Skip to content
Farawa 42:16-38

Farawa 42:16-38

16
Ku aiki ɗaya daga cikinku yă kawo ɗan’uwanku; za a sa sauranku a kurkuku, saboda a gwada maganarku a ga ko gaskiya ce kuke faɗi. In ba haka ba, to, da ran Fir’auna, ku ’yan leƙen asiri ne!”
17
Ya kuwa sa su duka a kurkuku na kwana uku.
18
A rana ta uku, Yusuf ya ce musu, “Ku yi wannan za ku kuwa rayu, gama ina tsoron Allah.
19
In ku mutane masu gaskiya ne, ku bar ɗaya daga cikin ’yan’uwanku yă zauna a kurkuku, yayinda sauranku su tafi, su kai hatsi don gidajenku da suke yunwa.
20
Amma dole ku kawo ƙaramin ɗan’uwanku gare ni, saboda a tabbatar da maganarku har ba za ku mutu ba.” Suka kuwa yi haka.
21
Sai suka ce wa juna, “Tabbatacce ana hukunta mu ne saboda ɗan’uwanmu. Mun ga yadda ya yi wahala sa’ad da ya roƙe mu saboda ransa, amma ba mu saurare shi ba, shi ya sa wannan wahala ta zo mana.”
22
Ruben ya amsa, “Ban faɗa muku cewa kada ku ɗauki alhakin yaron nan ba, sai kuka ƙi ji, to, yau ga alhakin jininsa muke biya.”
23
Ba su san cewa Yusuf yana jin su ba, da yake yana amfani da mai fassara ne.
24
Sai ya juya daga gare su ya yi kuka, sa’an nan ya dawo ya yi musu magana kuma. Ya sa aka ɗauke Simeyon daga gare su, aka daure shi a idanunsu.
25
Yusuf ya yi umarni a cika buhunansu da hatsi, a kuma sa azurfan kowane mutum a cikin buhunsa, a kuma ba su kalaci don tafiyarsu. Bayan aka yi musu wannan,
26
suka jibga hatsinsu a kan jakuna, sai suka kama hanya.
27
A wurin da suka tsaya don su kwana, ɗaya daga cikinsu ya buɗe buhunsa don yă ciyar da jakinsa, sai ya ga azurfansa a bakin buhunsa.
28
Sai ya ce wa ’yan’uwansa, “An mayar mini da azurfata. Ga shi a cikin buhuna.” Zuciyarsu ta karai, suka dubi juna suna rawan jiki, suka ce, “Mene ne wannan da Allah ya yi mana?”
29
Sa’ad da suka zo wurin mahaifinsu Yaƙub a ƙasar Kan’ana, suka faɗa masa dukan abin da ya faru da su. Suka ce,
30
“Mutumin da yake shugaba a ƙasar ya yi mana matsananciyar magana, ya kuma ɗauke mu tamƙar ’yan leƙen asirin ƙasa.
31
Amma muka ce masa, ‘Mu masu gaskiya ne; mu ba ’yan leƙen asiri ba ne.
32
Dā mu ’yan’uwa ne goma sha biyu, ’ya’yan mahaifi guda maza. Ɗayanmu ya rasu, kuma ƙaramin yanzu yana tare da mahaifinmu a Kan’ana.’
33
“Sai mutumin wanda yake shugaba a kan ƙasar ya ce mana, ‘Ga yadda zan san ko ku mutane masu gaskiya ne. Ku bar ɗaya daga cikin ’yan’uwanku a nan tare da ni, ku ɗauki abinci domin gidajenku masu yunwa, ku tafi.
34
Amma ku kawo mini ƙaramin ɗan’uwanku domin in san cewa ku ba ’yan leƙen asiri ba ne, amma mutane ne masu gaskiya. Sa’an nan zan mayar muku da ɗan’uwanku, ku kuma iya yin sana’a a ƙasar.’ ”
35
Yayinda suke juyewa hatsi daga buhunansu, sai ga ƙunshin azurfan kowane mutum a buhunsa! Sa’ad da su da mahaifinsu suka ga ƙunshe-ƙunshen kuɗi, suka firgita.
36
Yaƙub mahaifinsu, ya ce musu, “Kun sa ni rashin ’ya’yana. Yusuf ya rasu, Simeyon kuma ba ya nan, yanzu kuma kuna so ku ɗauki Benyamin. Kome yana gāba da ni!”
37
Sai Ruben ya ce wa mahaifinsa, “Ka kashe dukan ’ya’yana maza, in ban dawo da shi gare ka ba. Ka sa shi ga kulawata, zan kuwa dawo da shi.”
38
Amma Yaƙub ya ce, “Ɗana ba zai gangara zuwa can tare da ku ba, ɗan’uwansa ya rasu, shi ne kaɗai ya rage. In wani abu ya faru da shi a tafiyar da za ku yi, za ku sa furfurata ta gangara zuwa kabari cikin baƙin ciki.”

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options