God
Ayoyin da suka ambaci God
in suka canja zuciyarsu a ƙasar da aka riƙe su kamammu, suka tuba, suka kuma roƙe ka a ƙasar waɗanda suka ci su da yaƙi, suka ce, ‘Mun yi zunubi, mun yi abin da ba daidai ba, mun yi mugunta’;
in sun juye gare ka da dukan zuciyarsu, da dukan ransu a ƙasar abokan gābansu waɗanda suka kwashe kamammu, suka yi addu’a gare ka, suka fuskanci wajen ƙasar da ka ba wa kakanninsu, waje birnin da ka zaɓa, da kuma haikalin da na gina domin Sunanka;
sai ka ji daga sama, mazauninka, ka ji addu’a da roƙonsu, ka kuma biya musu bukatansu.
Ka gafarta wa mutanenka, waɗanda suka yi maka zunubi; ka gafarta dukan laifofin da suka yi maka, ka kuma sa waɗanda suka ci su a yaƙi su ji tausayinsu.
Gama su mutanenka ne, abin gādonka, waɗanda ka fitar daga Masar, daga tanderu mai narken ƙarfe.
“Bari idanunka su buɗe ga roƙon bawanka, ga roƙon mutanenka Isra’ila, bari kuma ka saurare su sa’ad da suka yi kuka gare ka.
Gama ka ware su daga dukan al’umman duniya su zama abin gādonka, kamar yadda aka furta ta wurin bawanka Musa sa’ad da kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka ka fitar da kakanninmu daga Masar.”
Da Solomon ya gama dukan waɗannan addu’o’i da roƙe-roƙe ga Ubangiji, sai ya tashi daga gaban bagaden Ubangiji, inda ya durƙusa da hannuwansa a buɗe waje sama.
“Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda ya ba wa mutanensa hutu kamar dai yadda ya yi alkawari. Babu magana guda da ta kāsa cika cikin dukan alkawaransa masu kyau da ya yi ta wurin bawansa Musa.
Bari Ubangiji Allah yă kasance tare da mu kamar yadda ya kasance da kakanninmu; kada yă taɓa rabu da mu, ko yă yashe mu.
Bari yă juye zukatanmu gare shi, don mu yi tafiya a cikin dukan hanyoyinsa, mu kuma kiyaye umarnansa, ƙa’idodinsa, da kuma farillan da ya ba wa kakanninmu.
Bari kuma waɗannan kalmomina, waɗanda na yi addu’a a gaban Ubangiji, su yi kusa da Ubangiji Allahnmu, dare da rana, don yă biya bukatan bawansa da na mutanensa Isra’ila, bisa ga bukatan kowa,
saboda dukan mutanen duniya su san cewa Ubangiji, shi ne Allah, babu kuma wani.
Amma dole ku miƙa zukatanku ga Ubangiji Allahnmu, don ku rayu, ta wurin bin ƙa’idodinsa, ku kuma yi biyayya da umarnansa, kamar yadda kuke yi a wannan lokaci.”
Sai sarki da dukan Isra’ila, suka miƙa hadayu a gaban Ubangiji.
Solomon ya miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, shanu dubu ashirin da biyu, tumaki da awaki dubu ɗari da dubu ashirin. Ta haka sarki da dukan Isra’ilawa suka keɓe haikalin Ubangiji.
A wannan rana sarki ya tsarkake sashe na tsakiyar fili a gaban haikalin Ubangiji, a can kuma ya miƙa hadaya ta ƙonawa, hadaya ta gari, da kitsen hadaya ta salama, gama bagaden tagulla a gaban Ubangiji ya yi ƙanƙanta sosai da za a miƙa hadayun ƙonawa, hadayun hatsi, da kuma kitsen hadayun salama.
Ta haka Solomon da dukan Isra’ila, wato, babban taro, suka yi bikin a lokacin. Mutane suka zo, tun daga Lebo Hamat har zuwa Rafin Masar. Suka yi biki a gaban Ubangiji Allahnmu, kwana bakwai. Suka kuma ƙara kwana bakwai, kwanaki goma sha huɗu gaba ɗaya.
A rana ta biye sai ya sallame mutane. Suka sa wa sarki albarka, sa’an nan suka watse zuwa gida, da farin ciki, da murna a zukatansu saboda kyawawan abubuwan da Ubangiji ya yi domin bawansa Dawuda, da kuma mutanensa Isra’ila.
Sa’ad da Solomon ya gama ginin haikalin Ubangiji da kuma fadan sarki, ya kuma yi dukan abin da yake so yă yi,
sai Ubangiji ya bayyana gare shi sau na biyu, kamar yadda ya bayyana masa a Gibeyon.
Ubangiji ya ce masa, “Na ji addu’arka da kuma roƙon da ka yi a gabana; na tsarkake wannan haikali wanda ka gina, ta wurinsa Sunana zai kasance a can har abada. Idanuna da zuciyata kullum za su kasance a can.
“Kai kuwa, in ka yi tafiya a gabana da mutunci a zuci da kuma gaskiya, kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, ka yi dukan abin da na umarta, ka kuma yi biyayya da ƙa’idodina da kuma dokokina,
zan kafa kujerar sarautarka a bisa Isra’ila har abada, kamar yadda na alkawarta wa Dawuda mahaifinka sa’ad da na ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani a kan kujerar sarautar Isra’ila ba.’
“Amma in kai, ko ’ya’yanka maza, suka juye daga gare ni, ba ku kuma kiyaye umarnai da ƙa’idodin da na ba ku ba, kuka yi gaba, kuka bauta wa waɗansu alloli, kuka kuma yi musu sujada,