Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Amma Ubangiji ya nuna musu alheri, ya ji tausayinsu, ya kuma damu da su saboda alkawarinsa da Ibrahim, Ishaku da Yaƙub. Har yă zuwa yau bai yarda yă hallaka su ko yă shafe su daga gabansa ba.

  2. Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji, sai dai ba kamar kakansa Dawuda ba. A kome dai ya bi gurbin mahaifinsa Yowash.

  3. Duk da haka bai kashe ’ya’yan masu kisan ba, bisa ga abin da yake a rubuce a Dokar Musa inda Ubangiji ya umarta, “Ba za a kashe iyaye saboda laifin ’ya’ya ba, ko kuma ’ya’ya saboda laifin iyayensu ba, kowa zai mutu don zunubansa.”

  4. Ya kwashi ɗaukan zinariya da azurfa da duk kayan da aka samu a haikalin Ubangiji da kuma ma’ajin fadan. Ya kuma kwashi bayi sa’an nan ya koma Samariya.

  5. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji bai kuwa kauce wa duk zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta aikata ba.

  6. Shi ne ya maido da iyakokin Isra’ila daga Lebo Hamat zuwa Tekun Araba, bisa ga maganar Ubangiji, Allah na Isra’ila, da ya yi ta bakin bawansa Yunana ɗan Amittai, annabi daga Gat-Hefer.

  7. Ubangiji ya ga irin muguwar wahalar da ta shafi kowa a Isra’ila, ko bawa ko ’yantacce, babu mai taimakonsu.

  8. Da yake kuma Ubangiji bai ce zai shafe sunan Isra’ila daga fuskar duniya ba, sai ya cece su ta hannun Yerobowam ɗan Yowash.

  9. Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji, yadda mahaifinsa Amaziya ya yi.

  10. Ubangiji ya sa wa sarki ciwon kuturta har mutuwarsa, ya kuma zauna a keɓe. Yotam ɗan sarki, shi ne ya gudanar da sha’anin fada, ya kuma shugabanci mutanen ƙasar.

  11. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda mahaifinsa ya yi. Bai bar aikata zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila suka yi ba.

  12. Ta haka maganar Ubangiji da ya yi wa Yehu ta cika, wadda ya ce, “Zuriyarka za tă zauna a kursiyin Isra’ila har tsara ta huɗu.”

  13. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. A duk tsawon mulkinsa, bai rabu da zunuban da Yerobowam ɗan Nebat ya sa Isra’ila suka aikata ba.

  14. Fekahiya ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat wanda ya sa Isra’ila ya aikata ba.

  15. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai kauce wa zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta yi ba.

  16. Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji yadda mahaifinsa Uzziya ya yi.

  17. Duk da haka, bai kawar da masujadan kan tudu ba; mutane suka ci gaba da yin hadaya da ƙona turare a can. Yotam ya sāke gina Ƙofar Bisa ta haikalin Ubangiji.

  18. (A kwanakin nan Ubangiji ya fara aikan Rezin sarkin Aram da Feka ɗan Remaliya, su yi gāba da Yahuda.)

  19. Ahaz ya zama sarki yana da shekara ashirin, ya kuma yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima ba kamar Dawuda mahaifinsa ba. Ahaz bai yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji Allahnsa ba.

  20. Ya yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila har ya miƙa ɗansa hadaya a wuta, yana bin hanyoyin banƙyama na al’ummai da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa.

  21. Ahaz ya ɗauki azurfa da zinariyar da suke a haikalin Ubangiji da suke kuma a ma’ajin fada ya aika wa sarkin Assuriya kyauta.

  22. Sai ya cire bagaden tagulla wanda aka keɓe ga Ubangiji, ya sa shi a gaban haikalin wato, tsakanin ƙofar shiga haikalin Ubangiji da sabon bagaden. Ya ajiye shi a gefen arewa na sabon bagaden.

  23. Ya kawar da rumfa Asabbacin da aka gina a haikalin, ya kuma kawar da mashigin sarki na waje da haikalin Ubangiji, duk dai don yă gamshi sarkin Assuriya.

  24. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, amma ba kamar na sarakunan Isra’ilan da suka riga shi ba.

  25. Duk wannan ya faru ne saboda Isra’ilawa sun yi wa Ubangiji Allahnsu zunubi, shi wanda ya fitar da su daga Masar daga ƙarƙashin ikon Fir’auna sarkin Masar. Sun yi wa waɗansu alloli sujada