƙonewa ba, balle ku girmama ni da hadayunku. Ban nawaita muku da hadaya ta gari ba balle in gajiyar da ku da bukatar turare.
Ba ku saya wani turaren kalamus domina ba ko ku gamshe ni da kitsen hadayunku. Amma kun nawaita ni da zunubanku kuka kuma gajiyar da ni da laifofinku.
“Ni kaɗai ne na shafe laifofinku, saboda sunana, ban kuma ƙara tunawa da zunubanku ba.
Ku tunashe ni abin da ya riga ya wuce, bari mu yi muhawwara wannan batu tare; ku kawo hujjarku na nuna rashin laifinku.
Mahaifinku na farko ya yi zunubi; masu magana a madadinku suka yi mini tayarwa.
Saboda haka zan kunyata manyan baƙi na haikalinku, zan tura Yaƙub ga hallaka Isra’ila kuwa yă zama abin dariya.
“Amma yanzu ka saurara, ya Yaƙub, bawana, Isra’ila, wanda zaɓa.
Ga abin da Ubangiji yana cewa, shi wanda ya yi ka, wanda ya siffanta ka a cikin mahaifa, wanda kuma zai taimake ka. Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub, bawana, Yeshurun, wanda na zaɓa.
Gama zan zuba ruwa a ƙeƙasasshiyar ƙasa, rafuffuka kuma a busasshiyar ƙasa; zan ba da Ruhuna ga ’ya’yanka, albarkata kuma ga zuriyarka.
Wani zai ce, ‘Ni na Ubangiji ne’; wani kuma zai kira kansa da sunan Yaƙub; har yanzu wani zai rubuta a hannunsa, ‘Na Ubangiji,’ ya kuma ɗauki sunan Isra’ila.
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, Sarki da kuma Mai Fansar Isra’ila, Ubangiji Maɗaukaki. Ni ne farko ni ne kuma ƙarshe; in ban da ni babu wani Allah.
Wane ne kuwa kama da ni? Ya faɗa a ji. Bari yă yi shela ya kuma nuna shi a gabana mene ne ya faru tun da na kafa mutanena na dā, mene ne kuma bai riga ya faru ba, I, bari yă faɗa abin da zai zo.
Kada ku firgita kada kuma ku ji tsoro. Ban furta wannan na kuma yi faɗar haka tuntuni ba? Ku ne shaiduna. Akwai wani Allah in ban da ni? A’a, babu wani Dutse; ban san da wani ba.”
“Tuna da waɗannan abubuwa, ya Yaƙub, gama kai bawana ne, ya Isra’ila. Na yi ka, kai bawana ne; Ya Isra’ila, ba zan manta da kai ba.
Na shafe laifofinka kamar girgije, zunubanka kamar hazon safe. Ka komo wurina, gama na kuɓutar da kai.”
Ku rera don farin ciki, ya sammai, gama Ubangiji ya aikata wannan; ku yi sowa, ya duniya a ƙarƙashi. Ku ɓarke da waƙoƙi, ku duwatsu, ku jeji da dukan itatuwanku, gama Ubangiji ya kuɓutar da Yaƙub, ya nuna ɗaukakarsa a cikin Isra’ila.
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansarka, wanda ya yi ka a cikin mahaifa. “Ni ne Ubangiji, wanda ya yi dukan abubuwa, wanda ya shimfiɗa sammai ya kuma kafa harsashen duniya da kansa,
wanda ya tabbatar da maganganun bayinsa ya kuma cika annabce-annabcen ’yan aikansa, “wanda ya ce game da Urushalima, ‘Za a zauna a cikinta,’ game da garuruwan Yahuda, ‘Za a gina su,’
wanda ya yi zancen Sairus ya ce, ‘Shi ne makiyayina zan kuma cika dukan abin da na gan dama; zai yi zancen Urushalima cewa, “Bari a sāke gina ta,” game da haikali kuma cewa, “Bari a kafa harsashinsa.” ’
“Ga abin da Ubangiji ya faɗa wa shafaffensa, ga Sairus, wanda hannun damansa yana riƙe da shi don yă ci al’ummai a gabansa ya kuma tuɓe makaman sarakuna, don yă buɗe ƙofofi a gabansa don kada a kulle ƙofofi.
Zan ba ka dukiyar duhu, arzikin da aka ajiye a asirtattun wurare, saboda ka san cewa ni ne Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya kira ka da suna.
Saboda sunan Yaƙub bawana, Isra’ila zaɓaɓɓena, na kira ka da suna na ba ka matsayin bangirma, ko da yake ba ka san ni ba.
Ni ne Ubangiji, kuma babu wani; in ban da ni babu wani Allah. Zan ƙarfafa ka, ko da yake ba ka san ni ba,
saboda daga fitowar rana har zuwa fāɗuwarta mutane za su san cewa babu wani in ban da ni. Ni ne Ubangiji, kuma babu wani.
Ni ne na siffanta haske na kuma halicci duhu, ni ne nake ba da nasara in kuma jawo bala’i; ni, Ubangiji ne ke aikata dukan waɗannan abubuwa.