God
Ayoyin da suka ambaci God
Sai suka aiki manzanni zuwa Kiriyat Yeyarim suka ce, “Filistiyawa sun komo da akwatin alkawarin Ubangiji, ku zo ku ɗauka ku kai wajenku.”
Mutanen Kiriyat Yeyarim suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji. Suka kai a gidan Abinadab da ke kan tudu, suka keɓe Eleyazar ɗansa yă lura da akwatin alkawarin Ubangiji.
Akwatin Alkawarin ya daɗe a Kiriyat Yeyarim ya kai shekara ashirin cif. Sai dukan mutanen Isra’ila suka yi makoki suka nemi Ubangiji.
Saboda haka Sama’ila ya yi magana da dukan gidan Isra’ila ya ce, in har da zuciya ɗaya kuke juyowa ga Ubangiji sai ku raba kanku da baƙin alloli da gunkin nan Ashtarot, ku ba da kanku ga Ubangiji. Ku yi masa bauta shi kaɗai, zai kuɓutar da ku daga hannun Filistiyawa.
Sai Isra’ilawa suka rabu da gumakan Ba’al da Ashtarot suka bauta wa Ubangiji kaɗai.
Sama’ila ya ce, “Ku tattara dukan Isra’ila a Mizfa, ni kuwa zan yi addu’a ga Ubangiji dominku.”
Sa’ad da suka taru a Mizfa, suka kawo ruwa suka zuba a gaban Ubangiji. A wannan rana suka yi azumi suka tuba, suka ce, “Mun yi wa Ubangiji zunubi!” Sama’ila kuwa ya zauna a Mizfa ya yi mulkin Isra’ilawa.
Suka ce wa Sama’ila, “Kada ka fasa kai kukanmu ga Ubangiji Allahnmu saboda mu, don yă cece mu daga hannun Filistiyawa.”
Sama’ila ya kama ɗan rago ya miƙa shi ɗungum hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ya yi roƙo ga Ubangiji a madadin Isra’ila, Ubangiji kuwa ya amsa addu’arsa.
Lokacin da Sama’ila yana miƙa hadaya ta ƙonawa, Filistiyawa suka matso kusa don su yi yaƙi da Isra’ila. A ranar Ubangiji ya sa babban tsawa ya ruɗar da Filistiyawa har suka gudu a gaban Isra’ilawa.
Sa’an nan Sama’ila ya ɗauki dutse ya kafa tsakanin Mizfa da Shen, ya sa masa suna, Ebenezer ma’ana, “Har zuwa wannan lokaci Ubangiji ya taimake mu.”
Ta haka Isra’ilawa suka ci Filistiyawa. Daga ranan Filistiyawa ba su ƙara yin nasara a kan Isra’ila ba. Ubangiji ya yi gāba da Filistiyawa har ƙarshen zamanin Sama’ila.
Amma yakan komo Rama inda gidansa yake, a nan yakan yi wa Isra’ila shari’a. A nan ne kuma ya gina wa Ubangiji bagade.
Amma Sama’ila bai ji daɗi sa’ad da suka ce, “Ka ba mu sarki da zai bi da mu.” Sai ya yi addu’a ga Ubangiji.
Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka saurari dukan maganganun da mutanen suke gaya maka. Ai, ba kai ba ne suka ƙi, ni ne suka ƙi in zama sarkinsu.
Haka suka yi daga tun daga ranar da na fitar da su daga Masar har zuwa yau, suka ƙi ni, suka bauta wa waɗansu alloli, haka ma suke yi maka.
Sama’ila kuwa ya ce wa mutanen da suke roƙo yă naɗa musu sarki dukan abin da Ubangiji ya faɗa.
Sa’ad da ranar ta zo, za ku yi kuka ku nemi a fishe ku daga sarkin da kuka zaɓa, Ubangiji kuwa ba zai ji ku ba.”
Da Sama’ila ya ji duk maganganun da mutanen suka faɗa, sai ya mayar wa Ubangiji.
Ubangiji kuwa ya ce, “Ka saurare su, ka naɗa masu sarki.” Sa’an nan Sama’ila ya ce wa mutanen Isra’ila, “Kowa yă koma garinsa.”
Amma bawan ya amsa ya ce, “Duba, a wannan gari akwai wani mutumin Allah, ana ganin girmansa ƙwarai kuma duk abin da ya faɗa yakan zama gaskiya. Mu tafi can wurinsa wataƙila zai gaya mana hanyar da za mu bi.”
Shawulu ya ce wa bawan, “Idan muka isa can, me za mu ba wa mutumin? Ga shi abinci guzurinmu duk ya ƙare, ba mu da wani abin da za mu kai wa mutumin Allahn nan. Me muke da shi?”
Bawan ya sāke ce masa, “Duba ina da kwatar azurfar da zan ba wa mutumin Allah don yă gaya mana wace hanya ce za mu bi.”
(A dā a Isra’ila, in wani yana so yă nemi nufin Allah, mutumin yakan ce, “Zo mu tafi wajen mai duba.” Gama wanda ake ce da shi annabi a yanzu, a dā ana kiransa mai duba ne.)
Shawulu ya ce wa bawansa, “Madalla, zo mu tafi.” Sai suka kama hanya suka nufi birnin da mutumin Allah yake.