Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. sai in yanke mutanen Isra’ila daga ƙasar da na ba su, in kuma ƙi wannan haikalin da na tsarkake domin Sunana. Isra’ila kuwa za tă zama abin gori da abin dariya a cikin dukan mutane.

  2. Wannan haikali zai zama tarin juji. Duk wanda ya wuce ta hanyan nan kuwa zai ji tausayi, yă kuma yi tsaki yana cewa, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka ga wannan ƙasa da kuma wannan haikali?’

  3. Mutane za su amsa su ce, ‘Saboda sun yashe Ubangiji Allahnsu, wanda ya fitar da su daga Masar, suka rungumi waɗansu alloli, suna yin musu sujada, suna bauta musu ne, ya sa Ubangiji ya kawo dukan masifan nan a kansu.’ ”

  4. A ƙarshen shekaru ashirin da Solomon ya ɗauka yana gina haikalin Ubangiji da fadan sarki,

  5. Ga lissafin ma’aikatan gandun da Sarki Solomon ya ɗauka don ginin haikalin Ubangiji, da fadarsa, da madogaran gini, da katangar Urushalima, da kuma Hazor Megiddo da Gezer.

  6. Sau uku a shekara Solomon kan miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama a kan bagaden da ya gina wa Ubangiji, yana ƙone turare a gaban Ubangiji haɗe da su, ta haka ya cika abin da ake bukata na haikali.

  7. Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ji game da sunan da Solomon ya yi, da kuma dangantakarsa da Ubangiji, sai ta zo tă gwada shi da tambayoyi masu wuya.

  8. Da irin abincin da yake kan teburinsa, da irin zaman fadawansa, da irin rigunan masu hidimarsa, da irin masu shayarwarsa, da kuma hadayun ƙonawar da yake yi a haikalin Ubangiji, sai ta yi mamaki ƙwarai.

  9. Yabo ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ji daɗinka, ya kuma sa ka a kujerar sarautar Isra’ila. Ubangiji ya naɗa ka sarki saboda madawwamiyar ƙaunar wa Isra’ila, don ka yi shari’a da adalci.”

  10. Sarki ya yi amfani da almug don yă yi kayan ado wa haikalin Ubangiji da kuma don fadan sarki, don kuma yă yi molaye, da garayu saboda mawaƙa. Ba a taɓa yin jigilar katakon almug ko a gani irin yawan katakai haka ba har wa yau.)

  11. Dukan duniya ta nemi su zo wurin Solomon don su ji hikimar da Allah ya sa a zuciyarsa.

  12. Sun fito daga al’ummai da Ubangiji ya ce wa Isra’ilawa, “Kada ku yi aurayya da su, domin tabbatacce za su juye zukatanku zuwa ga waɗansu alloli.” Duk da haka Solomon ya manne musu, ya nace, yana ƙaunarsu.

  13. Yayinda Solomon yake tsufa, matansa suka juye zuciyarsa ga bin waɗansu alloli, zuciyarsa kuwa ba tă bi Ubangiji Allahnsa ɗungum kamar yadda zuciyar Dawuda mahaifinsa ta kasance ba.

  14. Saboda haka Solomon ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji. Bai bi Ubangiji gaba ɗaya kamar yadda Dawuda mahaifinsa ya yi ba.

  15. Ubangiji ya yi fushi da Solomon domin zuciyarsa ya juye daga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya bayyana masa sau biyu.

  16. Ko da yake ya hana Solomon bin waɗansu alloli, Solomon bai kiyaye umarnin Ubangiji ba.

  17. Saboda haka Ubangiji ya ce wa Solomon, “Da yake halinka ke nan, ba ka kuma kiyaye alkawarina, da ƙa’idodina da na umarce ka ba, tabbatacce zan yage masarautar daga gare ka, in ba da ita ga ɗaya daga cikin bayinka.

  18. Amma saboda Dawuda mahaifinka, ba zan yi haka a zamaninka ba. Zan yage ta daga hannun ɗanka.

  19. Amma ba zan yage dukan masarautar daga gare shi ba, zan ba shi kabila ɗaya saboda Dawuda bawana, da kuma saboda Urushalima, wadda na zaɓa.”

  20. Sai Ubangiji ya tayar wa Solomon wani abokin gāba, mai suna Hadad, mutumin Edom daga gidan sarautar Edom.

  21. Allah kuwa ya tayar wa Solomon wani abokin gāba, mai suna Rezon, ɗan Eliyada, wanda ya gudu daga maigidansa, Hadadezer sarkin Zoba.

  22. Sa’an nan ya ce wa Yerobowam, “Ɗauki gida goma wa kanka, gama abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce ke nan, ‘Duba, zan yage masarauta daga hannun Solomon in ba ka kabilu goma.

  23. Zan yi wannan domin sun yashe ni, suka kuma yi wa Ashtarot, alliyar Sidoniyawa, da Kemosh, allahn Mowabawa, da kuma Molek, allahn Ammonawa sujada, ba su yi tafiya a hanyoyina ba, ba su kuwa yi abin da yake daidai a idanuna ba, ba su kiyaye farillaina da dokokina kamar yadda Dawuda, mahaifin Solomon ya yi ba.

  24. “ ‘Amma ba zan ɗauki dukan masarautar daga hannun Solomon ba; na naɗa shi sarki, dukan kwanaki ransa saboda Dawuda bawana, wanda na zaɓa, wanda kuma ya kiyaye umarnai da farillaina.

  25. Zan ba da ɗaya ga ɗansa don kullum Dawuda bawana yă kasance da fitila a gabana a Urushalima, birnin da na zaɓa in sa Sunana.